TARIHI

 • Tarihin Fatima Yar Sheikh Ibrahim Inyass Na Farko A Duniya.

  FATIMA YAR GAUSIN ZAMANI (YA FATU)

   

  Ita ce babbar diyar Shehul Islam Alhaji Ibrahim Niasse Allah ya ƙara yarda a gare shi, kuma matar cikamakin Halifofi Imamu Ali Cisse, kuma mahaifiyar Imamul Faira Sheikh Hassan Cisse Allah ya ƙara yarda a gare shi..

   

  Da wuya samun kamar ta domin itace yar Gausi, matar Qutib kuma Uwar Qutib.

   

  An tabbatar da cewa tun tana da ƙananan shekaru take karantar da Alkur’ani, kuma sannan tana yin salla a jama’i sau biyar a rana a tsawon shekaru a masallacin mahaifinta sannan ta rika tafiya Makkah, Madina da Fez.

   

  An ruwaito cewa a farkon shekarun aurenta ta samu yawaitar zubewar ciki. Don haka a lokacin da take ɗauke da cikin Imamu Hassan Allah ya ƙara yarda a gare shi, sai ta roƙi Maulana Shehul Islam Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya yi mata addu’a ta musamman domin neman tsira ga wannan abin haihuwa ya zo duniya.

   

  Shehu Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya yi mata addu’a sannan ya bata wani abu mai tsarkin gaske ya ce mata idan an zo haihuwar a haifi yaron a kan sa.

   

  Cikin ikon Allah an haifi jaririn cikin ƙoshin lafiya. Da ya ke ya zo da sirri mai girma tun haihuwarsa, kuma gashi ya kasance dan FATIMA da ALI, sai Shehu ya sawa jaririn suna HASSAN, kuma ya yi addu’ar Allah ya yi masa arzikin gadon sirrin Imam Hassan Ibn Ali Amincin Allah ya ƙara tabbata a gare shi

   

  Daga cikin ‘ƴaƴanta akwai Malamanmu Sheikh Tijjani Cisse da kuma Sheikh Mahy Cisse.

   

  Sheikh Tijjani Cisse

   

  A Lokacin da aka haifi Sheikh Tijjani, nan take Shehu ya sanya masa suna “Sheikh Ahmed al-Tijani”. Mahaifinsa Imamu Ali Cisse, ya yi wata addu’a a rubuce : “Ina rokon Allah mai girma ya zamo ga wannan abin haihuwa ya kasance cikakken magajin Shehu Tijjani”.

   

  An rawaito daga Sheikh Hassan Cisse ya ce a lokacin ya ce mahaifiyarmu Yafatu Niasse tana da ciki na Shehu Mahy ta yi mafarkin shugaba Sallallahu alaihi Wa sallama, a cikin mafarkin ya umurce ta da ta sa wa yaron da zata haifa suna “Muhammad al-Mahy”. Ta boye mafarkin ga kowa. Lokacin da aka haifi jaririn kuma aka kai shi wurin Shehu Ibrahim domin ya ba da suna. Kai tsaye ya sanyawa yaron suna, “Muhammad al-Mahy.” kuma ya yi wata magana mai girman gaske.

   

  Allah ya ba mu albarkar ta albarkarci Imamu Hassan Cisse…

   

  ~Mujaheed Magaji Muhammad

  Share
 • NANA FATIMA (A.S) Shugabar Matayen Talikai.. Kuma Mafi Soyuwar Mutane a Wajen Mahaifinta (S.A.W)

  A RANA MAI KAMAR TA YAU(20 Ga Watan JUMADA THANI Aka Haifi NANA FATIMAH(A.S)

   

  ZINARIYAR GIDAN ANNABTA, UWA GA SHARIFAI

   

  NANA FATIMA(A.S) Shugabar Matayen Talikai.. Kuma Mafi Soyuwar Mutane a Wajen MahaifinTA(S.A.W)

   

  Tafi Kowa Yin Kamanni Da MahaifinTA(S.A.W),

  Tafiyarsu Iri ‘Daya,

  Zamansu Da Tashinsu Iri ‘Daya,

  Maganarsu Ma Iri ‘Daya

   

  MahaifinTA(S.A.W) Ya Ce; FATIMAH Tsokar Jikina Ce. Duk Abin Da Ya Fusata Ta, To Nima Ya Fusata Ni. Kuma Ya Ce:”ALLAH Yana Fushi Da Fushin FATIMAH”.

