TARIHIN SHEIKH TIJJANI

  • Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Goma Sha Daya (11)

    CIKAMAKIN WALIYAI (11)

     

    AIKIN HAJJI DA DAWOWAR SA TILMISAN

     

    A Makka ya sadu da babban ƙudubi wato Sidi Ahmad ɗan Abdullahi Al-hindi RTA wanda ya kasance baya fitowa balle a ganshi ko ya ga mutane, sai hadimin sa ɗaya kawai ke iya ganin shi, don haka ya aikowa Shehu Tijjani wasiƙa yana mai sanar dashi cewa “kaine magajin sirrorina da haskena (ma’arifa) da komai nawa”. A lokacin da ya rubuta wannan wasikar, sai ya sanar da hadimin nasa cewa “wannan shine wanda na dade ina jiran tahowar sa, shine magaji na”, hadimin sai ya ce “haba shehi na, ni da na kwashe shekaru sha takwas ina maka hidima baka sanya na zama magajin ka ba sai bako daga magrib”, Sidi Ahmad Al-hindi yace ai zabin Allah kenan, wanda yaso yake ba baiwar sa, inda ace ni ke da ikon zaɓo magaji na, ai ɗa na zan ba tun kafin ka sanni.

     

    Sidi Ahmad Al-hindi ya gadar da komai nasa ga Shehu Tijjani sannan ya damƙa amanar karatun ɗan sa a hannun Shehu Tijjani RTA, kana ya sanar da cewa zai bar duniya ranar ashirin ga watan zul hajji, haka kuwa ya faru. Shehu Tijjani yaso ya sadu da shi ido da ido amma yace masa ba zai yiwu ba saboda yanayin muƙamin sa, sai dai yayi mai busharar saduwa da wanda zai hau mukamin sa bayan yayi wafati wato Sidi Muhammad ɗan Abdulkarim Assammani RTA.

     

    Bayan Shehu Tijjani ya kammala aikin hajji a makka kuma ya shayar da ɗan Sidi Ahmad Al-hindi ilimomi kamar yadda mahaifin nasa ya bukata, sai ya tafi madina domin ziyartar kakan sa shugaban halitta SAW. A madina ya sadu da Sidi Muhammad Assammani kamar yadda Sidi Ahmad Al-hindi yayi masa bushara.

     

    Assammani Ɗarikar sa ta samo asali ne daga Ƙadiriyya, Shazaliyya da khalwatiyya. Ya yiwa Shehu Tijjani iznin ismul A’azam gaba daya da sauran asrarai sannan yace Shehu Tijjani ya tambayi duk abinda yake so, Shehu Tijjani ya tambaya shi kuma ya lamunce mai.

     

    Daga Madina sai Shehu Tijjani ya sake dawowa Cairo domin ya ziyarci Sidi Mahamudul Kurdiy, a nan ne ya samu ijazar hadisi da sauran fannonin ilimi daga Sidi Mahamudul Kurdiy saboda ya shirya masa tambayoyi masu wahala a fannonin ilimi kuma Shehu Tijjani ya bada amsoshi gamsassu wayanda suka ƙayatar da malaman misra baki daya.

     

    Ya kuma bashi ijazar Ɗarikar Khalwatiyya da ikon shigarwa, koyarwa da tarbiyantar da mutane cikin ta amma Shehu Tijjani bai yarda ba sai Sidi Mahamudul Kurdiy yace masa kar ka damu, kawai ka wadatu da iznin ni kuma zan ji da sauran, daga nan suka yi bankwana, Shehu Tijjani ya koma tilmisan.

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • Takaitaccen Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Goma (10).

    CIKAMAKIN WALIYAI (10)

     

    TAFIYAR SA AIKIN HAJJI

     

    Hijira tana da shekara 1186, a lokacin Shehu Ahmadu Tijjani yana da shekaru talatin da shida a duniya, sai ya ga dacewar ya tafi aikin hajji da ziyarar kakan sa sanadin samuwar halittu baki daya, shugaban mu Annabi Muhammadu SAW.

     

    A hanyar sa ya sadu da Sidi Muhammad ɗan Abdurrahman Al az-hariy a garin “zawawa” na Algeria inda ya karɓi Ɗariƙar Halwatiyya Rahmaniyya daga wurin sa. Ko da ya isa tunisia, ya ziyarci waliyai da dama, daga cikin su akwai Sidi Abdussamad na Ɗarikar Halwatiyya amma shima karkashin Babban Ƙudubin Kasar yake, shi kuma babban ƙudubin babu mai ganin sa sai wasu mutane hudu kuma a daren Litinin da Juma’a kawai suke haduwa dashi, daga cikin su akwai Sidi Abdussamad, Don haka sai Shehu Tijjani ya ba shi ƙwandalar zinari da ake kira “Mahbub” ya kaiwa wannan ƙuɗubin a matsayin hadiyya, ai kuwa sai ya dawo masa da amsa mai dadi daga ƙudubin cewa “Almahbub ba’athal Mahbub” wato masoyi abin ƙauna ya bada kyautar ƙwandalar zinari.

