Sheikh Muhammadul Al-Hāfiz Ibn Abdullatīf Ibn Sālim Al-Tijjani, Daya Yake Tamkar Dubu.

Daga cikin manyan malaman mu akwai ɗaya tamkar dubu yana daga cikin tsofaffin Shehunan ɗariƙar Tijjaniyya, salihi ne matuƙa kuma babban malamin Hadisi, ne mai bai wa masu ilimi mamaki. Shi ne Sheikh Muhammadul al-Hāfiz Ibn Abdullatīf Ibn Sālim al-Tijjani.

 

Yana daya daga cikin mu mafiya masana hadisin a tarihi ƙasar Misra, ya kasance mafi ilimi a cikin cikakkun masana ilimin Hadisi, gwani ne matuƙa kuma mai zurfin fahimta ta tantance maruwaita, hadisi da kuma fito da kurakuran da ke cikin hadisi…

 

Babban Limamin kuma Shehun Azhar, Sheikh Abdul-Halīm Mahmud, an tambaye shi ko wane ra’ayin malamin hadisi kafi kafa hujja da sukar sa dangane da sarkakkun riwayoyi ko ingantattu/raunana ruwayoyi, ya kasance yana cewa: ‘Sayyid Abdulllah bin Siddiq al- Ghumāri da Sheikh Muhammadul al-Hāfiz al -Tijani.’

 

Allah ya jaddada masa rahama, misali ne na manya-manyan malaman Masar, kuma duk wanda ya kasance a kan tafarkinsa na ruhi irin nasa, to yana kan tafarki ingantacce, mai matuƙar kyau kuma karbabbe.

 

~Sheikh Ali Gomaa, tsohon babban Mufti na ƙasar Masar, .

Share

Back to top button