Larabar Karshen Safar Ce Allah Yake Saukar Da Dukkan Bal’in Shekara.

Ranar Larabar Karshen Safar

 

A Larabar Karshen Safar Ce Allah Yake Saukar Da Dukkan Bal’in Shekara Kuma A Irin Wannan Larabace Annabi S,a,w Ya Kamu Da Ciwon Ajali

 

A Dan Haka Sufaye Suka Fitar Da Wannan Addu’a Da Sallah Da Rubutu Dan Mata Da Kanan Yara Dama Wanda Bai Samu Damar Aikata Sallahar Ba

 

Za’ayi Sallah Raka’a 4 Sallama 1 Kowace Raka’a Za’a Karanta Fatiha 1 Suratul Kausar 17 Suratul Ikhlasi 5 Suratul Falaqi Da Nasi Kafa 1

Zakayi Haka A Kowace Raka’a

 

Bayan Sallama Za’a Karanta Wannan Aya Mai Girma

والله غالب على أمره ولكن أكثر الناس لا يعلمون

Kafa 360

 

Sai JAUHARATUL Kamali Kafa Kafa 3

Sai Kacika Da

سبحان ربك رب العزة عما يصفون وسلام على المرسلين والحمد لله رب العالمين

Wanda Bai Iya Jauharaba Zai Iya Karanta Salatul Fatihi Madadinta

 

Sai Wanda Zaiyi Rubutu Yasha

Ana Rubuta

سلام سلام

Guda 7 Dake Cikin Alqur’ani Sai A Wanke Asha

 

Sashen Arifai Ma’abota Kashfi Sun Fada Cewa A Kowace Shekara Allah Yana Saukar Da Bal’i 320k A Cikin Shekara Amma A Larabar Karshen Safar Allah Yana Nunka Wannan Bal’i Shiyasa Itace Mafi Girman Rana A Ranakun Shekara Ranace Mai Hadari

 

Wanda Yayi Wannan Sallah Da Kaifiyyar Da Muka Ambata Ko Ya Rubuta Wadannan Ayoyi Yasha Allah Zai Kareshi Daga Dukkan Bal’i Da Musibu

 

Ya Allah Yabamu Kariya Daga Dukkan Bal’i.

 

Ya Allah Kabamu Lafiya Da Zaman Lafiya A Jahar Mu Da Kasar Mu Dan Tsarkin Zuciyar Annabi SAW. Amiin Yaa ALLAH

 

26/08/2024

23/02/1445 Hijira

Share

Back to top button