SHEIKH DAHIRU

  • KISSA: Kissan Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA Da Wasu Jikokin Sa.

    Wasu Kananan Yara Daga Cikin Jikokin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi Suka Aikata wani karamin Laifi su Uku Ana Sallah sai Suka Kunna Famfo sunata Wasa da Ruwa Bayan Idar da Sallah sai Maualana Sheikh yasa

     

    Aka kirawosu gabansa yace a samo bulala sai yace dasu meye yasa ana Sallah Kuna Wasa sai Suka kasa magana sai Shehu yace ya’yan waye sai a kace Akaramakallh dan-wane -ne da Dan wane Cikin ya’yan Maualana Sheikh sai maulana Sheikh yace meye Sunanku sai daya.

     

    Yace sunana Muhammadu dayan yace Ahmad Tijjani dayan yace Ibrahim Inyass sai babu bata lokaci Shehu yace dasu Ku tashi ku tafi kunci Albarkacin masu Sunanku ko sunana Shehu Ibrahim Inyass R T.A. Shehu baya iya kira haka

     

    Gatsau sai dai Idan karatu ya biyo takai shiyasa ma yake Kiran khadimul Faida da Suna Shehu saboda takwarane ga Shehu Ibrahim Inyass R.T.A. to bari Kuma Shugaban Halitta Annabi Muhammadu S.A.W.. yakamata a kula Allah ya kiyaye mana Imanimmu don Alfarmam Annabi Muhammadu S.A.W.

     

    Daga: Abubakar Ibrahim Wunti

  • Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya tattauna da DW Hausa albarkacin cikarsa shekaru 100 a duniya.

  • Babban Shehin Malami Kuma Jigo A Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru 101 A Duniya Lissafin Hijiriyya.

    Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR Ya Cika Shekaru 101 A Duniya Lissafin Hijiriyya.

     

    Sheikh Dahiru Bauchi OFR RA, sanannen malamin Islama ne da yayi suna a nahiyar Afirka baki daya saboda hidimarsa ga addinin Musulunci Shehin malamin na da shekaru 101 Hijjah Miladiya a duniya.

     

    Kuma shehin malamin yana da yara 80, Malamin ya bayyana cewa a cikin yara 80 guda 70 duk sun haddace kur’ani mai tsarki.

     

    Shehin ya rubuta kur’ani sau biyu, da hannun sa yana kan na ukun kuma ya yi aikin hajji fiye da 50 a duniya da aikin Umrah fiye da 100.

     

    Sheikh Dahiru Usman Bauchi babban shehin darikar Tijjaniya ne da ake ji dashi a duk fadin nahiyar Afirka.

     

    Ya sadaukar da rayuwarshi wajen hidimtawa Al-Qur’ani ta hanyar koyar dashi ga jama’a, Yana da makaratu a duk jihohin Arewacin Nijeriya dama yammacin Africa.

     

    An haifi shehin malamin a ranar 28 ga watan Yuni 1927 ko 1924 wanda ya yi dai-dai da 2 ga watan Muharram 1346. Ko 1344, Bisa sabanin Lissafi.

     

    An haifeshi a garin Nafada da ta ke jihar Gombe a halin yanzu kuma shine dan fari a wajen mahaifin sa, Shekh Dahiru Usman Bauchi Cikakken bafulatani ne gaba da baya. Sunan mahaifiyar sa Maryam ‘yar Ardo Sulaiman, mahaifinshi sunanshi Alhaji Usman dan Alhaji Adam.

     

    Shehin malamin ya haddace kur’ani a wurin mahaifinsa inda daga baya ya tura shi Bauchi don neman tilawa. Malamin ya yi auren fari a 1948 lokacin yana da shekaru 20 a duniya

     

    Sheikh Dahiru ya ce yana da ‘ya’ya kimanin 80 kuma 70 daga ciki sun haddace kur’ani. Wasu daga ciki sun haddace tun suna da shekaru 7 a duniya, tun kafin su iya rubutun allo.