   

  ALLAH Ya Girmama NANA FATIMAH(A.S), Don Haka MANZON ALLAH(S.A.W) Yake Girmamata.

   

  Idan Yana Zaune Idan Ya Hangota Ta Taho, Sai Ya Mike Ya Tarota.

   

  Ya Kan Rungumeta Yana Cewa;”Madalla Da ‘Yata Kuma Sanyin Idanuna”.

   

  Idan MA’AIKI(S.A.W) Zai Tafi Yaki Sai Yabi Ta Gidanta Yai Mata Sallama. Sannan Idan Ya Dawo Ma Haka.

   

  A Cikin Iyalan Gidansa Ita Ce; Farkon Wacce Ta Fara Rasuwa a Bayansa, Kuma Ita Ce Wacce Zata Fara Haduwa Da Shi a Ranar Alkiyamah.

   

  A Ranar Al-Qiyamah Idan Dukkan Mutane Da Aljannu Da Mala’iku Sun Hadu, Za’a Ji Wata Murya Tana Cewa:

   

  “KU YI ‘KAS DA KANKU(KU YI LADABI) FATIMAH CE ‘YAR ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) ZATA WUCE!!!”.

   

  LA ILAHA ILLALLAH………..

   

  Muna Taya MUMINAI Murnar Zagayowar Wannan Rana; Da Aka Haifi SHUGABAR MATAN ALJANNAH, TSOKA DAGA JIKIN MA’AIKI(S.A.W) Wato NANA FATIMAH (A.S)

   

  Ya ALLAH Ka Bamu Albarkar NANA FATIMAH(A.S),

   

  Ka ‘Kara Mana Son NANA FATIMAH(A.S),

   

  Ka Amintar Damu a Cikin Amincinta,

   

  Ka Yarda Damu Dominta(Aminci Da Yardar ALLAH Su ‘Kara Tabbata a Gareta Da Mahaifinta).

   

  Salatin ALLAH Da Amincinsa Su ‘Kara Tabbata a Bisa Shugaban Manzanni Tare Da Iyalen Gidansa Da Dukkan Sahabbansa. Amiin

  Share
 • Tarihin Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano Kashi Na Hudu (4).

  MAI TAMBARIN ZIKIRI DATTIJO MAI ABUN MAMAKI MAULANA SHEIKH ALIYU HARAZIMI HAUSAWA (RADIYALLAHU ANHU) (IV) Hudu 4.

   

  Har yanzu muna cikin goman farko ta watan Zul Hajji wanda a cikin irin kwanakin Maulana Sheikh Aliyu Harazimi Hausawa (Radiyallahu anhu) Ya kasance a wannan duniya. A ranar 9 ga wata wanda a ranar ake tsayiwur Arfa..

   

  Insha Allahu zan ɗora da tarihin ƙasaitaciyar rayuwar Maulana Sheikh Aliyu Harazimi Hausawa (Radiyallahu anhu) Na tsaya a inda na ke bada tarihin zaman Maulana a wajen shahararren waliyin nan Sheikh Muhammadu Gibrima (Radiyallahu anhu).

   

  Shehu ya dawo garin Kano da zama bayan wafatin Shehinsa Muhammadu Gibrima (Radiyallahu anhu) wanda yayi wafati a shekarar 1975 duda akwai maganganu da suke tabbatar da cewa dama yana zaune a cikin birnin Kano tun kafin wafatin Shehinsa.

   

  Shehu ya cigaba zama a zawiya da ke unguwar Hausawa da ya gada a wurin mahaifinsa, Shehu ya kwashe sama da shekaru sittin na rayuwarsa yana karantarwa, da horar da zuciyar Bayin Allah ta koma tsarkakiya da kaddamar da dimbin almajirai a Kano da wajenta.

