CIKAMAKIN WALIYAI (Last Part)
CIKAR MURADIN SA
Muradin Shehu Ahmadu Tijjani RTA bai wuce samun muƙamin Ƙuɗubaniyyatil Uzma ba, burin nasa kuwa ya cika kamar yadda manyan waliyai da Annabi SAW suka yi masa bushara.
Allah ya bashi muƙamin Ƙuɗubul Maktum (ƙuɗubi Abin ɓoyewa) a ranar 18 ga watan safar 1214H, Sannan ya samu Muƙamin Ƙuɗubul Makhtum (Khatimil Auliya/Cikamakin waliyai) ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal 1214. Sidi Aliyu Harazumi yana cewa “daga cikin abubuwan da na shaida a rayuwar Shehu Tijjani na karama da mukamin sa, akwai watarana wuraren sulusin dare na tsakiya, a daren 12 ga watan Rabi’ul Auwal 1214H, Shehu Tijjani ya kama hannu na muka fara tafiya nan da nan sai ga mu a Dutsen Arfah, can daga sama wani koren haske ya sakko, a cikin hasken akwai wani hular sarauta, sai hular ta sauka bisa kan Shehu Tijjani ta zauna daram, daga nan sai muka dawo cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma hular na kansa bata bace ba”.
Waliyai da yawa sun samu ƙuɗubaniyyatil Uzma, amma babu wanin su wanda ya taɓa samun muƙamin Khatimil Auliya sai Shehu Tijjani RTA, Dama Shehu Ibn Arabi Alhatimi yayi bayanin cewa babu wanda zai samu wannan mukamin sai mutumin Fas wanda ake yiwa Alkunya da Abul Abbas.
WAFATIN SA
Ranar 17 ga watan Shawwal 1230H, bayan yayi sallar Asubah, yayi ƙaura zuwa ga mahaliccin sa, yana da shekaru 80 a duniya. Sidi Ahmad Ibn Sulaiman, Sidi Aliy Alguemar, Sidi Ɗahhar ibn Abdussaddaƙ (Allah ya kara musu yarda) sune suka yi masa sutura.
A Masallacin ƙarawin aka yi masa sallar jana’iza, duk wani babban mutum mai daraja ya halacci wannan jana’iza face Maulaya Sulaiman saboda baya gari a lokacin. Babban Alƙalin Fas ne yayi masa sallah, wato Sidi Muhammad ibn Muhammad Ibn Ibrahim Al khayyat, sannan a zawiyyar sa aka yi masa raudah.
Khalifan sa shine Sidi Aliyu Tamasiniy, wanda tun Shehu Tijjani yana raye yayi masa ishara akan cewa lallai yaje ya fadada gidan sa saboda nan gaba zai yi baƙi sosai. Shehu Tijjani ya damƙa amanar ya’yan sa a hannun Sidi Aliyu Tamasiniy, duk da dai gabanin wafatin Shehu Tijjani yayi musu aure, Sidi Muhammadul Kabir ya auri Fatimah, yar Sidi Muhammad ƙanin Shehu Tijjani, Sidi Muhammadul Habib kuma ya auri Hasana yar uwar Sidi Ahmad ibn Musa Turkiy.
Nan muka kawo karshen wannan tarihi, akwai cikakken bayani fiye da wannan a ainihin littafin, zan fitar dashi Insha Allah babu jimawa.
Nayi hadiyyar duk alherin dake cikin wannan aikin zuwa ga murabbina Sidi Muhammadul Bashir ( Ibrahim Bashiru ), kura-kuren dake ciki kuwa Allah ka dubi Shehu Tijjani ka yafe min.
Alhamdulillah!
✍️ Sidi Sadauki