Malaman Tijjaniyya Sune Ma’abota SUNNAH Na Gaskiya.

AZO A FAHIMCI MECECE “SUNNAH” WAJEN “AMBASADODIN SUNNAH” NA GASKIYA.

 

Ba’a taba kafa wani allon gefen hanya, ba tare da manufar nuni zuwa ga ainashin inda ake so matafiyi yaje ba, haka zalika ba’a ruwaici “Sunnonin MANZON ALLAH (S.A.W)” a litattafai kawai dan ake karanta su da fatar baki, wasu su kebanci kawunansu da wannan suna “Ahli-Sunnah ba” a lokacin da halaye da dabi’unsu ke zama kishiyoyi ga halaye da dabi’un Fiyayyen Halitta (Sallallahu Alaihi Wassallam) ta kowacce kusurwa.

 

Da kazo kake cewa da kanka “AHLI SUNNAH” ka ke cewa da mu “YAN BIDI’A” shin menene cikin dabi’unka da idan mukai duba zuwa gareshi zai zame mana addreshi zuwa ga wani hadisi cikin hadisan MANZON ALLAH (S.A.W) dake wassafa halaye da dabi’unsa…?

 

Shin kana shigar da farin ciki a zukatan abokan mu’amala, shin kana nesantar cutar da kowa da harshe da kuma hannayenka, shin idan aka baka amana kana kiyayewa, shin zantukanka da kakeyi gaskiya kake fadi akan masoyi da makiyi, shin kana gusar da damuwoyin al’umma gwargwadon iyawarka da sauransu, shin kana sassautawa da afuwa ga wadanda suka saba maka, shin kana fifita maslahar al’umma akan taka, shin kana kyautar da duk abinda yazo gareka, shin kana tausayawa raunana da mabukata da sauransu?

 

Sunnah ba wani Bajo bane da ake rejistarsa ta din-din a wani ofishi, da idan ka mannata shikenan ko yaya aikin ka ya gurbata zaka ci gaba da amsa sunanta, sunnah aiki ne, sunnah dabi’ane, sunnah mu’amalane, sunnah kyautatawane, sunnah soyayyane, sunnah gyarawane, sunnah hadin kai ne, sunnah shiryarwane, sunnah Ilmine sunnah…….!

 

Ina ma za ku aboci zama da ambasadodin sunnah na gaskiya irinsu Maulana Prof. Ibrahim Maqari (H) anan ne zaku kyautata fahimtarta ga barin fahimta ta yaudarar kai da kai domin abinda aka karanta ba’a fatar baki kadai yake tsayawa ba, face sai an kyautata aiki da shi a ga66ai. ALLAH YA GANAR.

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua.

Back to top button