   

  Littattafai da yawa Shehu ya rubuta, wasu an buga su, wasu kuma suna yawo a matsayin rubuce-rubuce a tsakanin mu mu mabiyansa. Amman a matsayinsa na Sufi wanda babban abin da ya dame shi shi ne koyar da mai son samun Allah a sauƙaƙe yadda ake tsarkake zuciya Nafs al-Ammara (ƙananan ruhi) don ya mayar da ita cikin Nafs al-kamila cikakken samun zauƙin Ubangiji.

   

  Maulana Shehu Aliyu Harazimi (Radiyallahu anhu) Ya rubuta littattafai da dama a fagen ilimin halin ruhi. Waɗanda sun haɗa da, wani littafi mai suna , Kasr al-nufus da kuma wani littafi mai suna Juhud al-‘ajiz (‘Ƙoƙarin marasa ƙarfi’).

   

  Waɗannan littattafai sun tattauna akan matakai daban-daban da ƙalubalen da mai neman Allah yake zai fuskanta yayin ƙoƙarinsa na samun wusuli.

   

  Wani fanni da Shehu kuma ya yi rubuta a cikinsa shi ne nau’inkan Salati ga Annabi (Sallallahu alaihi Wa sallama) . Ba sai na yi bayanin yanda muhimmancin salati ga Annabi a wajen Muslimi musamman Sufaye. Domin daruruwan Sufaye da yawa, sun yi rubutu wanda suke tabbatar da shine ya zama ginshiƙin tafarkin ruhi, kamar yadda aka yi imani da cewa yana ba wa mai buri damar shiga ‘halarar Annabi’ (al-hadra al-Muhammadiyyah) kuma ya sami haske.

   

  Wannan gaskiya ne musamman a cikin tafiyar Sufaye, wanda ya zama koyarwarmu mun yi imani cewa haƙiƙanin Annabi (al-Haqiqa al-Muhammadiyya) shine farkon halittar Allah kuma shi ne ruhin Duniya (al-Nafs al-kulli) ya mamaye wuri na tsakiya.

   

  Wasu daga cikin manyan malaman Darikar Tijjaniyya.. sun rubuta littafai irin nasu na salati ga Annabi, wadanda ake karantawa a Najeriya a yau. Wasu misalan sun hada da;

  Akwai littafi mai suna Yaqutat al-muhtaj, wanda Shehu Muhammadu al-Damrawi ya rubuta (wanda ya rasu a shekara ta 1799), wanda ya kasance aminin Shehu Ahmad al-Tijani (Radiyallahu anhu)

   

  Akwai shahararren littafin nan na Salati mai suna Al-Tibb al-fa’ih, wanda Sheikh ‘Abd al-Wahid al-Nazifi ya rubuta wanda yayi wafati a shekarar 1948.

  Da kuma litattafai da dama kamar irin wanda Shehun Najeriya Sheikh Muhammad Gibrima Shehin Maulana ya rubuta, wasu daga cikin litattafan Salati akwai.

   

  Jihaz al-sarih…da

  Nata’ij al-Safar.

   

  Shima Sheikh Aliyu Harazimi Radiyallahu anhu ya tattara nasa salati ga Annabi sun hada da; Sullam al-muhibbin ila hadrat khayr al-mursalin Sannan akwai shahararren littafin nan mai suna Sir al-asrar (‘Sirrin Sirri’), duka an buga su a Kano.

   

  ~Mujaheed M Muh’d

  Share
 • Takaitaccen Tarihin Sheikh Modibbo Aliyu Jobbo Dan Modibbo Abbdullahi (Shetiman Dukku) Dake Garin Gombe.

  TAKAITACCEN TARIHIN MAULANMU SHEIKH MODIBBO ALIYU JOBBO GOMBE ALLAH YA ƘARA YARDA A GARE SHI.

   

  Na samu wannan rubutun daga zuriyarsa mai albarka kuma su ne su kai izinin da a ƙara yaɗawa ƴan uwa domin mu ƙara amfana da ƙasaitaciyar rayuwar Maulana Sheikh Madibo Aliyu Jobbo.

   

  Sunansa Modibbo Aliyu Jobbo ɗan Modibbo Abbdullahi (Shetiman Dukku) ɗan Modibbo Ardo Haruna jikan Modibbo Ardo Sambo Bodejo Sarkin Fulani na farko a kasar Dukku.

