TARIHIN SHEIKH TIJJANI

  • Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmad Tijjani RA Shugaban Waliyai Kashi Na Goma Sha Shida 16 (Khatmah).

    CIKAMAKIN WALIYAI (Last Part)

     

    CIKAR MURADIN SA

     

    Muradin Shehu Ahmadu Tijjani RTA bai wuce samun muƙamin Ƙuɗubaniyyatil Uzma ba, burin nasa kuwa ya cika kamar yadda manyan waliyai da Annabi SAW suka yi masa bushara.

     

    Allah ya bashi muƙamin Ƙuɗubul Maktum (ƙuɗubi Abin ɓoyewa) a ranar 18 ga watan safar 1214H, Sannan ya samu Muƙamin Ƙuɗubul Makhtum (Khatimil Auliya/Cikamakin waliyai) ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal 1214. Sidi Aliyu Harazumi yana cewa “daga cikin abubuwan da na shaida a rayuwar Shehu Tijjani na karama da mukamin sa, akwai watarana wuraren sulusin dare na tsakiya, a daren 12 ga watan Rabi’ul Auwal 1214H, Shehu Tijjani ya kama hannu na muka fara tafiya nan da nan sai ga mu a Dutsen Arfah, can daga sama wani koren haske ya sakko, a cikin hasken akwai wani hular sarauta, sai hular ta sauka bisa kan Shehu Tijjani ta zauna daram, daga nan sai muka dawo cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma hular na kansa bata bace ba”.

     

    Waliyai da yawa sun samu ƙuɗubaniyyatil Uzma, amma babu wanin su wanda ya taɓa samun muƙamin Khatimil Auliya sai Shehu Tijjani RTA, Dama Shehu Ibn Arabi Alhatimi yayi bayanin cewa babu wanda zai samu wannan mukamin sai mutumin Fas wanda ake yiwa Alkunya da Abul Abbas.

     

    WAFATIN SA

     

    Ranar 17 ga watan Shawwal 1230H, bayan yayi sallar Asubah, yayi ƙaura zuwa ga mahaliccin sa, yana da shekaru 80 a duniya. Sidi Ahmad Ibn Sulaiman, Sidi Aliy Alguemar, Sidi Ɗahhar ibn Abdussaddaƙ (Allah ya kara musu yarda) sune suka yi masa sutura.

     

    A Masallacin ƙarawin aka yi masa sallar jana’iza, duk wani babban mutum mai daraja ya halacci wannan jana’iza face Maulaya Sulaiman saboda baya gari a lokacin. Babban Alƙalin Fas ne yayi masa sallah, wato Sidi Muhammad ibn Muhammad Ibn Ibrahim Al khayyat, sannan a zawiyyar sa aka yi masa raudah.

     

    Khalifan sa shine Sidi Aliyu Tamasiniy, wanda tun Shehu Tijjani yana raye yayi masa ishara akan cewa lallai yaje ya fadada gidan sa saboda nan gaba zai yi baƙi sosai. Shehu Tijjani ya damƙa amanar ya’yan sa a hannun Sidi Aliyu Tamasiniy, duk da dai gabanin wafatin Shehu Tijjani yayi musu aure, Sidi Muhammadul Kabir ya auri Fatimah, yar Sidi Muhammad ƙanin Shehu Tijjani, Sidi Muhammadul Habib kuma ya auri Hasana yar uwar Sidi Ahmad ibn Musa Turkiy.

     

     

    Nan muka kawo karshen wannan tarihi, akwai cikakken bayani fiye da wannan a ainihin littafin, zan fitar dashi Insha Allah babu jimawa.

     

    Nayi hadiyyar duk alherin dake cikin wannan aikin zuwa ga murabbina Sidi Muhammadul Bashir ( Ibrahim Bashiru ), kura-kuren dake ciki kuwa Allah ka dubi Shehu Tijjani ka yafe min.

     

    Alhamdulillah!

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmad Tijjani RA Shugaban Waliyai Kashi Na Goma Sha Biyar 15.