     

    Kuma yayan sa kan fita kasashen duniya don karatun fannonin addini har da na boko. Akwai Daraktoci a cikin ‘ya’yana a yanzu,”

     

    Sheikh Dahiru Bauchi na da mata hudu, duk da wasu sun rasu, wasu kuma dq yawa sun fita.

     

    Sheikh Dahiru yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani.

     

    cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda suka karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.

     

    Sheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.

     

    Shehin malamin Yace abin da ya fi bashi sha’awa a rayuwarsa shi ne irin yadda ya mayar da Alkur’ani sana’arsa da kuma yadda ya rungumi Darikar Tijjaniya ta zama rayuwarsa.

     

    Allah ya kara ma rayuwa albarka, ya karawa Maulana Sheikh lafiya da nisan kwana. Amiin Yaa ALLAH

  • ARFAT 2024: Kallin Yanda Aka Gudanar Da Wazifa A Filin Arfat Cikin BIDIYO.

    Yau ce ranar da al’ummar Musulmai da ke gudanar da aikin Hajjin bana ke tsayuwar Arfa.

     

    Tsayuwar Arfa na ɗaya daga cikin ƙololuwar aikin Hajji, inda ake buƙatar mahajjata su tsaya a filin domin yin addu’o’i na musamman.

     

     

    Mabiya Darikar Tijjaniyya a fadin duniya suna daga cikin wanda suke halartan Aikin Hajj duk shekara tare da gabatar da ayyukan su na sufanci a filin Arfat.

     

    Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR ya jagoranci Wazifa a filin Arfat tare da daukaci mutane daga sassan fadin duniya.

     

    Allah ya karbi ayyukan mu da Addu’o’in mu baki daya. Amiin Yaa ALLAH

  • Najeriya ta fi kowace ƙasa yawan mahaddata Alkur’ani a duniya – Sheikh Dahiru Bauchi RA.

    Najeriya ta fi kowace ƙasa yawan mahaddata Alkur’ani a duniya – Sheikh Dahiru Bauchi

     

    Shehun malamin ya ce Najeriya ta sha bamban da sauran kasashe wajen haddar Alkur’ani.

     

    Sheikh Dahiru Usman Bauchi Shugabanin Darikar Tijjaniya na Afirka, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce Najeriya ta fi kowace kasa yawan mahadatta Alkur’ani mai girma a fadin duniya.”

     

    Ya ce a fadin duniya babu kasar da ta kai Najeriya yawan mahaddata Alkur’ani wanda hakan, ya sa kasar ta zama daban da sauran kasashe.”

     

    Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wajen bikin yaye dalibai mahaddata da gidauniyarsa ta Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta gudanar, karo na hudu a Gombe.”

     

    Shehun malamin ya samu wakilcin ɗansa, Sayyadi Ali Shiekh Dahiru Bauchi, inda ya koka kan yadda tsadar rayuwa ta tsananta a Najeriya.”

     

    Ya kuma gargadi mahaddatan da cewa Alkur’ani, ba abun wasa ba ne, inda ya jaddada bukatar kada su yi wasa da shi.

     

    Kazalika, ya yabawa masu yi wa addinin Musulunci hidima don ganin ya samu daukaka a Najeriya da ma duniya baki daya.”

     

    Sai dai ya ja hankalin masu hannu da shuni da su rungumi akidar taimakawa marasa karfi don rage musu radadin tsadar rayuwa da ake fuskanta.”

     

    Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, ya samu wakilcin Kwamishinan Kimiyya da Kere-Kere, Farfesa Abdullahi Bappah Garkuwa.

     

    Kwamishinan ya jinjina wa Sheikh Dahiru Bauchi, kan kafa gidauniyar a jihohin kasar nan, wanda hakan ke kara yawan mahaddata Alkur’ani.

Back to top button