ZIYARA

  • RAHOTO: Ziyaran Sarkin Kano Dr Aminu Ado Bayero Kasar Algeria Tare Da Tawagar Sa.

    CIKAKKEN RAHOTON: Ziyara Sarkin Kano Dr, Aminu Ado Bayero Da Alh Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi Tare Da Tawagar Sa Kasar Algeria.

     

    Daga Babangida Alhaji Maina

     

    Mai martaba sarkin Kano Alhaji Dr Aminu Ado Bayero ya ziyarci kasar Algeria da Sayyadi Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi RA don gabatar da wasu muhimman abubuwan a Algeria inda suka samu tarba na musamman daga babban Khalifan Tijjaniyya na duniya Sheikh Khalifa Ali Bel Arabi da Sidi Ahmad bin Sidi Abdel Jabbar da manyan jami’an gwammati an kuma shirya masa liyafar cin abincin rana domin karrama shi. Tare Da Yan tawagar sa.

     

    Ziyaran wanda ta kunshi muhimman abubuwan masu muhimmmanci inda suka gabatar Algeria international conference mai taken Imam Mohammed Ibn AbdulKarim Al Maghili Governance Stability and Unity Of African Societies. A ranar 13/12/2022.

     

    Bayan kammala taron tawagar mai martaba sarkin Kano Dr, Aminu Ado Bayero sun ziyarci garin Aina Madi inda aka haifi shugaban Darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Ahmed Tijjani RA, inda Khalifa Ali Bel Arabi ya bayyana cikakken tarihin Sheikh Ahmad Tijjani RA tare da tarihin gidan maulanmu Shehu Tijjani RA.

     

    Tawagar mai martaba sarki da manyan shehunai da malamai tare da masu rakiya sun ziyarci masallacin Sidi Muhammad Al-Habib, mai cike da tarihin a Musulunci da Tijjaniyya.

     

    A karshen ziyarar mai martaba sarki, ita ce kabarin Sidi Belarabi El Damraoui, inda aka karanta Fatiha na littafin don hadiya gare shi da sauran al’ummar Musulmai baki daga, wanda Sheikh Sidi Belmashri ya Jagoranci.

     

    Babban bako mai martaba sarkin ya nuna matukar jin dadinsa da wannan ziyara da ya zama wajibi ga kowane dan Tijjaniyya ya kasance matakin farko a darikar sa shine Sheikh Sharif Ahmadu Tijjani RA, da kuma matsayin darikar Tijjaniyya a tsakanin bangarori da dama na ‘yan Najeriya. An kuma gabatar wa da mai martaba sarkin Kano sakon girmamawa wanda ya dace da matsayin da na basarake mai daraja.

     

    Cikin tawagar akwai Sheikh Prof, Muhammad Kabir Yusuf Hamdani, Dr Surumbai Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Dr, Lawi Sheikh Atiku Sanka, Ambassador Munir Yusuf Liman, Sayyadi Muktar Ibrahim Dahiru Bauchi.da sauran su.

     

    Allah ya dawo mana dasu gida lafiya, ya bada ladan ziyara, Allah ya kara taimako. Amiiiin

    Share
  • Muhimman Abubuwan Da Malamai Suka Bayyana Wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A Wata Ziyara.

    Malamin addinin Musulunci, sun yiwa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari nasiha a ziyarar da suka kai masa a kwanakin baya.

     

    Sannan sun ja hankalinsa kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi al’ummar Arewacin ƙasar nan.

     

    1 Malaman sun yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’an Allah ya bashi ikon kammala mulki lafiya.

     

    2 Sun sake tunatar dashi nauyi da yake kan sa na al’ummar Najeriya.

     

    3 Mun bashi shawarwari akan abubuwan da suke faruwa a kasa don ya gyara kuma ya dauki mataki.

     

    An tattauna maganar manyan ayyuka da gwamnatin tarayya take yi wanda ya kunshi titin dogo daga Kano zuwa kasar Niger da kuma titin mota daga Kano zuwa Kaduna, zuwa Borno.

     

    An tattauna maganar man fetur da aka haku a jihar Gombe/Bauchi wanda malamai suka bada shawara akan ayi kokari wurin kammala wannan muhimmin aiki wanda zai amfani arewacin Najeriya.