     

    A tunisia Shehu Tijjani RTA ya sadu da Annabi SAW yace masa ya roki ilimin da yake so ko wani abu daban shi kuma zai ce masa Amin, Shehu Tijjani ya roƙa, sai Annabi SAW ya karanta Suratut duha, yana zuwa ayar “wala saufa” sai ya kalli Shehu Tijjani kallon soyayya sannan ya ƙarasa karatun. Shekarar Shehu Tijjani guda tsakanin garin tunis da sousse yana ibada da koyar da ilimomi har da Al-hikamil Aɗa’iyya, saboda ilimin sa ne ma Sarkin tunisia ya aiko masa sako akan yana so ya zauna a ƙasar a matsayin malamin ilimi da fatawa, zai bashi gida da albashi har da shaidar kasancewa farfesa daga jami’ar Zaituna na Tunis. Shehu Tijjani bai ce komai ba sai washegari kawai ya nemi jirgin ruwa ya tafi alƙahira (cairo) na ƙasar masar (Egypt).

     

    A cairo ya sadu da Sidi Mahamudul Kurdiy RTA, yace masa “Allah yana son ka a duniya da lahira”, Shehu Tijjani yace taya kasan haka? Mahamudul Kurdiy yace Allah ne ya gaya min, sai Shehu Tijjani yace masa nayi mafarki da kai yayin da nake tunis, nace maka an yi nine da ƙarfe, sai kace kwarai haka ne, amma zaka mayar da ƙarfen nawa zuwa zinari, yana gama fadi sai Mahamudul Kurdiy yace kwarai haka yake kamar yadda ka gani. Bayan yan kwanaki sai Mahamudul Kurdiy ya tambayi Shehu Tijjani RTA game da burin sa, sai yace ni burina in samu ƙuɗubaniyyatil Uzma, Mahamudul Kurdiy yace Allah yayi maka tanadin muƙami fiye da na Imamu Shazali (wato fiye da ƙuɗubaniyyatil Uzma da yake nema).

     

    Shehu Tijjani ya hau jirgi daga Misra zuwa Sa’udiyya ya ƙarasa birnin Makka a watan shawwal, hijira tana da shekara 1187.

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • Sunayen Kakanin Sheikh Ahmadu Tijjani RA Har Zuwa Manzon Allah SAW.

    SALSALAR SHEIKH AHMAD TIJJANI R.A.

     

    ZA KAJI WANENE SHEHUN MU SHEHU TIJJANI R.A.

    Shehu Tijjani R.A. Jikan Annabi Muhammadu S.A.W.

    An haifeshi Ranar Alhamis (13) ga Watan Safar Hijra (1150).

    Shine Shehu Ahmad Tijjani R.A. Dan Shehu Muhammad

    Dan Shehu Muhammadul Mukhtar R.A.

    Dan Shehu Ahmad R.A.

    Dan Shehu Muhammad R.A.

    Dan Shehu Salim R.A.

    Dan Shehu Ahmad (Wanda Ake Ma Laqabi Ul’wani R.A.).

    Dan Shehu Ahmad R.A.

    Dan Shehu Aliyu R.A.

    Dan Shehu Abdullahi R.A.

    Dan Shehu Abbas R.A.

    Dan Shehu AbdulJabbar R.A.

    Dan Shehu Idris R.A.

    Dan Shehu Idris R.A.

    Dan Shehu Ishaqa R.A.

    Dan Shehu Zainul Abideen R.A.

    Dan Shehu Ahmad R.A.

    Dan Shehu Muhammadu Nafsiz Zakiyya R.A.

    Dan Shehu Abdullahil Kamil R.A.

    Dan Imamu Hasanul Musannah R.A.

    Dan Imamu Hasanus Subdi R.A.

    Dan Sayyiduna Aliyu Karamallahh Wajhahu A.S./R.A. Da Fadimatuz Zahra’u A.S.Yar Annabi Muhammadu S.A.W.

    To Kaji Jinin Annabi Muhammadu S.A.W.