   

  Sun zo ƙasar Dukku tun kafin jihadin Shehu Usman dan Fodiyo a shekarar ta 1804, kamar yadda ya zo a tarihi sun zo ne daga yammaci kasar Sudan wato yankin Kurdufan yankin yana maƙotaka da ƙasar Tchadi, sun biyo ta yankin Kanem Borno sun tsaya a Ƙatar kalam Dukku a yanzu wasun su kuma suka wuce garin Mama’are, wasu kuma garin Shira duk a jihadin garin Bauchi wasu kuma sun wuce yankin Jahun na jahar Jigawa.

   

  An haifi Maulana Modibbo Jobbo a garin Dukku na jihar Gombe a yanzu a shekarar 1895 ko 1898 wanda tai daidai da 1315 ko da 1316 Hijiriyya….

   

  Ya ta so cikin kullawar mahaifinsa Modibbo Abdullahi Allah ya ƙara yarda a gare shi, wanda ya kasance shi ma shahararren waliyin ne. Sunan mahaifiyarsa Sayyada Fadima. Ya fara karatun Alkur’ani mai girma a wajen mahaifansa ya fara karatun Ilimomin addinin musulunci duka a wajen mahaifinsa kamar irin su Fikihu, Luga, da Nahawu.

   

  Ya cigaba da zama a gaban yayan mahaifinsa a lokacin shi ne sarkin Dukku na ana kiran sa da suna Sarki Haruna Rashid, mai rubutun tarihin ya ci gaba da cewa Sarki ya tura mahaifin Maulana zuwa wani yanki don ya ci gaba da gudanar da karantarwar addinin musulunci kamar yadda suka gada iyaye da Kakani.

   

  Maulana ya ci gaba da zama a garin Dukku, bai bi mahaifinsa ba sakamakon Sarki Haruna Rashidi ya ce yana son zama da Maulana saboda kiyaye faɗin wani baƙon Malami da ya zo wucewa ta ƙasar Dukku ya ke cewa “Wannan matashin zai taka matsayi mai girma awilaya.

   

  Maulana Modibbo Aliyu Jobbo ya shiga garin Gombe, wajen shahararren malami Alkalin gari Wazirin gari Shehu Ahmad Tijjani Ibn Abubakar

  wanda Shehu Ibrahim ya ke yabonsa a cikin Rihla Hijaziyya.

   

  Maulana har sai da ya kai matsayin dukkan babu kamarsa Shehin yana cewa “Duk wanda ya yi karatu a wurina to ya maimaita a wajen Modibbo Jobbo” Sauda dama ya kan ce musu Ku dinga daukan karatu a wajensa.

   

  Sannan ana cewa faɗin girman shaharar wannan makaranta ta Waziri Tijjani ta kai ba’a inda ake samun irin ta sai Irin ƙasar Kano, da ƙasar Zazzau a faɗin ƙasar Najeriya ta yanzu.

   

  Makarantar ta fitar da shahararun waliyi irin su.

   

  Modibbo Jailani Yola

  Modibbo Umar Jarkasa

  Modibbo Tukur Gombe

  Modibbo Muhammadu Kagadama Jigawa Shehu Manzon Gombe

  Modibbo Ali Gombejo

   

  Da akwai da yawansu.

   

  Mai rubutun tarihin Allah ya saka masa da mafificin alheri, ya cigaba da kawo tarihin ya rubuta cewa: Waɗanda su kayi karatu suka zama manyan Malamai sunfi mutum ɗari Uku (300) daga wurare daban-daban a cikin ƙasar Najeriya, Jamhuriyar Nijar, Kamaru Jamhuriyar Tsakiyar Afirka (Central Afrika) da sauransu.

