SHEIKH DAHIRU

 • Shin Akwai Aljanu Yan Darikar Tijjaniyya Kamar Yanda Sheikh Dahiru Bauchi RA Yake Fada. ???

  SHIN AKWAI ALJANU YAN ĎARIQAR TIJJANIYYA KAMAR YADDA AKE YAĎAWA MAULANMU SHEHU ĎAHIRU BAUCI YA FAĎA?

   

  Banji hakikar abinda Maulanmu Shehu Ďahiru Bauci ya faďa kan wannan qadhiyya ba, sai dai koma yaya lamarin ya kasance wannan magana bata saba da shari’a ba balle ta zamto abin yin Isgili ga wannan babban bawan Allah da ya karar da rayuwar sa cikin hidimar Musulunci.

   

  Tamkar yadda mutane suke firaq daban daban Ahlussunah,Shi’a mu’utazila da Yan Izala haka abin yake cikin Aljanu.

   

  Allah ya faďa mana cikin qur’anin sa mai girma game da firaq na Aljanu.

   

  وَأَنَّا مِنَّا الصَّالِحُونَ وَمِنَّا دُون ذَلِكَ كُنَّا طَرَائِق قِدَدًا

  ( Daga cikin mu akwai Salihai akwai waďand basu ba, mun kasance tafarkai ne mabanbanta)

   

  Al’imamu Alqurďubi ya hakaito daga Suddiy yana lokacin da yake fassara طرأئق قددا.

   

  Yace 👉 السدي في قوله تعالى { طرائق قددا} قال : في الجن مثلكم قدرية، ومرجئة، وخوارج، ورافضة، وشيعة، وسنية. وقال قوم :

   

  Alhafiz Ibn Katheer cikin tafsirin sa karkashin wannan aya ya kawo kissar Sulaiman bin Mihrãn Al’a’amash yadda yayi magana da Aljani har ya tambaye shi abincin da yake so ya kawo mashi sannan ya tambaye shi Su Waye Rãwafidh cikin ku (Aljanu) sai Aljanin yace sune mafiya sharrin mu.

   

  سمعت الأعمش يقول تروح إلينا جني فقلت له ما أحب الطعام إليكم فقال الأرز قال فأتيناهم به فجعلت أرى اللقم ترفع ولا أرى أحدا فقلت فيكم من هذه الأهواء التي فينا قال نعم فقلت فما الرافضة فيكم قال شرنا

   

  Ibn Katheer yace ” Na karantawa Shehina Mizzi isnãdin wannan kissa yace min ta inganta”

   

  Kenan a wajen Malamai ba sabuwar magana bace ace an sami Aljani ďan ďariqa ko wata firqa.Wanda dama mu yan Tijjaniya bamu shakka ko kaďan akwai Aljanu masu tarin yawa da suke Tijjaniya.

   

  Haka kuma akwai Aljanun da suke bin tafarkin Bidi’a na Wahabiyya wanda waďannan Aljanu masu shiga jikin Yan mata su hana su Aure saboda…

   

  Allah ya kara wa Shehi lafiya. Amiiiin

  Share
 • Za’a gina babban katafaren cibiyar haddar Alkur’ani mai girma ta zamani a jihar Bauchi mai suna “Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA”

  ALBISHIRIN KU MUTANE SHEIKH DAHIRU BAUCHI RA.

   

  Za’a gina babban katafaren cibiyar haddar Alkur’ani mai girma ta zamani a jihar Bauchi mai suna “Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA” wanda mai girma gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulƙadir Ƙauran Bauchi ta dauki nauyin ginawa.

   

  Gwamnan jihar Bauchi Senator Bala Abdulƙadir Ƙauran ya fadi hakan ne, a yayin da yakai ziyara girmamawa ga babban malamin a gidan sa dake titin Bauchi zuwa Gombe, inda ya tabbatar da fara aikin cikin kan-kanin lokaci da rardan Allah.

   

  Muna alfahari da wannan katafaren aiki, Muna addu’an Allah ya saka masa da alkhairi, ya karawa Maulana Sheikh lafiya da nisan kwana albarkacin Manzon rahma SAW. Amiiiin

   

  Babangida Alhaji Maina

  Tijjaniyya Media News

  Share
 • ZABEN 2023: Kowa Yake Ya Zabi Wanda Yake So, Amman Ku Zabi Shugaba Nagari. Inji Sheikh Dahiru Bauchi OFR RA.

  YA DACE JAGORORIN KUNGIYA SU NAKALCI IRIN WANNAN HIKIMAR WAJEN JAGORORIN SUFAYE.