    CIKAMAKIN WALIYAI (15)

     

    HIJIRAR SA ZUWA FAS

     

    Kamar yadda Annabi SAW yayi hijira daga makka zuwa Madina bisa dalilin tsana da tsangwamar makiyya Allah, haka Shehu Tijjani bisa dole yayi hijira daga Abu Samguna zuwa Fas saboda mulkin kama karya da turkuwa suke yi a wancan lokacin. A ranar 17 ga watan Rabi’ul Auwal 1213H Shehu Tijjani tareda iyalin sa da Almajirin sa Sidi Aliyu Harazumi da Sidi Muhammadul Mishiri RTA, sun isa garin Fas a ranar 6 ga watan Rabi’us sani 1213H, a lokacin shekarun Shehu Tijjani 63. A ranar sai Shehu Tijjani ya daure dabbobin sa a masallacin Jami’ar Ƙarawin, jama’a suka yi korafi kan cewa ai zasu lalata wurin da fitsari da kashi, Shehu Tijjani yace ba zasu yi ba, haka kuwa ya faru, washegari jama’a suka yi mamakin wannan karamar na Shehu Tijjani RTA.

     

    A gidan iyayen Sidi Aliyu Harazumi aka sauke Shehu Tijjani da iyalan sa, nan da nan labarin sa ya cika Fas saboda ilimi, hikima da karamar sa, sarkin Fas Maulaya Sulaiman, ya samu labarin Shehu Tijjani har yaso ya kulla alaƙa dashi amma malamai masu hassada da Shehu Tijjani suna kushe shi, har saida Alƙali Sidi Abdulƙadir ya wanke Shehu Tijjani a wurin Maulaya Sulaiman, Sannan ya gayyace shi cikin da’irar malaman ƙasar. Watarana wani gwani yana tafsirin Suratun Nas, Maulaya Sulaiman yace wa Shehu Tijjani ya tofa albarkacin bakinsa kan abinda gwanin ya faɗa, Shehu Tijjani yayi masa gyara da sharhi wanda duk malaman saida suka yi mamakin ilimin Shehu Tijjani, shi kuma Maulaya Sulaiman nan ya yarda lallai Shehu Tijjani yana saduwa da Annabi ido da ido kamar yadda ake fadi a gari, don haka shima sai ya nemi Shehu Tijjani ya sada shi da Annabi SAW, Amma ko sadu da Annabi ido da ido, bai iya jure hasken ba dole ya suma, bayan ya farka ya sallamawa Shehu Tijjani ya karɓi Ɗariƙar sa nan take sannan daga baya ya ba Shehu Tijjani gida a inda ake kira “Darul Miraya” ya zauna kyauta amma Shehu Tijjani kowani wata sai ya bada kudin hayan gidan ga mabuƙata bisa iznin Annabi SAW saboda tsammanin gidan na masarauta ne ba na Maulaya Sulaiman ba.

     

    Wata biyu bayan zaman sa a Fas ya umurci Sidi Aliyu Harazumi ya rubuta littafin “Jawahirul Ma’ani wa bulugul Amani fiy faidhi Abul Abbas Tijjani”, littafin da ya ƙunshi muhimman ilimomin Shari’a da Sufanci baki ɗaya.

     

    ZAWIYYAR FAS

     

    A farko, Shehu Tijjani da Almajiran sa suna wazifa ne a farfajiyar gidan sa, wani lokaci a zawiyoyi daban-daban, sai Annabi SAW ya umarce shi da ya gina nasa zawiyyar, Shehu Tijjani ya nemi kufai a “Dardas”, Duk da dai kufan yana da ban tsoro, babu mai iya shiga shi kaɗai, har ma wani majazubi mai suna Sidi Lahabi yakan kara kunnen sa a kofar kufen yana jiyo muryoyi kamar ana zikiri.

     

    An fara ginin zawiyar ne 4 ga watan Rabi’ul Auwal 1214. Maulaya Sulaiman ya aiko kuɗi mai yawa domin gina masallacin, Amma Shehu Tijjani yaƙi karɓa, yace “Wannan ginin yana hannun Allah ne kai tsaye”.