   

  Bayan komawa Sheikh Waziri Tijjani Allah ya ƙara yarda a gare shi, zuwa rahmar Ubangiji a garin Makka, bayan komawarsa aikin Hajji. almajiran Shehi gaba ɗayan su sun dawo zawiyyar Maulana Modibbo Jobbo, ya zamanto malami kuma jagora ga dukkan almajiran Shehu Ibrahim Niasee, Allah ya ƙara yarda a gare shi, na kasar Gombe da kewaye kuma zawiyyarsa ta zamo cibiyar Faira bayan bayyanar Faira, domin dukkan abin da Shehu Ibrahim Niasee Allah ya ƙara yarda a gare shi, zai aiko daga Kaulaha zuwa ga mukaddamai da muridai na al’ummar ƙasar Gombe da kewaye shi ya ke aikowa ya sannan ya tara muƙaddamai ya faɗa musu.

   

  Akwai alaƙa mai karfi tsakaninsa da Shehu Ibrahim Niasee Allah ya ƙara yarda a gare shi .

   

  Modibbo Jobbo yana da Ijazozi daban daban daga Shehunai mabanbanta kamar su Shehinsa Shehu Waziri Tijjani, Sheikh Ibn Umar Ainamali, Sheikh Adamu Badamagare Azare, Shekhul Hadis Sheikh Isma’il Ibn Ali daga Makkatul Mukarram, Shehul Hadi Murtaniya, da kuma shakundum wato Shehul Islam Alhaji Ibrahim Niasee Allah ya ƙara yarda a gare shi.

   

  Maulana Modibbo Jobbo yana da tarin almajirai da dama kamar yadda ya gabata a baya kusan dukkan almajiran Sheikh Waziri Tijjani almajiransa ne.

   

  Akwai daga fitattun almajiransa akwai:

   

  Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi

   

  Maulana Shehu Manzo Gombe.

   

  Maulana Modibbo Tukur Gombe

   

  Maulana Shehu Ibrahim Bogo

   

  Maulana Modibbo Muhammad Ali Garuza

   

  Shugaban alƙalai Yahya Ahmad (Grand Khadi)

   

  Maulana Halifa Sheikh Bashir Modibbo Jobbo

  Sheikh Habibu Modibbo Jobbo

   

  Maulana Sheikh Modibbo jelani Yola

   

  Maulana Modibbo Jobbo yana da ƴaƴa masu albarka kamar haka:

   

  Halifa Sheikh Bashir Modibbo Jobbo, Sheikh Habibu, Sheikh Mustafa , Sheikh Ahmad Tijjani akwai Sayyada Balkisu, Sayyada Asma’u, Sayyada Rukayya da Sayyada Rabi’atu

   

  Ya koma zuwa rahmar Ubangiji a shekarar 1973 wanda ya ci gaba jagorancin almajirai da ƴaya shi ne Halifa Sheikh Bashir Modibbo.

   

  Zawiyyar tana kan Titin Jankai Dawaki ta yamma a birnin Gombe.

   

  Na samu rubutun daga zuriyar Maulana na ƙara wasu batutuwan kadan a rubutun saboda na shigar da shi cikin jerin waɗanda nake kilacewa.

   

  Godiya ta musamman ga Adamu Habibu Jobbo Allah ya saka masa da mafificin alheri. Amiiiin

   

  Daga: Mujaheed M Muh’d

  Share
 • SHIN YA GASKATA CEWA” ITA DIN NA DAGA ZURIYAR MANZON ALLAH (S.A.W)” KO AKASIN HAKAN..?

  SHIN YA GASKATA CEWA” ITA DIN NA DAGA ZURIYAR MANZON ALLAH (S.A.W)” KO AKASIN HAKAN..?

   

  SARAUNIYA ELIZABETH II.

   

  Tun bayan da gidan jaridar “Al Ousboue” ta kasar Morocco ta fitar da labari dake hakaito cewa, Lallaine Sarauniyar England Elizabeth II, ta kasance Jikanyar MANZON ALLAH (S.A.W) a zageyen tsatso na 43, wannan labari ya tada hazo a gidan Malaman Tarihi, ko da yake wasunsu sun tafi akan baza’a gaskata ba, duk da babu cikekkiyar hujjar korewa.