   

  A zabukan 2011 da kuma 2015 wasu daga Maluman Kungiya sun ayyanawa mabiya yan takarar jam’iyyun da suke so su zaba, karshe dai duk dadin bakin da sukayiwa mabiya aka fuskanci akasinsa kowa yaji a jikinsa, to sai gashi yanzu ma wasunsu na son mai-maita kuskure ta hanyar yin abinda suka yi a baya.

   

  Ka duba jawabi mai cike da wayewa, yadda Maulana Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, da Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A) suka fayyacewa dukkanin mabiya akan, kowa ya zabi wanda ya kwanta masa a rai, wanda hakan matakine da babu wani guda da zai kuka dasu har abada, idan aka samu akasi a mulkin wani shugaba da ace sun ayyana shi.

   

  ALLAH YA GANAR DA JAGORORIN WAHABIYA GA RUNGUMAR WANNAN HIKIMAR, WALA’ALLAH SA RAGE DUMLMIYAR DA MABIYA. AMIIN YAA ALLAH.

   

  Daga: Muhammadu Usman Gashua

  Share
 • Ni Bani Da Wani Ɗan Takara Ɗaya Tak Da Zan Zaba. Inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR

  PRESS RELEASE;

   

  Zantawar MAULANMU SHEHU TAHIRU (R.A) Da ‘Yan Jaridu a Jiya Litinin 20-02-2023

   

  “INA SON KOWA YA FITA YA ZAƁI WANDA YAKE SO, DON NI BA NI DA WANI ƊAN TAKARA” – SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI.

   

  Babban Shehun Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Shehu Ɗahiru Usman Bauchi Ya Ce; Ba Shi Da Wani Ɗan Takara Ɗaya Tak Da Zai Ce a Zaɓa a Babban Zaɓen Shugaban Ƙasa a Najeriya Da Za a Gudanar a Ranar Asabar Mai Zuwa.

   

  Shehu Ɗahiru Usman Bauchi Wanda Ya Ke Amsa Tambayoyi Daga Manema Labaru a Abuja Ya Ce; Shi Kowa Na Sa Ne a ‘Yan Takarar, Don Haka Ya Ke Bukatar Jama’a Su Yi Amfani Da Hankalinsu Wajen Zabar Wanda Su Ka Ga Ya Dace a Babban Zaɓen.

   

  Kazalika Malamin Ya Yi Fatan Duk Wanda Ya Lashe Zaɓen Ya Zama Sabon Shugaban Najeriya To Ya Mai Da Hankali Wajen Kawo Hanyoyin Da Talakawa Za Su Samu Sauƙi Daga Ƙuncin Tattalin Arzikin Da Ake Fama.

   

  “Gwamnatin Nan Da Mu Ka Fito, Ba Mu Ji Daɗin Ta Ba, Akwai Abubuwa Da Yawa Na Matsuwar Mutane a Zamaninta, Wanda Ba Mu Ji Daɗinsu Ba, Kamar Tsare(Rufe) Ƙasa a Hana Komai Shiga, Na Ciki Kuma Ba Ya Isa, Mu Ne Talakawa ‘Yan Ƙasa Ba Mu Ji Daɗin Waɗannan Ba.”

   

  Malamin Ya Gabatar Da Addu’ar Zaman Lafiya Mai Ɗorewa a Najeriya Ya Na Mai Yabawa Manema Labaru Da Yanda Su Ke Aikin Isar Da Saƙonnin Wayar Da Kan Jama’a.

   

  (©️Mai Rahoto/Rubutawa; Nasiru Adamu El-Hikaya, VOA Hausa).

   

  Ameeeen, Ameeen SHEHU(R.A).

   

  ALLAH Ya Kara Maka Lafiya Da Nisan Kwana, Ya Sa Mu Kammala Waɗannan Zaɓuka Da Muka Saka a Gaba Lafiya, Ya Bamu Mafi Alkhairi, Don Albarkar SHUGABA(S.A.W) Amiiiin

   

  Daga: Othman Muhammad

  Share
 • Jawabi Mai Matuƙar Muhimmanci Daga MAULANA SHEIKH DAHIRU BAUCHI OFR (R.A).

  Daga Taskar MAULANMU SHEHU TAHIRU USMAN BAUCHI (R.A)

   

  Jawabi Mai Matuƙar Muhimmanci Daga MAULANA SHEIKH DAHIRU BAUCHI OFR (R.A).

   

   

  ALLAH Ya Ƙara Muku Yarda. Amiiin

   

  Allah Ya Kara Wa Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA Lafiya Da Nisan Kwana Albarkacin Manzon Allah SAW. Amiin

  Share
Back to top button