     

    Kafin a fara ginin, Shehu Tijjani ya rubuta wani Ismul A’azam a bisa babban dutse sannan a gana ya rubuta “Ya ubangiji na saboda sunan ka mai girma, ka kare almajirai na daga ƙaf zuwa ƙaf”, wato daga bangon duniya zuwa daya bangon, sannan yasa aka binne dutsen a inda aka tayar da ɗaya daga cikin dirkokin masallacin, wanda ake kira “Dirkar Zinari”.

     

    Bayan kammala ginin, majazubin nan wato Sidi Lahabi yace “Fas ta sake zama rayayya, musamman ma dai Dardas”.

     

    Mafi yawan lokuta in Shehu Tijjani yana zaune da sahabbansa a zawiyyar, sai ya tashi ya leƙa waje yana kallon dama da hauni yana murmushi, da suka tambaye shi dalili sai yace “Ina duba zawiyyar ne yadda take yanzu ne da yadda zata koma nan gaba wurin faɗi da tsawo”, gashi kuwa yanzu yadda ya misalta girman, haka ya kasance.

     

    ABUL ABBASI MAULANA WALIYULLAHI TIJJANI.

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmad Tijjani RA Shugaban Waliyai Kashi Na Goma Sha Hudu 14.

    CIKAMAKIN WALIYAI (14)

     

    ZAWIYYAR FARKO A TIJJANIYYA

     

    Shekara daya bayan Annabi SAW ya cika masa komai na Ɗarikar Tijjaniyya wato shekarar 1201H kenan, a lokacin da ya ziyarci Aini Madhi sai wasu mutane su goma suka zo masa ziyara daga garin “Oud Suf”, tara daga cikin su mutanen kauyen Kamar/Guemar ne, cikon na goman su kuma daga kauyen Tagzut yake. Sun taho ƙarƙashin jagorancin Sidi Muhammad Sassi wanda ya karbi Ɗarika 1198H daga hannun Shehu Tijjani RTA.

     

    Shehu Tijjani yayi musu izinin gina Zawiyya a Guemar, da suka koma sai suka samu wuri mai kyau a Tagzut suka gina zawiyyar, bayan shekara daya suka dawo wurin Shehu Tijjani yace kun gina zawiyyar? Suka ce Eh mun gina a Tagzut saboda duk wuri daya ne da Guemar din (wato babu nisa), Shehu Tijjani yace Allah da Manzon sa ba zasu karɓi Ginin zawiyya a ko ina ba sai a gabashin Guemar, don haka suka koma suka sake ginawa a Guemar, wannan shine zawiyyar farko a tarihin kafuwar Tijjaniyya.

     

    MATA DA YA’YAN SA

     

    A garin Abu Samguna aka haifi wata baiwa mai cikakken hankali da tarbiya kuma salihar mace wacce ake kira Sayyida Mabaruka, itace ta haifawa Shehu Tijjani RTA Ɗan sa Muhammadul Kabir wanda shima aka haife shi a Abu Samguna bayan ya ƴanta ta.

     

    Matar sa ta biyu kuwa itama waliyiyar mace ce kyakkyawar gaske a hali da suffa, mai cikakken hankali da tarbiyya, sunan ta Sayyida Mubarakah, ita kuma an ce Shehu Tijjani ya same ta ne a wuraren Sudan, wasu ma suna hasashen yar nigeria ce daga Daular El-kanemi, Itama baiwa ce, Shehu Tijjani ya yanta ta kana ya aure ta.

     

    Shehu Tijjani RTA yana matukar kaunar su saboda darajar su wurin Allah, har yana cewa “Albarkar Allah ta cigaba da tabbata a gidan da Mabaruka da Mubaraka suke ciki”.

     

    Yayan Shehu Tijjani guda biyu sun rasu a Abu Samguna, Sidi Isma’il da Sidi Muktar, sannan a Fas kuma daya ya rasu wato Sidi Khalifa (Allah ya kara musu yarda).