   

  Amma a gefe guda Malaman tarihi kamar Harold B. Brooks-Baker, mawallafin littafin “Burke’s Peerage”, ya karfafa tare da gaskata wannan ikirari na wannan jarida ta silar Zaida ta “Salibiyun” wato Seville, wata gimbiya Musulma, wacce akaci garinsu da yaki, aka kame ta a matsayin baiwa, karshe ta koma Kristanci kuma ta kasance daya daga cikin matan Sarki Alfonso VI na Castile, amma sai dai bai bayyana karara cewa lallaine ita Zaida, shin da gaske tana da alaka da MANZON ALLAH (S.A.W) ko babu ba.

   

  Shima Masanin Tarihi wanda Jaridar Al-Ousboue ta wallafa wannan labari bisa dogara da bayanansa, yayi amannar cewa lallai akwai alaka mai karfi a tsakani, domin yayi amfani da Zaida a matsayin ganuwarsa na bibiyar tsatson Elizabeth, har ya gano ta kasance Jikanyar MANZON ALLAH (S.A.W) ta 43.

   

  Ya kara da cewa ” idan za mu iya dogara da bayanan asali na Spain na farkon-tsakiyar Karni. Dole ne a lura, duk da haka, yawancin majiyoyin mu daga zamanin jahiliyya, suna jayayya ko rashin tabbas, don haka ba zai yiwu a yi wani cikakken bayani ba. Mabuɗin haɗin bayanan sune:

   

  A cikin shekarar 1023, Abu al-Qasim Muhammad ibn Abbad ya zama sarkin Seville a al-Andalus. A da shi ne Qaadi (alkali) wanda halifan Cordoba ya nada, amma ya kwace mulki ya kafa daularsa, wato Abbadidas.

   

  Ta kasance zuriyar ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) ta hanyar diyarsa Fatima kuma jikansa Hasan ibn Ali. A shekara ta 1091, Almoravids daga Morocco sun mamaye Musulmin Spain, kuma jikansa Al-Mu’tamid ibn Abbad ya rasa gadon sarautarsa. ‘Yarsa Zaida ta gudu daga arewa kuma ta fake a kotun Sarki Alfonso na shida na Leon. Ta zama uwargidansa – Sarki ya riga ya yi aure, amma matarsa ​​tana kwance da rashin lafiya. Daga baya Zaida ya koma Kiristanci, ta dauki sunan baftisma Isabella kuma – da matar sarki ta mutu – sai ita (Zaida) ta aure shi, ta haifa masa ‘ya’ya uku da muka sani.

   

  A cikin shekara ta 1352 Maria de Padilla, zuriyar Zaida da Alfonso, ta zama uwargidan Sarki Peter ‘mai zalunci’ na Castille. Sun haifi ‘ya’ya hudu – biyu daga cikin ‘ya’yan mata sun auri ‘ya’yan Sarki Edward III na Ingila. Daga Isabella na Castille da Edmund, Duke na York ne Sarauniyar Burtaniya ta yanzu ta fito.

   

  GA YADDA TSATSON NATA YA SAMO ASALI.

   

  Elizabeth II, Sarauniyar Burtaniya – ‘yar George VI, Sarkin Burtaniya – ɗan George V, Sarkin Burtaniya – ɗan Edward VII, Sarkin Burtaniya – ɗan Victoria, Sarauniyar Ingila. Birtaniya – ‘yar Edward, Duke na Kent da Strathearn – dan George III, Sarkin Birtaniya – dan Frederick, Yariman Wales – dan George II, Sarkin Birtaniya – dan George I, Sarkin Birtaniya – ɗan Sophia, Zaɓaɓɓen Hanover – ‘yar Elizabeth ta Bohemia – ‘yar James I/VI, Sarkin Ingila, Ireland & Scotland – ɗan Maryamu, Sarauniyar Scots – ‘yar James V, Sarkin Scots – ɗan Margaret. Tudor – ‘yar Elizabeth ta York – ‘yar Edward IV, Sarkin Ingila – ɗan Richard Plantagenet, Duke na York – ɗan Richard na Conisburgh, Earl na Cambridge – ɗan Isabella Perez na Castille – ‘yar Maria Juana de Padilla – ‘yar Maria Fernandez de Henestrosa – ‘yar Aldonza Ramirez de Cifontes – ‘yar Aldonza Gonsalez G Black Iron- ‘yar Sancha Rodriguez de Lara – ‘yar Rodrigo Rodriguez de Lara – ɗan Sancha Alfonsez, Infanta na Castile – ‘yar Zaida (aka Isabella) – ‘yar Al-Mu’tamid ibn Abbad, Sarkin Seville – ɗan Abbad. II al-Mu’tadid, Sarkin Seville – dan Abu al-Qasim Muhammad ibn Abbad, Sarkin Seville – dan Ismail bn Qarais – dan Qarais bn Abbad – dan Abbad bn Amr – dan Amr bn Aslan – dan daga Aslan bn Amr – dan Amr bn Itlaf – dan Itlaf bn Na’im – dan Na’im II al-Lakhmi – dan Na’im al-Lakhmi – dan Zahra bint Husayn – ‘yar Husayn bn Hasan. dan Hasan bn Ali – dan Fatima – ‘yar ANNABI MUHAMMAD (SAW).

