Biyayya Ga Manzon Allah SAW Shine Biyayya Ga Allah Subhanahu Wata’ala. Inji Sheikh Ibrahim Maqari.

ALLAH YA KEBANCI ANNABI MUHAMMADU S.A.W. DA WASU DARAJOJI AKAN SAURAN ANNABAWA BA.

 

An karbo hadisi daga “Jabir Dan Abdullah R.A. cewa Annabi Muhammadu S.A.W. Yace:

 

 

“An bani wasu abubuwa guda biyar (5) wadanda ba a ba dasu ba ga wani Annabi da yazo gabani naba:

 

1. An taimake Ni da tsorata abokan gaba wadanda tsakanina dasu akwai nisar tafiyar wata guda.

 

2. An sanya min kasa ta zamo tsarkakakkiya (wajen yin taimama) kuma gurin sallah, don haka; duk wanda sallah ta riske shi a hanya sai ya tsaya yayi.

 

3. Kuma an halattamin cin ganima wacce bata halatta ba ga wani Annabi daya zo gabanina ba.

 

4. An bani damar yin ceto (a farfajiyar kiyama).

 

5. Annabawan da suka zo gabani na sun kasance ana aiko sune zuwa ga mutanensu kawai; Amma Ni kuwa an aiko Ni ne zuwa ga mutane baki daya kai har da dabbobi ma”. [Bukari Da Muslim Ne Suka Ruwaito Shi].

 

Ya zo a cikin Sahihu-Muslim a Hadisin Anas R.A. cewa Annabi Muhammadu S.A.W. Yace: “Nine farkon wanda zai fara yin ceto ranar kiyama, kuma nafi dukkan Annabawa samun mabiya ranar kiyama”. “Nine kuma zan fara kwankwasa kofar Aljanna don a bude”. Ya zo a hadisin Abu-Huraira R.A. Cewa Annabi Muhammadu S.A.W. Yace:

 

“Nine shugaban ‘Yan-Adam” ranar kiyama. “Kuma Nine farkon wanda zai fara fitowa/tashi daga kabari ranar kiyama”.

 

“Nine kuma farkon wanda zai yi ceto, kuma farkon wanda za’a bashi damar yin ceto”. Allah Ka Bamu Albarkacin Annabi Muhammadu S.A.W.

 

Daga: Kamal Sa’eed Ibrahim

Share

Back to top button