TARIHIN SAYYADA FATIMAH

  • Shugabar Matan Duniya-Da-Lahira SAYYIDA FADIMA AZZAHRA (Alaihas-Salaam).

    FATIMA, FATIMA CE.

     

    A Rana Ta 20 Ga Watan Jumada Al-Thani Aka Haifi SAYYIDA FATIMA (A.S)!!!

     

    Shugabar Matan Duniya-Da-Lahira SAYYIDA FADIMA AZZAHRA (Alaihas-Salaam)

     

    SAYYIDA FATIMA AZZAHRA (A.S) Ta Rayu a Wannan Duniyar Tsakanin Shekarun(20 Jumada Al-Akheera, 5BH/27 July 604 AD), Zuwa (03 Ga Jumada Al-Thani, 11 AH/28 August, 632),

     

    Wato Ta Rayu Tsawon Shekaru Ashirin Da Takwas’28′(Masu Albarka) Kenan a Wannan Duniyar.

     

    An Ruwaito a Hadisi Cewa SAYYIDA FATIMA (A.S) Tana Da SUNAYE Guda Goma(10) Kamar Haka:

     

    *1. FATIMA

    *2. SIDDIQAH

    *3. MUBARAKAH

    *4. ƊAHIRAH

    *5. ZAKIYYAH

    *6. RADIYAH

    *7. MARDIYYAH

    *8. MUHADDASAH

    *9. AZ-ZAHRAH

    *10. BATULA.

     

    Ya ALLAH! Ka Yarda Da Mu Albarkacin NANA FADIMA AZZAHRA(A.S) Da Kuma Zuri’arta.

     

    Ya ALLAH! Ka Bar Mu Da Ƙaunarsu, Har Su Shede Mu a Gaban MANZON ALLAH (S.A.W) a Bisa Soyayyarsu Ameeeeen.

    Share
  • TARIHIN SAYYADA FATIMAH YAR’ MANZON ALLAH (SAW) Kashi Na Biyar (5).

    JIMADA THANI Watan Haihuwar Tsokar Jikin MA’AIKI(S.A.W); NANA FATIMA AZ-ZAHRA’U

     

    7⃣ FALALAR SON SAYYIDA FATIMA(A.S);

     

    Aƙwai Hadisai Masu Yawa Da Aka Ruwaito Daga MANZON ALLAH(S.A.W) Akan Falalar Son SAYYIDA FATIMA(A.S);

     

    1. MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Ce;

     

    “Duk Wanda Ya So Faɗima Ƴa Ta, To Zai Kasance Cikin Aljanna Tare Da Ni.”

     

    2. A Wani Hadisi Kuma MANZON ALLAH (S.A.W) Ya Ce, “Son Faɗima Yana Amfanar Mutum a Wajaje Ɗari Daga Cikin Wajajen Akwai Lokacin Mutuwarsa, Zamansa a Ƙabari, Ranar Ƙiyama, Kan Siraɗi Da Kuma Wajen Hisabi.

     

    A Wata Ruwaye Ya Zo Akan Cewa; Son Faɗima Alama Ce Ta Imani, Ƙinta Kuma Alama Ce Ta Munafurci.

     

    A Wata Ruwaya Kuma MANZON ALLAH Ya Ce; “An Sanya Ma Faɗima Suna Faɗima Ne Domin ALLAH Ta’ala Ya Yaye Duk Mai Sonta Daga Wuta.” – Wato Ma’ana Bashi Ba Wuta.

     

    8⃣ WAFATINTA;

     

    Akwai Ruwayoyi Kusan Goma Da Suka Yi Magana, Amma Ruwayar Da Tafi Shahara Wacce Ni Nafi Gamsuwa Da Ita, Kuma Na Gani a Littaffan Manyan Magabata Ita Ce Uku Ga Watan Jimada Thani Shekara Ta 11 Bayan Hijira.

     

    9⃣ KABARINTA;

     

    Shima Wannan Akwai Saɓani Na Ainihin Inda Kabarinta Yake Amma Akwai Zantuka Uku Wasu Sun Ce a Baƙi’a Yake, Wasu Sun Ce Yana Tsakanin Kabarin MANZON ALLAH (S.A.W) Da Minbarinsa, Wasu Sun Ce Yana Cikin Ɗakinta.

     

    Allahu A’alam.

     

    Jama’a NANA FATIMA (A.S) Tana Da Girma Da Martabar Da Bazamu Iya Faɗar Taba Sanin Haƙiƙanin Girmanta Da Martabarta Da Darajarta Sai Mahaliccinta.