     

    Shehu Tijjani ya bar ya’ya biyu a duniya, Sidi Muhammadul Kabir wanda aka haifa a Abu Samguna da Sidi Muhammadus Sagir wanda ake kira da Muhammadul Habib, shi kuma a Fas aka haife shi hijira tana da Shekara 1215.

     

    Sidi Muhammadul Kabir yayi shahada lokacin yakin su da Turkawa, babu wanda yasan inda kabarin sa yake, wasu sun ce ma turkawan sun yanke kansa ne suka wuce dashi gidan tarihi a Turkiyya. Duk zuri’ar Shehu Ahmadu Tijjani sun samu ne ta tsatson Sidi Muhammadul Habib kuma raudar shi tana Aini Madhi.

     

    Allah ya ƙara musu yarda. Amiiiin Yaa ALLAH

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmad Tijjani RA Shugaban Waliyai Kashi Na Goma Sha Uku (13).

    CIKAMAKIN WALIYAI (13)

     

    FALALAR DARIKAR TIJJANIYYA

     

    Bayan Annabi SAW ya yiwa Shehu Tijjani RTA iznin bayar da wannan Ɗarikar, sai Shehu Tijjani ya rubuta wasikar neman Alfarma ga Annabi SAW saboda shi ba zai iya kallon Annabi ido da ido ya dinga magana yadda yaso ba saboda kunya da ladabi.

     

    A wasikar yana cewa:

     

    Ina neman Alfarma daga gareka ya Manzon Allah SAW ka tabbatar min ni da dukkan wayanda suka rayu cikin wannan Ɗariƙar, mutuwa da cikakken imani, Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya kiyaye mu daga azabar sa, da tsoro da firgici da firgita da dukkan sharri, daga lokacin mutuwa har zuwa lokacin da muka tabbata a gidan Aljannah, ya kuma gafarta mini da su dukkan zunuban mu da suka gabata baki daya da wayanda za muyi masu zuwa. Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya lullube mu da Al’arshin sa ranar kiyama, kuma ya shayar da mu a tafkin Shugaban mu Manzon Allah SAW. Ina rokon Ubangijin mu ya shigar da mu Aljanna ba tare da hukunci ko Azaba ba, ya sanya mu a rukunin farko na masu shiga Aljanna kuma ya tabbatar damu a cikin Firdausi da Adnan. Ina kuma roƙon Manzon Allah SAW ya tabbatar min da dukkan abin da aka ambata a cikin waɗannan wasika gareni da dukkan sahabbai na, Allah ya amshi abin da na roƙa gaba ɗayansa”

     

    Daga nan aka isar da wannan rubutu zuwa hannun Manzon Allah SAW mai albarka a farke ba a mafarki ba, Annabi SAW ya amsa masa da cewa: “Ka sani na tabbatar da dukkan buƙatun da ke cikin wannan wasiqar, tare da alqawari gare ka da su, har sai kun kasance tare da ni a matsayi mafi girma na Iliyin, Wassalamu Alaikum.”

     

    Bayan mutuwa cikin imani da shiga aljanna babu hisabi, a duniya akwai falalar samun Muƙamin ƙudubaniyya daidai da ƙuɗubai dubu daya ga duk mutum ɗaya wanda ya karbi darikar Tijjaniyya, Alhamdulillah.

     

    FA MU MABIYAN KA MUN SAMU

    WA KEDA UBA KAMAR NAMU

    DARIKA BA KAMAR TAMU

    ANA WURIDI KAMAR NAMU

    FA BABU KAMAR KA TIJJANI

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Goma Sha Biyu (12).

    CIKAMAKIN WALIYAI (12)

     

     

    SAMUWAR DARIKAR TIJJANIYYA

     

    A Tilmisan Shehu Tijjani ya haɗu da ɗaya daga cikin manyan almajiran sa, wato Sidi Muhammadul Mishiri RTA. Shehu Tijjani ya bashi Ɗariqar khalwatiyya sannan ya umarce shi ya dinga jagorantar khamsus salawatu domin Shehu Tijjani baya son yin kowacce irin jagoranci saboda tsananin ƙas-ƙas da kan sa.

