BABBAR JARABAWA CE A HALICCEKA A NIGERIA (AREWA) ALLAH KABAMU IKON CIN WANNAN JARABAWA.
Daga Barr Aminu Balarabe Isa.
Babu shakka a halicce ka a Nigeria babbar jarabawa ce.
1- A Nigeria ne (Arewa) zakayi alkhairi 99 amma ayi shiru ayi tsit babu mai yi maka adduar alkhairi da karfafarka akai amma daga ranar da kayi kuskure daya tak za kaga anyi caa akan ka kamar a cinye ka.
2- A Nigeria ne (Arewa) za kaga mutum zai sake maka fuska da dariya amma a zuciyar sa haushin ka yake ji kamar ya kashe ka.
3- A Nigeria ne(Arewa) za kaga mutum yana bada labari a kanka yana hakikan cewa akan wani abu akan ka alhali bai taba ganin ka ba ko kuma bai taba wata hulda da kai ba kawai labari shima yaji akan ka.
4- A Nigeria ne (Arewa) duk mai kudi barawo ne azzalumi ne, amma duk talaka marar ko sisi bawan Allah ne salihi mutumin kirki.
5- A Nigeria ne(Arewa) kowa malami ne mai bada fatawa ne.
6- A Nigeria ne(Arewa) Duk malami talaka shine malamin Allah, amma malami mai rufin asiri ba malamin Allah bane malamin Gomnati ne mai ci da Addini ne.
7- A Nigeria ne (Arewa) ba zaka taba jin an fadi alkhairin Shugaba ba sai bayan ya mutu.
8- A Nigeria ne (Arewa) Zaka ga Limami na jin haushin mamu, mamu na jin haushin Liman.
9- A Nigeria ne (Arewa) za kaga talaka yana tsine wa Shugaban sa wai saboda zalunci amma da Shugaban ya bashi kudi ya rabawa yan uwan sa talakawa sai ya cinye ya danne ya hana su.
10- A Nigeria ne (Arewa) masoyinka shine adali amma abokin adawar ka kuwa duk kirkin sa mugu ne azzalumi ne.
11- A Nigeria ne (Arewa) Zaka ga mutum yana da tarin bukatu sai ya kwana yana barci ya kasa tashi ya fadawa Allah cikin dare amma da safe sai ya je ya fadawa mutum dan uwan sa damuwar sa.
12- A Nigeria ne (Arewa) zaka taimaki mutum daga Allah ya daga shi to yanzu bashi da babban abokin ga ba sai kai.
13- A Nigeria ne (Arewa) kyakkyawan zato yayi karanci amma mummuna kam hmmm sai abin da ya karu.
14- A Nigeria ne (Arewa) yau mutum har ya rasa Wanda zai dauka a matsayin Amini ko masoyi babban aboki saboda ba ka da tabbas akan sirrinka.
15- A Nigeria ne (Arewa) mutum zai ga kayi kuskure ya kasa maka fada ko nasiha amma sai ya fara ya madidi da kai wai kuma abokin ka ne.
16- A Nigeria ne (Arewa) duk lokacin da ka yabi wani Shugaba ko wani mai mulki shi kenan zaka ji ana cewa maula yake aa Neman na miya yake.
Subhanallah.
Inna Lillahi Wa inna ilaihi rajiuun.
Laa Haula wala Quwwata Illa billah.
Allah Ubangiji ka bamu ikon cin wannan jarabawa da kayi mana. Albarkan annabi SAW.