NASIHA

  • ZINA Tana Cikin Manyan Laifuffuka A Addinin Musulunci.

    SHIN KUN SAN ILLOLIN ZINA KUWA???

     

    ZINA Tana Cikin Manyan Laifuffuka,

    Wanda Dukkan Shari’un Da ALLAH

    Ta’ala Ya Saukar Sun Hadu Akan

    Haramcin Zina,

     

    AL-QUR’ANI Mai Girma Da Sunnar

    ANNABI (S.A.W) Da Dukkan Malamai Sun Hadu Akan Haramcin Zina,

     

    Malamai Sun Tabbatar Da Cewa Kofofin Zina Guda Biyar Ne

     

    *1 – Kallo Zuwa Ga Abinda ALLAH Ya Haramta

     

    *2 – Shigar Batsa

     

    *3 – Kalaman Batsa

     

    *4 – Kebancewa Da Matar Da Ba Muharramarka Ba,

     

    *5 – Sha’awa Mai Qarfi Babu Aure

     

    ALLAH(S.W.T) Ya Ce:”Kada Ku Kusanci Zina”

     

    Manzon ALLAH(S.A.W) Ya Ce:”Mai Zina Ba Zai Yi Zina Ba, Yayin Da Yake Zina, Sai An Cire Masa Imani”

     

    Abdulllah Dan Mas’ud(R.A) Ya Ce:”Duk Al’ummar Da Take Zina, Ta Jawowa Kanta Fushin ALLAH, Da Halaka”

     

    Musulunci Yayi Umarni Da Tsare Abubuwa Biyar Kamar Haka: Addini, Dukiya, Rayuka, Hankali, Mutunci, Nasaba, To Amma ZINA Ita Kadai, Tana Rusa Wadannan Duka.

     

    YA ALLAH KA KARE MU DA ZURIYARMU BAKI DAYA DAGA SHARRIN FASADIN ZINA, MASU YI KUMA ALLAH YA SHIRYE SU AMEEN.

  • DOLE MASU ILIMI NE ZASUYI JAGORANCI A ADDINI MUSAMNAN TIJJANIYYA.

    KHALIPHA FATIHU SHEIKH MUHAMMADU GIBRIMA.

     

    DOLE MASU ILIMI NE ZASUYI JAGORANCI A ADDINI MUSAMNAN TIJJANIYYA FAIDAH.

     

    MU TARU MU GAYAWA KAN MU GASKIYA DAN MU GYARA.

     

    Jawabin Maulana Khalifah FATIHUL AGLAQ da ke cikin Recordin ‘DIN.

     

    1. Abubuwan da su ke faruwa ba qaramun damun mu su ke ba – inji Shehu Fatihul Aglaq (RTA).

     

    2. Sai ya ba da misalin abubuwan da suke damun na su kamar haka.

    A. Rataya hoto ana yawo da shi

     

    B. Tara suma ta zamo ita ce abin ado

     

    C. Daukar motoci ana yawon ZIKIRI ba karatu

     

    D. Zaman addu’a da Sallah a Qabarburan Bayin Allah

     

    E. Fifita Shehu Ibrahim RA akan Annabi Muhammadu S.A.W (kowa yasan akan suwa yake ramzi).

     

    F shafe Sallah.

     

    3. Sannan sai ya yi kira ga masu wa’azi Har SAU HU’DU da su dinga yi musu wa’azi saboda abin ya zamo masifa.

     

     

    4. Ya koka matuqa akan abinda ya ke faruwa na waqi’ar Abdul Inyass (L. A), Saboda fifita SHEHU IBRAHIM Inyass (RTA) da ake akan Annabi Muhammadu S.A.W.

     

    5. Ya cigaba da cewa Ko zamanin Shehu Gibrima da Halifa ba su ga ana al’adar TARA Suma da yawon ZIKIRI ba KARATU ba.

     

    7. Ya kara jaddadawa cewa duk fa wani mai daraja ya samu darajarsa ne da Annabi Muhammadu S.A.W.

     

    8. Sannan ya yi magana akan ziyarar RAUDAR BAYIN ALLAH da ake, da kuma abubuwan da ake na rashin kyautatawa.

     

    9. ya ta6a sawa an RUFE WAJEN ZIYARA (RAUDAR SHEHU GIBRIMA) saboda abubuwan da ake na su’ul adabi.

     

    8. Sannan ya jaddada tare da tabbatar da kafircin masu shafe Sallah.

     

    9. Ya qara jaddadawa akan ziyara Fadinsa “Fatiha da d’aya, qulhuwallahu 11, salatul fatihi 10, KURSIYYU 10”, sun isa (Ramzi akan masu tarewa a RAUDOJIN BAYIN ALLAH).

     

    10. Ya nuna haramcin yin sallah A Raudojin Bayin Allah.

     

    Allah ka kare mu ka kare mu zamiya cikin Allah alfarmar shugaba Annabi Muhammadu (saw). Amiin

     

    Daga: Sayyadi Sani Sadi Hassan

  • Sheikh Imam Munir Adam Koza, Baka Fadi Komai Ba Face Gaskiya.

    ALLAH YA SAKA DA ALKAIRI.

     

    Sam-sam babu bukatar turo da kowanne guda daya daga cikin Manzanni zuwa ga al’ummu da suka gabata, da sakonnin da suke fayyace dai-dai da kuskure, gaskiya da karya, shiriya da kuma bata, cikin tsari da dokokin da ubangijin bayi yakeso bayinsa su rayu akai ta hanyar saukar da litattafai mabambanta, idan da ace kowa abinda ya kimtsa a tunaninsa, na ra’ayinsa da kuma sha’awowinsa shine Addini a gareshi.