    Wadannan Sune Iyayen Shehun Mu Shehu Tijjani R.A, Allah Ka Barmu Da Shehu Tijjani R.A. Amiin Yaa ALLAH

     

    Daga: Kamal Saidu Ibrahím

    Share
  • Takaitaccen Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Tara (9)

    CIKAMAKIN WALIYAI (9)

     

    TAFIYAR SA ZUWA TILMISAN

     

    Hijira tana shekara 1181, a lokacin Shehu Ahmadu Tijjani RTA yana da shekaru talatin da daya a duniya ya tafi “tilmisan”, babban gari a ƙasar Algeria mai ɗauke da al’umma daban-daban saboda tarin albarkar dake cikin sa.

     

    A wannan garin ne Shehu Tijjani ya sadaukar da lokacin sa wurin koyar da tafsiri da hadisi da kuma ayyukan sa na Ibada, mutanen garin da malamai suna matuƙar kaunar sa kuma suna girmama shi saboda madarar ilimi da tarin hikimar sa. Jama’a sukan tambaye shi inda ya samo wannan ilimin, sai yace musu “ban samu ilimi na lokaci daya ba kuma ba daga wurin malami daya na samu ba face daga wurin duk wayanda na zauna dasu”.

     

    Wannan baiwar na Shehu Tijjani yasa shi samun mabiya daga ciki da wajen tilmisan, wasu suna zuwa ne don neman ilimi, wasu suna zuwa ne don neman albarkar sa saboda sun dauke shi babban Shehi, shi kuwa yana tsawatar musu bisa faɗin haka saboda tawadi’u (ƙas-ƙas da kai) irin nashi.

     

    A tilmisan ne Shehu Tijjani yayi mafarki da babban ƙudubin nan kuma gausun zamanin sa mai suna Sidi Abu madyan, ya ganshi a cikin taro yana cewa “wa zai bani kyauta ni kuma in lamunce masa abinda yake so”, Shehu Tijjani yace masa zan baka masaƙil (nau’in lissafin kudi a wancan lokacin) guda hudu kai kuma sai ka lamunce min samun ƙuɗubaniyyatil Uzma, Abu madyan yace na lamunce maka, Shehu Tijjani zai mika masa kudin kenan sai ya farka.

     

    Gari yana wayewa ya tafi raudar Abu Madyan yace “ga abinda nayi alkawarin baka amma zan rabawa mabuƙata sai ladan ya iso gareka”, yaje yana raba musu kenan sai wani daga cikin su yace “zan aurar da yarinya bani da kudi sai nayi kamun ƙafa da waliyyin nan Abu Madyan jiya, kaga shine Allah ya bani domin sa”, Shehu Tijjani yayi murmushi kawai ya tafi.

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • Takaitaccen Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Takwas (8).

    CIKAMAKIN WALIYAI (8)

     

    KOMARWA SA AINI MADHI DAGA FAS

     

    A cikin mu’amalar sa da waliyai, ya haɗu da babban waliyyin Malamatiyya, Sidi Ahmad (RTA) wanda ya ba Shehu Tijjani Ismul A’azam yace masa ya kamata ya shiga halwa har sai ya samu Fat-hul Akbar domin yana da babban muƙami nan gaba, Shehu Tijjani bai amince da haka ba sai shehin yace bakomai, muddin dai zai cigaba da karanta Ismul A’azam din da ya bashi, burin sa zai cika.

     

    Shehu Tijjani ya samu mukamai daga Halarar Ubangiji sosai saboda kokarin sa wurin riko da hanyoyin sufayen nan, kuma kullum ƙishirwan sa bai gushe ba saboda har yanzu bai riski burin shi ba.

     

    Shehu Tijjani ya hadu da wani waliyyi kashifi a Fas wanda ya bashi karfin gwiwar komawa gida (Aini Madhi) domin yana cewa “burin ka zai cika ne a yankin sahara”. Shehu Tijjani ya karɓi shawarar sa ya kama hanyar tafiya, a hanya ya tsaya a zawiyoyi daban-daban domin ziyartar waliyai har ya isa Aini Madhi.

     

    Daga Aini Madhi sai ya tafi “Albayad”, Tafiyar kilomita 100 da wani abu daga Aini Madhi, Ana yiwa garin lakabi da “Sidi Shekh” saboda a garin aka binne babban waliyyin nan jikan Sayyidina Abubakar Siddiƙ mai suna Abdulƙadir ɗan Muhammad (Allah ya kara musu yarda).

     

    A nan Shehu Tijjani ya zauna Shekara biyar yana koyarwa kuma yana ayyukan sa na sufanci sannan yana zuwa Aini Madhi lokaci-lokaci.

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
Back to top button