     

    Anyi magana akan bankuna na Bank of Industry da kuma bank of Empowerment wanda basa bawa yan arewacin Najeriya bashi kudi, kuma ya kamata a karfafa bangaren bankuna Musulunci kamar Ja’iz, da Jaz da sauran wanda yan arewacin Najeriya zasu amfana.

     

    Daukacin malaman sun bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari sharawa akan a cigaba da inganta fanni tsaro da tattanin arziki a arewacin Najeriya tare da taimakawa mutane.

     

    Daga karshe shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yada da wannan ziyara inda ya bayyana cewa malamai ba neman kudi ko mulki bale ya kawo su wurin mai mulki ba, ya kuma gode masu da irin wannan shawara da tunatar wa.

     

    Allah ya amfanar damu cikin wakilcin malaman Addinin Islama ya bashi ikon kariya sauran ayyuka masu amfani ga Najeriya. Amiiiin

    Share
  • Malaman Darikar Tijjaniyya Sun Ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A Gidan Sa.

    HOTUNAN ZIYARA:

     

    Ziyarar Malaman addini Musulunci na jihar Kano zuwa gurin mai girma Shugaba kasar Nigeria General Muhammadu Buhari a gidan sa dake Daura jihar Katsina.

     

    Cikin wakilcin malaman bangaren Tijjaniyya akwai Khalifa Sayyidi Bashir Tijjani Usman Zangon Bare-bare da Khalifa Sayyidi Ibrahim Usman Mai Hula (Shehi-Shehi) da Imam Nasir Adam Shugaban Limamai na jihar Kano.

     

    Ziyara ta kunshi manyan malamai daga bangarorin malaman Darikar Tijjaniyya dana Darikar Kadiriyya tare da malaman kungiyar Izala/Salafiyya. Na jihar Kano.

     

    Muna Addu’an Allah ya karbi ziyara ya amfanar damu cikin sa, Allah ya sanya albarka a tsakanin mu. Amiiiin

    Share
  • Dan Takaran Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Ziyarci Sheikh Dahiru Bauchi RA.

    Sheikh Dahiru Bauchi RA Ya Karbi Bakwancin Dan Takaran Shugaban Kasa Atiku Abubakar

     

    Maulana Lisanul Faidah Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA Ya Karbi Bakwancin Dan Takaran Shugaban Kasa A Najeriya Alh Atiku Abubakar A Gidan Sa Dake Birnin Bauchi.

     

    Alh Atiku Abubakar Shine Dan Takaran Shugaban Kasa A Najeriya Karkashin Jam’iyya PDP A Najeriya.

     

    Allah Ya Karawa SHEHU Lafiya Da Nisan Kwana Albarkacin Manzon Allah SAW. Amiin

     

    Tijjaniyya Media News

    Share
  • Shugaban Darikar Tijjaniyya Na Duniya Ya Ziyarci Shugaban Kasar Senegal

    Babban Khalifan Darikar Tijjaniyya Na Duniya Sheikh Khalifa Ali Bel Arabi Ya Ziyarci Macky Sall Shugaban Kasar Senegal.

     

    Khalifa Ali Bel Arabi tare da tawagar sa sun samu tarba a hukumance daga Macky Sall, shugaban kasar Senegal a kasar gwamnatin kasar Senegal.

     

    Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya yaba da kyakykyawar alaka dake tsakanin kasar Aljeriya da irin rawar da Darikar Tijjaniyya ke takawa wajen kulla alaka da soyayya tsakanin al’umma da tabbatar da hakuri da shugabancin Musulunci a kasashen Afirka.

     

    Khalifa Ali Bel Arabi ya gode wa shugaban kasar Senegal da kuma Abdelmadjid Tebboune saboda tsananin sha’awar da kwaunar Afirka na Aljeriya da kuma daukar nauyin wannan ziyara a karon farko.

     

    Muna addu’an Allah ya tabbatar da alkhairi ya karawa Khalifa lafiya da daukaka. Amiin

     

    Babangida A. Maina

    Tijjaniyya Media News

    Share
Back to top button