Za Ka Iya Yin Komai Don Mauludi Matukar Ba Sabon Allah Ba Ne ???

Za Ka Iya Yin Komai Don Mauludi Matukar Ba Sabon Allah Ba Ne

 

— Sheikh Dr. Yusuf Ali

December 17, 2017, 10:3064

 

 

 

 

TAMBAYA:

Akrimukallah, wanne kira za a yi wa matasa kan maulidi?

 

AMSA:

Abinda malamai su ke cewa shi ne duk wani abu da za ka yi game da murna da haihuwar Manzon Allah (SAW) in dai bai sabawa addinin Muslunci ba kamar ya zama na cewa wasu maganganu ne na batsa ko kuma wasu maganganu ne da ba su da dangantaka da addinin Muslunci ko kuma a samu gwamutsuwa da cudanya tsakanin maza da mata ko kuma za a yi wasu abubuwa na sha kamar shaye-shaye ko wasu abubuwa na munkari in dai ba wadannan za a yi ba to ana so a yi Mauludi. Maulud ya zama mustahabbi ne duk abinda malamai su ka bayyana.

 

Ko a yanzu babu wani malami da zai budi baki ya ce mauludi ba kyau sai dai ya ce a na yin wasu abubuwa da bai dace ba wannan kuwa ko a musabakar Kur’ani koma a hailala ne abin da bai dace ba bai dace ba. Misali idan ka ce a Musulunci akwai mashaya akwai mazinata sai kuma ka ce a daina Musuluncin? In kai haka baka yi wa muslunci da Musulmin kwarai adalci ba. Sai dai a ce a gyara.

 

Mutane a gidajensu suna murnar zagayowar ranar haihuwar ‘ya’yansu ba kuwa ma da an tabbatar da salihancin dan ba bayan ya girma hatta aure in shekarar da aka yi shi ta zagayo sai a taru a yi murna. A majalisar dinkin duniya suna ware ranaku da ake tunawa ko a tunasar a ciki misali ranar mata ta duniya ranar ma’aikata ko a shekaran jiya an yi ranar masu ciwon Kanjamau . Wadanda ke cewa mauludi ba kyau wasu mutane ne da suke da wata manufa ta a sansu wanda in ba sun ware ba a za a san da su ba.

 

Matasa ya kamata su lura da irin duk wadannan abubuwa musamman a soshiyal midiya inda kowa Malam ne babu hujja babu komai mutum ya kafirta mutane inda in bayan maulidin ba za ka iya kama su a wani abin ba kamar sallah ko azimi ko zakka ko a karatun kur’ani ko a aure ko yadda suke kasuwanci ko mu’amalarsu ko iliminsu da sauransu in haka ne sai ka yi adalci tunda shi maulidin ba ka san shi ba amma ka san wadancan dai-dai suke sai ka sallama ko ka yi shuru. Matasa ya kamaa su sani Allah subhanahu wata’ala yana fada a suratu Yunus “Ka ce da Falalar Allah da rahmarsa da shi za su yi farin ciki ya fi duk abin da su ka tara”.

 

Falalar Allah an ce Kur’ani Rahmarsa shi ne Manzo Sallallahu alaihi wassalama. Abinda mu ke so matasa su sani kar ya zamana tunda an ce mauludi son Annabi ne to a yi shi ta kowacce siga ba, a’a a tsaya a binda ake cewa Hudud, wato iyaka ta shari’a don kuwa idan ka shigar da wani abu da ba na shari’a ba za a yi ma hisabi a binda ka shigar.

 

Haka Danfodiyo ya fada haka Ibn Hajj Al-Madkhal ya fada.Wadannan sun ce indai mauludi ba wani abu na keta shari’a to ya halatta . Malamai sun yi wallafe-wallafe inda suke cewa duk inda aka yi mauludin Annabi Allah zai raba wannan wajen da annoba da duk wani abu na ka-ka-ni-ka-yi da duk wani abu da yake ba na farin ciki ba kuma Allah zai yalwata su. Mai yin mauludi yana baiyana son Annabi ne kuma Allah subhanahu wata’ala a suratu dhuha y ace “ Idan Allah ya yi maka wata baiwa ka bayyanawa mutane” wannan ba riya ba ne ba yanda za a yi ka bayyana in ba ta haka ba. Ba yanda za a yi kana son abu ka iya boyewa.

 

Misali, ko da budurwa ka yi za ka fadawa abokinka ko wani na kusa in har kana sonta ba za ka iya daurewa ba, kuma da zai fadi wani abu na kushe kanta ta ba za ka ji dadi ba. Don haka ya na daga hanya ta nuna son Annabi shi ne ranar da aka haife shi ko watan da a ka haife shi ko kai kadai ne ko kai da abokanka ko da iyalanka ko ‘yan’uwanka ku hadu ku nuna soyayyarku gare shi. Annabi Muhammad SAW yace “ Ba wanda yai imani sai wanda ya zama yana sonsa fiye da iyayensa fiye da ‘ya’yansa fiye da dukiyarsa fiye da ransa tukunna.”

 

Kenan Annabi (SAW) bai kebe wata hanya da za a nuna kaunarsa ba ko za nuna farin ciki da samuwarsa ba. Ya ragewa kowa ya yi tunaninsa sai dai kada ya kauce wa shari’a. In har ba ka yi murna da haihuwar Annabi ba to gaba za ka yi ko bakin ciki ? dole in kana sonsa ba ka kinsa in kana kinsa ba ka son sa saboda fadin Allah subhanahu Wata’ala y ace “ Bai sanya wa mutum zuciya biyu ba a cikinsa ba.”

 

 

 

Wanne darasi mauludi ke koyarwa?

 

Abubuwan da a ke fada kyawawan halayen Annabi (SAW) shi ne babban darasin da a ke so a dauka a mauludi bayan soyayyar kanta da ake nunawa ana ambaton Hakuri inda ake kawo wa daga tarihinsa yadda ya sha wahala wajen kira amma ya yi hakuri. Annabi (SAW) ya na kallo gumaka a ke bautawa 360, amma bai ce zai yi fito-na-fito ba da mutane har sai da ya sami dama, ko da ya sami damar ma ya shiga Makka rushe su kawai ya yi kuma yace duk ku tafi an sake ku.

 

Annabin da yake da yafiya irin wannan shi ake cewa a yi koyi da shi . Annabin da ya kasance babu wanda ya kai shi kykkyawar mu’amala a tsakaninsa da Allah babu wanda ya kai shi kyakkyawar mu’amala a zamantakewar iyali in dai har ya zama akwai wanda ake ba wa wani kambun girmamawa a duduniya to kuwa Annabi Muhammad shi ya cancanta. In har akwai wanda za a girmama a fadi halinsa don a yi koyi da shi to Annabi Muhammad (SAW).

 

Annabin da ya kawo shiriya gaba ki daya a duniya wanda duk halinsa na kirki ne wanda duk duniya an hadu da musulmin da kafiran in dai a kyan hali ne an yarda ba wanda ya fi shi. Kowanne aiki na alkahiri ba wanda Annabi Muhammad (SAW) bai yi ba ko bai umarni da shi ba. Darussan su na da yawa sai dai mu ce, kulli aamin wa antum bi khairin.

Share

Back to top button