ALBARKAR GASHIN MA’AIKI (SAWW)
Tsira da Amincin Allah su Qara tabbata abisa mafi tsantsar Kyawun halittu baki-daya.
Kamar yadda muka fada achan baya, Manzon Allah (saww) Allah yayishi bisa mafi cikar kyawun zubin halitta.
Duk da cewa ya rayu har tsawon Shekaru 63 a duniya, amma Gashinsa baqi wuluk yake. Gaba daya furfurar da take kansa bata wuce guda 17 ba.
A lokacin Hajjinsa na Qarshe, Manzon Allah (saww) ya sanya wani Wanzami yayi masa aski, Sai ya tattara wannan gashin Sannan ya kira Wani daga cikin manyan Sahabbansa wanda ake kira “ABU-TAL’HA” ya bashi kaso daya ya rabawa Sahabbansa Maza, sannan ya ware wasu kaso biyu kuma ya ba wa Ummu-Sulaym yace mata ta raba ma ‘Yan uwanta Mata.
(aduba Sahihul-bukhary, juzu’i na 4 shafi na 33).
Imam Ibnu Hajar Al-askalany (ra) acikin sharhin da yayiwa Sahihul-bukhary, da yazo kan wannan hadisin sai yace Wannan rarraba gashin da Manzon Allah (saww) yasa akayi, shine babbar hujjar da take tabbatar mana da halarcin neman Albarkar gashin Manzon Allah (saww).
Imamu Ahmad ya ruwaito cewar Idan ana yiwa Manzon Allah (saww) aski, Sahabbansa sukan zo su kewayeshi. Basu barin koda kwaya daya na silin gashinsa ya fa’di akasa.
Da zarar ya zubo zasu chafkeshi da hannayensu.
(aduba Musnad juzu’i na 4, shafi na 324, da kuma Sahihu Muslim Juzu’i na 2 shafi na 256).
Anas bn Malik (ra) ya ruwaito cewar wata rana A mina (Wajen aikin Hajji) anyi wa Manzon Allah (saww) aski, sai ya raba gashin nasa kaso biyu.
Ya ba ma Abu-Tal’ha rabi, Sannan kuma ya raba daya kason atsakanin Sauran Sahabbansa.
Sayyiduna Khalid bn Walid (ra) ya nemi alfarma awajen Sayyiduna Abu-Tal’ha cewar acikin wannan gashin, ya bashi na WAJEN GOSHIN MANZON ALLAH (SAWW).
Da Abu Tal’ha din ya bashi, sai ya kasance yana ‘dora wannan gashin akan idanuwansa sannan yana sumbantarshi .
Daga nan sai Khalid din ya sanya wannan gashin acikin hularsa ta Yaki. Duk lokacin da zai tafi fagen fama, sai ya dauko wannan hula ya sanyata sannan ya rufe da Sulkensa. Saboda haka duk yadda ya tunkari abokan gaba sai yayi nasa akansu. ALBARKACIN GASHIN GOSHIN ANNABI (SAWW).
(Imamul-Wakidi ya ruwaitoshi acikin Maghazy, da Kuma Ibnu Hajar acikin Al-Isabah).
Ita kuwa Sayyidah Ummu Sulaym (ra) ajiyewa nata rabon tayi. Ta adanashi.. Ta nemo wata kwalbar Azurfa ta sanya wannan gashin Aciki.
Duk lokacin da wani mutum bashi da lafiya, ko zazzabi ko ciwon ciki ko maita, ko kambun baka, Sai akawo ruwa gidan Ummu Sulaym. Da zarar ta tsoma wannan gashin aciki, indai mutum yasha, nan da nan sai lafiya ta samu.
* Shi kuwa Thabitul-Bunany (Almajirin Anas bn Malik) ya ruwaito mana cewa:
“Alokacin da Sayyiduna Anas bn Malik yake kwance zai rasu, sai ya dauko wani silin Gashi ya nuna min, Sannan yace:
“WANNAN DAYA NE DAGA CIKIN SILIN GASHIN MANZON ALLAH (SAWW). IDAN NA RASU, KA SANYA MIN SHI AQARKASHIN HARSHE NA”
Saboda haka bayan ya rasu sai na sanya masa shi akarkashin harshensa aka binne shi dashi”.
(aduba Sunanus-Sihah na Imam Ibnus-Sakan)
Imamul-Bukhary da Imam Ahmad bn Hanbal da Imamul-Baihaqy duk sun ruwaito daga Babban Tabi’in nan mai suna IBNU SEERIN (rah) yana cewa:
“WALLAHI KWAYA DAYA DAGA SILIN GASHIN MANZON ALLAH (SAWW) SHI NAFI SON IN MALLAKA FIYE DA ZINARE DA AZURFA. KUMA SHINE YAFI ALKHAIRI FIYE DA DUNIYA DA DUKKAN ABINDA YAKE CIKINTA.”.
Shima Sayyiduna Abeedah (ra) yace “WALLAHI KWAYA DAYA DAGA GASHIN MANZON ALLAH (SAWW) SHI YAFI SOYUWA AGARENI FIYE DA DUNIYA DA DUKKAN ARZIKIN DA YAKE CIKINTA”
Shi kuwa SAYYIDUNA MU’AWIYAH (RA) an ruwaito cewar ya bar wasiyya cewar Idan ya rasu, asanya Gashi da kuma faratan Manzon Allah (saww) akan Goshinsa da idanuwansa da Makogoronsa kafin asanya shi acikin Makara akaishi kabarinsa.
To jama’a kunji yadda Sahabbai da Magabata na kwarai sukd neman albarka daga Gashin Kan Ma’aiki (saww) mai daraja. Don haka duk mai da’awar bin tafarkin Magabata in dai da gaske yake yi, to dole ya tashi tsaye ya nemi albarkar Ma’aiki (saww).
Kuma wannan ya tabbatar mana da cewa su Sahabbai awajensu Annabi Muhammadu (saw) ba mutum ne kamar irin kowa da kowa ba. Don haka suke gigicewa akan Silin gashinsa ma ka’dai.