   

  Ko da yake, wasu zasu iya kore wannan dangantaka, kasancewar fadin ALLAH a Suratul Ahzab (33:33)

   

  إنما يريد الله ليذهب عنكم الرجس أهل البيت ويطهركم تطهيرا

   

  Ma’ana: Lallai Abin sani kawai, ALLAH Yana nufin Ya tafiyar da (Duk) ƙazanta daga gare ku, yã mutãnen gidan ANNABI, kuma Ya tsarkake ku tsarkakewa.

   

  Kuma ita ba ta kasance Musulma ba, baldai ta kasance “Ahlal Kitabi” saboda haka kai tsaye wannan aya na iya kore kowacce irin dangantaka tsakaninta da zamowa Jikar MANZON ALLAH (S.A.W), kuma ko da ace ta tabbata a tarihi hakane, to Waki’ar ANNABI NUHU (A.S) da Dansa shima na iya kore hakan, tunda ALLAH yace “إنه ليس من أهلك”

   

  Ma’ana:- Shi baya daga cikin iyakanka.

   

  Sannan mun sani Kristoci na yiwa ALLAH kishiya ta hanyar nasabta masa, ‘Da, da Mata, kuma ALLAH ya fadi a Suratu Tauba aya ta 28 “يا أيها الذين آمنوا إنما المشركون نجس”

   

  Ma’ana Yaku wanda sukayi Imani, lallaine Mushrikai Najasane” kaga kuma ALLAH ya tsarkake Iyalan gidan MANZON ALLAH (S.A.W) daga kowacce irin Najasa, kamar yadda aya ta gabata akan haka, kenan Najasa bai zamowa daga Ahalin gidan MANZON ALLAH (S.A.W).

   

  Sai dai abin lura shine “Ko ayayin da Turawa sukayi mamaya ga daular Musulunci a Salibiyyun a yankin Spain da (Andulus) Turkiya ayau, yazamo babu zabi ga duk wanda suka kama a matsayin bawa ko baiwa ko ya chanja Addini zuwa Kristanci ko kuma su kasheshi, dayawa daga Musulmai sun zabi su boye Musuluncinsu a zuci da yin ibadu a boye, ta hanyar bayyana Kristanci a fili (Ta siffar sutura da zuwa wajen Bauta), wanda wannan Dabi’a ta bisu wasunsu har zuwa yau, zaka samu Mutanen Turkey bazaka iya gane wasu daga Musulminsu ta hanyar sutura ba, ko da ace basu kasance suna Bayyana Kristanci ba, saboda yanci.

   

  Domin dayawansu sun hardace Kur’anine da hadisan MANZON ALLAH (S.A.W) ta hanyar zuwa cikin daji, su shiga cikin kogo su buya. Ko ayayin da suka shigo cikin gari kuma su bayyana Kristanci a fili.

   

  Saboda haka, lallai babu kwararan hujjoji na tabbatarwa ko kuma kore danganenta da MANZON ALLAH (S.A.W), Sai dai kame baki cikin sha’aninta, da barin fadin muggan zance shine mafi alkairi ga komai sabanin hakan.

   

  ALLAH YA TABBATAR DAMU AKAN SHIRIYAR MANZON ALLAH (S.A.W) DUNIYA DA LAHIRA.

   

  ALHAMDULILLAH.

  Share
Back to top button