SHEHU TIJJANI BAHAUSHE NE
Ƙwarai kuwa, Shehu Ahmadu Tijjani RTA ɗin nan namu dai bahaushe ne ta wurin mahaifiyar sa, sunan ta Afiya, baiwa ce wacce Mijin ta ya samo ta daga ƙasar hausa, ya kaita Aini Madhi ya yanta ta, ya aure ta, Amma saboda tsananin wahalar juna biyu da tsangwamar abokan zama a gidan mijin nata, shiyasa dole tayi hijira daga Aini Madhi zuwa yankin Constantine/Rome inda ƙabilar Shawi suka tarbe ta domin sarkin su mutumin kirki ne, ya bata kulawa sosai har ta haihu lafiya, bayan ta haihu sai ta sa ma yaron nata suna Ahmad.
Baku fahimta ba ko?
Ina magana ne akan Sidi Ahmad Ammar ɗan Sidi Muhammadul Habib ɗan Sidi Abul Abbas Shehu Ahmad Tijjani RTA, wanda ake yawo da hoton sa a matsayin shine Shehu Tijjani mai ɗariƙa alhali jikan sa ne amma tabbas sunyi kama sosai.
Mahaifiyar sa ta sa masa suna Ahmad ne don ta yiwa Shehu Tijjani takwara, Sannan tayi masa alkunya da sunan sarkin nan wanda ya taimake ta wato “Ammar” saboda godiya bisa halaccin sa.
Watarana limamin masallacin Atiƙ a Aini Madhi yayi mafarki da Sidi Muhammadul Habib ɗan Shehu Tijjani RTA, yace masa “kaje ka gayawa ɗana Sidi Muhammadul Bashir cewa yana da ɗan’uwa kuma lallai yaje ya nemo shi”. Sidi Bashir kuwa ana gaya masa nan take ya tura mutane neman wannan ɗan’uwan nasa ko ina a ƙasar Algeria amma babu labarin sa.
Bayan lokaci ƙanƙani sai yaji labarin wani yaro mai abubuwan ban mamaki a garin “Annaba/عنابة” na Algeria, ya aika a roƙe su a taho dasu domin ya samu labari babu wanda ke yi musu dole ballantana wulakanci, saboda watarana Sidi Ahmad Ammar yana kiwo sai wani baturen faransa masu mulkin mallaka ya ɗaga hannu zai dake shi saboda dabbar yaron ta kusanci gonar sa, nan take hannun baturen ya sage, sai da yayi ta magiya yana ba yaron nan haƙuri sannan daga baya hannun ya dawo daidai, wannan labarin ya karaɗe ko ina, shiyasa ake shakkar tunkarar su da zalunci.
Ko da aka yi sa’a aka lallaɓa yaron nan da mahaifiyar sa suka iso Aini Madhi, Sidi Bashir yana ganin yaron, Allah yayi masa kashafi yaga tambarin su na zuri’ar Shehu Tijjani a tare dashi, ashe wannan yaro Sidi Ahmad Ammar ne da Mahaifiyar sa Afiya (Allah ya ƙara musu yarda). Sidi Bashir yayi farinciki sosai bisa haɗuwar sa da wannan ƙani nasa mai albarka kuma ba jimawa ya miƙa masa khalifancin Tijjaniyya sannan ya mai da hankali wurin bashi kulawa sosai, duk da shi Sidi Bashir ne babba, amma Allah ne a gaban sa ba mulki ba, shiyasa ya girmama hasken dake tare da ɗan’uwan sa.
A takaice, zuri’ar Shehu Tijjani sun yaɗu ne ta tatson Sidi Bashir da Sidi Ammar ya’yan Sidi Muhammadul Habib ƙanin Sidi Muhammadul Kabir, Allah ya ƙara musu yarda, damu tare dasu baki daya, Amin.
✍️ Sidi Sadauki