     

    Assalatu Was-Salamu Alaiki Ya Ummul-Mu’uminin

     

    Daga: Imam Anas

     

    ALLAH Ka Sanya Mu Cikin Jerin MASOYA NANA FATIMA (A.S), Ya Ƙara Mana ƘaunarTA (A.S)

     

    Amincin ALLAH Ya Ƙara Tabbata Ga CIKAMAKIN ANNABAWA DA MANZANNI (S.A.W). Amiin Yaa ALLAH

    Share
  • TARIHIN SAYYADA FATIMAH MATAR ALIYU BIN ALI DALIB (RA) Kashi Na Hudu (4).

    JIMADA THANI Watan Haihuwar Tsokar Jikin MA’AIKI(S.A.W); NANA FATIMA AZ-ZAHRA’U

     

    6⃣ MATSAYINTA A GURIN ALLAH(S.W.T) DA MANZON ALLAH(S.A.W):

     

    Lallai Haƙiƙa NANA FATIMA(A.S) Tana Da Matsayi Mai Girma a Gurin ALLAH Da MANZONSA.

     

    Mun Sani Ku San Komai Nata Sauƙaƙƙe Ne Daga Wajen ALLAH Maɗaukakin Sarki:

     

    Sunan Ta Sauƙaƙƙe Ne Daga Sama, ALLAH Ta’ala Ne Yayo Wahayi Ta Hanyar MALA’IKA JIBRIL Cewa; A Samata Wannan Suna ‘FAƊIMA’.

     

    Haka Nan Al’amarin Ɗaurin Aurenta, ALLAH Ne Ya Aiko Da Umarni Ga MANZONSA Cewa; Ya Aurar Da Ita Ga SAYYIDINA ALI(Karramallahu Wajhahu),

     

    Shi Yasa Lokacin Da Wasu Daga Cikin Sahabbai Da Suka Nemi Aurenta Basu Samu Ba, Suka Ce Ma MANZON ALLAH(S.A.W) Mun Nemi Auren ‘FAƊIMA’ Baka Bamu Ba, Amma Ka Aura Ma ALIYU???

     

    Sai Ya Ce Masu; Bani Na Hana Ku Ba ALLAH Ne Ya Hana Ku, Ya Aura Masa Ita, Haka Ma Lokacin Ɗaurin Auren Sai Da Aka Yi a Sama Gabanin Ayi Shi a Ƙasa Kai Hatta Likkafaninta Daga Gidan Aljanna Aka Zo Da Shi.

     

    Haka Nan Ya Zo a Hadisi Daga MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Ce;

     

    “Duk Wanda ‘Faɗima’ Ta Yarda Da Shi, To ALLAH Ya Yarda Da Shi, Wanda Kuma Take Fushi Da Shi, To ALLAH Yana Fushi Da Shi.”

     

    Wato Dai ALLAH Yana Fushi Da Fushinta, Yana Kuma Yarda Da Yardarta.

     

    A Wani Hadisi Kuma MANZON ALLAH Yana Cewa; “Azaba Ta Tabbata Ga Duk Wanda Ya Zalunce Ta Ko Ya Zalunci Zuriyarta”.

     

    Daga: Imam Anas

     

    ALLAH Ka Sanya Mu Cikin Jerin MASOYA NANA FATIMA(A.S), Ya Ƙara Mana ƘaunarTA (A.S)

     

    Amincin ALLAH Ya Ƙara Tabbata Ga CIKAMAKIN ANNABAWA DA MANZANNI (S.A.W). Amiin Yaa ALLAH

    Share
  • TARIHIN SAYYADA FATIMAH YAR’ FIYAYYEN HALITTA (SAW) Kashi Na Uku (3).

    JIMADA THANI Watan Haihuwar Tsokar Jikin MA’AIKI(S.A.W); NANA FATIMA AZ-ZAHRA’U

     

    5⃣ DARAJOJINTA/SIFFARTA;

     

    Darajojinta Suna Da Yawa, NANA FATIMA(A.S) Ta Kasance Ma’abociyar; Kyau Da Kwarjini Da Kamewa Mai Haƙuri,

     

    Ma’abociyar Addini, Zaɓaɓɓiya, Mai Mutunci, Mai Biyayya, Mai Yawan Godiya Wa UBANGIJI Maɗaukakin Sarki Ce.

     

    MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Bayyana Cewa;

     

    فاطمة بضغة منى يربني ما رابها، ويؤذونى ما آ ذاها.

     

    Muslim Hadisi Na(2449).

     

    Fassara: “Faɗimatu Tsokace Daga Jikina, Duk Abin Da Ya Fusatata Yana Fusatani, Abinda Ya Cutar Da Ita Yana Cutar Dani.” Kaɗan a Cikin Darajojinta.

     

    1. NANA AISHA(ر ضي الله عنها) Ta Ce:

     

    Faɗimatu Ta Zo Tana Mai Tafiyarta Irin Tafiyar MANZON ALLAH (صلى الله عليه وعلى ءاله وسلم ) Sai Ya Miƙe Mata Ya Ce “Maraba Da Ƴata”.