     

    Jama’a suna zuwa gun Shehu Tijjani domin neman iznin kasancewar sa jagoran su, amma shi bayan ya basu Ɗarikar Khalwatiyya sai yace musu “ni daku abokai ne, ban fi ku ba ballantana in zama shehin ku”.

     

    Hijira tana 1191 Shehu Tijjani RTA ya kama hanyar zuwa Fas domin ziyartar raudar Maulaya Idris, sai ya bi ta Ujda, a nan ya haɗu da babban almajirin sa wato Sidi Aliyu Harazumi RTA a cikin ayarin matafiya. Bayan kwana kaɗan sai Shehu Tijjani ya nunawa Sidi Aliyu Harazumi karama ta hanyar tuna masa mafarkin da yayi da Shehu Tijjani tun shekaru biyu da suka wuce alhalin ya manta, Sidi Aliy Harazumi yace Alhamdulillah wannan ranar nake jira kuma tazo, Maulana gani a hannun ka kayi yadda kaso.

     

    Bayan Shehu Tijjani ya dawo Tilmisan sai ya cigaba da ilimantarwa da tarbiyantar da al’umma, amma saboda zalunci da hantarar bayin Allah da wani kwamandan yaƙi yake yiwa mutane, hijira tana da shekara 1196 shehu Tijjani ya bar tilmisan zuwa garin “Abu Samguna”. Wannan garin ya samo sunan sa ne daga wani baban Waliyyi wanda ake kira Abu Samguna, kuma an tabbatar Shehu Tijjani shine Waliyyi na arba’in da ya zauna a garin.

     

    A garin Abu Samguna, 17 ga watan Safar 1196H, Shehu Ahmadu Tijjani RTA ya samu kololuwar buɗi (Fat-hul Akbar) domin ya ga Annabi SAW ido da ido ba a bacci ba, dama ya saba ganin sa a haka amma wannan ganin ya girmi sauran saboda yanayin ganin da abinda ganin ya ƙunsa, wato Annabi SAW ya umarce shi da ya saki zikirin kowacce Ɗarika, daga wannan ranar shi (Annabi) da kansa ne shehin sa, shi zai dinga yi masa madadi, babu wani waliyyi mai iko dashi, sannan ya bashi izinin yin Astagfirullah 100, Salatin Fatihi 100 kullum, kuma yayi masa iznin bayar dasu ga duk wanda ya nema tareda sharuɗɗan da za a kiyaye,

     

    Sannan Annabi SAW yayi masa bushara cewa “Duk wanda ya karɓa daga gareka, da shi da iyalin shi da iyayen shi da masoyan shi za su shiga aljanna babu hisabi balle azaba, zasu kasance tare dani a “Illiyyina”, kaine mai ceto ga duk wanda ya bika, ka rike zikirorin nan da kyau ba tareda halwa ko wani jiyar da jiki wahala ba har abinda aka yi maka alkawari (ƙuɗbabniyyatil uzma) ya tabbata”.

     

    Bayan shekaru hudu wato 1200H, Annabi ya sake bayyana gareshi ya cika masa da La ilaha illallahu 100 da sauran abubuwa wayanda Ɗarikar Tijjaniyya ta ƙunsa a yau. A shekarar nan ne kuma Shehu Assammani ya rasu, don haka jama’a suka karkato gaba daya ga Shehu Tijjani domin neman ilimi da saduwa da Allah ta hannun sa, suna zuwa masa da kyaututtuka na kudi da dukiya irin su raƙuma.

     

    RANAR LARABA 21 AUGUST 2024 SHINE DAIDAI DA 17 SAFAR 1446, DARIKAR TIJJANIYYA TA CIKA SHEKARU DARI BIYU DA HAMSIN (250 YEARS) DA SAMUWA.

     

    Alhamdulillah Masha’Allah

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
Back to top button