     

    Amma lallai muddin mun yarda mu Musulmine, kuma munyar da akwai MANZON da aka aikoshi da tsarin rayuwar da ALLAH yakeso mu rayu akai a wannan zamanin, kuma mun aminta mu al’ummarsane kuma mun yarda dukkanin jagororin da muke tutiya dasu basu kasance masu sabawa abinda yazo dashi ba, to bin wannan tsarin rayuwar da MANZO (S.A.W) yazo dashi shine dai-dai kuma shine mafifici karbabbe a wajen ALLAH, duk wani tsarin rayuwa sa6anin wannan lalataccene, gurbataccene, sannan kuma bai kasance abin bi ga wadanda suka kasance suna rayuwa bisa neman dai-daito da dacewa da shiriya ba.

     

    Babu shakka Sheikh Imam Munir Adam Khoza, baka fadi komai ba face gaskiya, kuma lallai komawa zuwa ga abinda magabatan da muke intisabi dasu, shine gaskiyar tafarki na shiriya, sabanin hakan babu inda zai kaimu, face muna tunanin mu mabiyansune masoyansu, amma a hakika mu masu saba musu ne, sannan makiya ga abinda suka dora mu akai.

     

    Lallaine dama wannan abune tabbatacce da ya wanzu a tarihin Duniya, a duk inda gaskiya ta gifto ta motsa to takan nufi inda alkairi ya dosa, kuma a duk inda Alkairi ya wanzu to sharri kan biyoshi a sukwane domin ya kishiyancesa.

     

    FATANMU ALLAH YA TABBATAR DA MAGASKATA AKAN GASKIYARSU, YA SHIRYI MASU HIDIMA GA AKASINTA A DUK INDA SUKE. Alhamdulillah

     

    Daga: Muhammadu Usman Gashua

  • Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi Yayi Muhimman Magagganu A Wurin Maulidi

    Rayuwar Annabi SAW Ta Kasance Abar Koyi Tun Ma Kafin A Saukar Da Wahyi. Inji Gwamnan Jihar Bauchi.

     

    “Tun kafin sauƙar masa da wahayi, rayuwar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta kasance abar kwaikwayo ga ɗaukacin al’uma.

     

    “Juriya, sadaukarwa, zaman lafiya, taimako da neman ilimi na cikin ababen da Manzon Allah ya koyar da sahabban sa masu daraja.

     

    “Waɗannan da ma wasu na cikin kiran da nayi ga ɗaukacin al’umar musulmi da suka yi cincirindo daren jiya a filin wasa na tunawa da marigayi Firaminista Abubakar Tafawa Balewa a nan fadar jiha don taya mu bikin mauludin wannan shekara.

     

    “A yau Lahadi da ake gudanar da zagaye a Bauchi da kewaye, ina kira ga al’uma da su gudanar da wannan biki cikin nutsuwa, lafiya da bin doka da oda alfarmar wanda muke bikin domin sa.

     

    “Kada mu gajiya wajen kwaikwayon halayyen fiyayyen halitta tare da yawaita masa salati don neman sabati, yalwatuwar arziki da zaman lafiya ga jihar Bauchi da ƙasar mu Najeriya.

     

    Allah ka cigaba da shiga lamuran mu alfarmar Annabi Muhammadu ɗan Amina”, cewar Gwamna Bala na jihar Bauchi.

     

    Daga Lawal Mu’azu Bauchi

    Mai taimakawa Gwamna Bala Mohammed

    Kan harkokin Sabbin kafafun sadarwa

  • BABBAN TASHIN HANKALI: Watarana Mala’ika Jibreelu (A.S) yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) a wani lokacin da bai saba zuwa masa ba.

    BABBAN TASHIN HANKALI!!!

     

    Hadisi ne zan karanta muku Amma ina neman alfarma guda awajenku kafin ku karanta Hadisin nan, Alfarmar da nake nema awajenku ita ce, ku tsayar da duk abinda kukeyi, ku nutsu ku karantashi da kyau.

     

    Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani.

     

    BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

    Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Karshe, da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya.

     

    Yazeedur Raqqaashiy ya karbo Hadisin daga Anas bn Malik (R.A) yana cewa: Watarana Mala’ika Jibreelu (A.S) yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba.

     

    Yazo, gaba dayan launin fuskarsa ya canza. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa “MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA CANJA HAKA?”. Yace “Ya Muhammadu (S.A.W) nazo maka ne awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu hura wuta suci gaba da Hura ta.

     

    Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Kabari gaskiya ce, kuma Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamata yayi wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa ya samu tsira daga wannan”.

     

    Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa “YA JUBREELU INA SO KA SIFFANTA MUN YADDA JAHANNAMA TAKE”.

     

    Sai yace “Na’am. Hakika Allah madau kakin Sarki yayin da ya halicci Jahannama, yasa an hurata tsawon Shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA -JAWUR.

     

    Sannan aka sake hurata tsawon Shekaru DUBU har sai da ta zama FARI – FAT!!

    Sannan aka sake hurata tsawon shekaru DUBU har sai da ta zama BAKA – KIRIN!!!.

    Tana nan har yanzu BAKA KIRIN ce, mai

    tsananin duhu ce.Harshen Balbalinta basu mutuwa ballantana Garwashinta.

     

    Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za’a bude misalin kofar allura daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan Ma’abotan doron duniyar nan sun kone baki dayansu saboda tsananin zafinta.

     

    Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za’a ratayo tufafi guda daya tufafin ‘Yan Wutar Jahannama a makaloshi atsakanin Sararin Samaniya, da sai Dukkan Ma’abotan doron kasa sun Mutu baki dayansu saboda tsananin.

     

    Ya Allah ka karemu daga dukkanin azabarka kasa muyi kyaky kyawan karshen Ya Hayyu Ya Qayyum

Back to top button