     

    2. An Karɓo Daga NANA UMMU SALAMA Ta Ce: Haƙiƙa MANZON ALLAH(صلى الله عليه وعلى ءاله وسلم ) Ya Rufa Mayafi Akan: Sayyidina Alhassan Da Hussaini Da Aliyu Da Faɗimatu, Sannan Ya Ce;

     

    “Ya Ubangiji! Waɗannan Sune Ƴaƴan Gidana Kuma Keɓantattu, Ka Tafiyar Da Dauɗa Gabanin Su, Sannan Ka Tsakake Su Tsarkakewa.”

     

    Sai Nana Ummu Salama Ta Ce, Ina Tare Da Su Yaa MA’AIKIN ALLAH???”

     

    Sai Ya Ce; ”Ke Ma Kina Kan Alkhairi.”

     

    3. NANA AISHA(R.A) Ta Ce; Nana Faɗima Ta Yi Kama Da ANNABI MUHAMMADU(S.A.W).

     

    4. An Karɓo Daga Abi Sa’ad: MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Ce: “Wani Ba Zai Fusata Ahalin Gidana Ba, Face ALLAH Ya Shigar Da Shi Wuta”.

     

    Daga: Imam Anas

     

    ALLAH Ka Sanya Mu Cikin Jerin MASOYA NANA FATIMA (A.S), Ya Ƙara Mana ƘaunarTA (A.S)

     

    Amincin ALLAH Ya Kara Tabbata Ga CIKAMAKIN ANNABAWA DA MANZANNI (S.A.W). Amiin Yaa ALLAH

    Share
  • TARIHIN SAYYADA FATIMAH YAR’ MANZON ALLAH (SAW) Kashi Na Biyu (2).

    JIMADA THANI Watan Haihuwar Tsokar Jikin MA’AIKI(S.A.W); NANA FATIMA AZ-ZAHRA’U

     

    3⃣ LADUBBANTA/SUNAYENTA;

     

    Daga Cikin Ladubbanta Akwai;

     

    Ma’asuma,

    Mazluma,

    Karima,

    Sabira

    Mabaruka,

    Da Sauransu.

     

    Ya Zo a Hadisi Cewa; ‘NANA FATIMA(A.S)’ Tana Da Sunaye Guda Tara a Wajen ALLAH Maɗaukakin Sarki;

     

    1. FAƊIMA: Ma’anar Faɗima Ya Zo Da Ma’anoni Daban-Daban a Ruwayoyi, Amma Ma’anar Da Tafi Shahara Ita Ce; ALLAH Ta’ala Ya ‘Yanta Ta Daga Wuta Da Dukkan Masu Sonta.

     

    2. SIDDIƘA: Ma’ana Mai Yawan Gaskiya Ko Mai Gaskiya a Dukkan Zantukanta Ko Kuma a Wata Ma’ana Mai Yawan Gasgatawa Ga Saƙon Da Mahaifinta Ya Zo Da Shi.

     

    3. MUBARAKA: Ma’ana Ma’abociyar Albarka.

     

    4. ƊAHIRA: Ma’ana Tsarkakakkiya Daga Dukkan Najasa Ta Zahiri Da Baɗini.

     

    5. ZAKIYYA: Ma’ana Tsarkakakkiya Daga Dukkan Munanan Ɗabi’u.

     

    6. RABIYYA: Ma’ana Yardarta Da Hukunci Ko ‘Kaddara Ta ALLAH Ta’ala.

     

    7. MARDIYYA: Ma’ana Yardajjiya a Wajen ALLAH Maɗaukakin Sarki.

     

    8. BATULA: Ma’ana Wadda Ba Ta Jinin Al’ada Na Mata Kamar Jinin Haila Ko Na Nifasi-Biƙi.

     

    9. ZAHRA: Ma’ana Wadda Take Da Haske Na Zahiri Da Baɗini, a Wata Ruwaya Ya Zo Akan Cewa; Ana Ce Ma Ta Zahra Ne Saboda Idan Tana Ibada To Haskenta Yana Bayyana Ga Ma’abota Sama Wato Mala’iku Kamar Yadda Hasken Taurari Yake Bayyana Ga Ma’abota ‘Kasa(Wato Mutane).

     

    4⃣ KINAYARTA;

     

    Haƙiƙa Tana Da Kinaya Masu Yawa Amma Waɗanda Suka Fi Shahara Sune;

     

    *. Ummul-A’immah

    *. Da Kuma Ummu Abiha.

     

    Daga: Imam Anas

     

    ALLAH Ka Sanya Mu Cikin Jerin MASOYA NANA FATIMA(A.S), Ya Ƙara Mana ƘaunarTA(A.S).

     

    • Amincin ALLAH Ya Ƙara Tabbata Ga CIKAMAKIN ANNABAWA DA MANZANNI (S.A.W). AMIIN YAA ALAH
    Share
Back to top button