DARASI MAI TAKEN: MUƘAMIN WALIYAI KASHI NA DAYA (1)

MUƘAMIN WALIYAI (1)

 

Al-waliy (الولي) suna ne daga cikin sunayen Allah SWT wanda yake nufin “Mai kulawa ko taimakawa halitta”, kamar yadda Allah da kanshi yake cewa “Allah shine waliyyi (mai taimako) ga wayanda suka yi imani, yana fitar dasu daga duhu zuwa haske. (Baqarah: 257)

 

Su kuwa waliyai ba kowa bane illa wayanda Allah SWT yake cewa “Babu tsoro a garesu kuma ba zasu yi baƙin ciki ba, sune wayanda suka yi imani kuma suka kasance masu taƙawa). (Yunus: 62/63). Dogaro da wannan ayar, zamu gane Allah shine mai taimakon waliyai wato muminai masu taƙawa ba ordinary muminai ba, su kuma waliyai sune masu taimakon sauran halittu.

 

Yayin da Allah yayi nufin bayyanar da Muƙamin Wulaya cikin halitta, sai yace wa mala’iku “zan saukar da khalifa (wakili) na a doron ƙasa” (Baqarah: 30). Wannan khalifan shine shugaban mu Annabi ﷺ. Kamar yadda ya zamo farkon halitta kuma sanadin samuwar sauran halittu baki ɗaya amma a zahiri ya bayyana cikin su a tsakiya ko kusa da ƙarshen zamani, Haka ya kasance khalifan Allah a muhalli madaukaki, kafin daga baya Allah ya saukar da hasken khalifancin sa cikin Annabi Adamu A.S, ƙarni zuwa ƙarni har zuwa ga Sayyidina Abdullahi A.S.

 

A ƙarƙashin wannan muƙamin na khalifa akwai mataimaka, kamar yadda Allah yake cewa “kuma sai muka sanya khalifofi a cikin ku” (Namli: 62), Khalifofin nan sune dukkan Annabawa da Manzanni (Allah ya kara musu yarda), da wasu daga cikin zaɓaɓɓun bayin Allah salihai, misali khidir A.S, ba Annabi bane balle ya zama manzo, kawai salihi ne.

 

Annabi ﷺ shine khalifan Allah, sauran waliyai khalifofin Annabi ﷺ ne, muƙamin su ya rabu kashi tara kamar haka:

 

1. Gausu

2. Imãmãni

3. Autãdu

4. Budalã’u

5. Rajibiyyun

6. Nujabã’u

7. Nuƙabã’u.

8. Akh-yãru

9. Auliyã’u

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button