MAS’ALAR WAHABIYA SUKA GAZA GANEWA GAME DA MAS’ALAR “TAUSAYI” A LAMARIN ALLAH.

AN FAYYACE MAS’ALAR DA MALAMAN WAHABIYA SUKA GAZA GANEWA GAME DA MAS’ALAR “TAUSAYI” A LAMARIN ALLAH.

 

Daga: Muhammad Usman Gashua

 

Tun bayan fitowar wannan zance mimbaran wa’azin wasu daga Malamai su kai bakuncin Maudu’in tattaunawa na raddi da sauran dangoginsa.

 

Amma ga wadanda suka kasance masu idanu da kwalli, sun san me Sheikh Nazifi Alkarmawy ike nufi, domin wannan siffa ta rashin tausayi “Insaniyya” kamalace ga ALLAH domin tausayi a fuskar hukunci na daga rauni daga dabi’a ta halitta, face siffa ta ALLAH gusar da abinda tausayi bai iya gusarwa wato jinkai da kuma rahama dake shiryarwa zuwa ga sakamako mai kyau ga bayi ko , Horo da Azaba a fannin Adalcinsa Adalcinsa dake shiryarwa zuwa ga hukunci na jalala.

 

ALLAH NA DA SIFFOFI NA:

 

1- Siffa ta Jamala da ke isarwa zuwa ga gafara, jin kai, amfanarwa da kuma jibancin bayi a wannan fuska ALLAH na da sunaye kamar:- Arrahmanu, Arrahimu, Algaffaru, Arraziqu da sauransu.

 

2- Siffa ta Jalala da ke isarwa zuwa ga hukunci, da kuma martani ga bayi ko wata jarabawa mai taba zuciya kamar sunan sa Al-Muntaqim, Al-mumitu, Ad-Dhar da sauransu.

 

• Tausayin irin na bayi cike ike da rauni wanda zai haifar da matsala ga abin tausayawa ta fuskar hukunci, hakan kuma abin korewa ne ga ALLAH.

 

• ALLAH kuma tsarkakke ne ga duk wani rauni da zai haifar da gajiyawa wajen gusar da abinda yake na matsala ga bawa, cikin gafara da jinkansa, ko cikin hukunci da horo ko kuma domin jarabawa ga bayi.

 

BARA MU WARWARE ABIN A SAUKAKE.

 

1- Mutum ne Dansa ya samu karaya a kafa, sai ya zamto da an taba wajen sai yaro ya kurma ihu, shin kana ganin iyayen wannan yaro zasu iya daure wannan karaya da wannan yaro ya samu a kafafunsa?

 

Kaga ba zasu iya ba, wajibinsu su dauke shi su kai shi wajen likita mai dori, a yayin da shi kuma zai ta matsa wannan ciwo wannan yaro na kuka da kururuwa, iyayensa ma na zubda kwalla.

 

Abin lura anan, shin idan saboda tausayin da iyayen wannan yaro suke ma dansu dalilin halin da ya tsinci kansa ciki, yasa suka ki kai shi wajen gyara shin baka ganin wannan tausayin na su zai zama silar cutarwar ga shi yaron, domin kafar yaron zata lalace karshe ta shafi lafiyarsa baki daya, har ma zai iya rasa rayuwarsa, to yaya abin zai kasance idan madorin yaron shi ma ya kasance yana tausayin yaron irin siffar tausayin iyayensa kaga kenan dai tausayinsa da tausayin iyayen zasu taru su cutar da yaron, amma sai shi madori ya zamo mai kokarin son gusar da ciwo da damuwar da yaron ya samu ta hanyar gyara da koruwar tausayi irin na iyayen yaron ga Dan Nasu.

 

To haka zalika shi ALLAH ya kan gusarwa bawa abu da zai haifar masa da matsala, ko da ta hanyar gusarwar zukatan wasu zasu sosu.

 

2- A irin namu dabi’ar, duk uba shi ke da mas’uliyar ciyar da ‘ya’yansa, sai kaga mutum ya tara yara kanana sama da 20 kullum sai ya fita zai samo abinda za su ci, shi ne cinsu, kuma shi ne shansu, lokaci guda sai kaga ALLAH ya karbe shi, sai kaga mutane dangi da yan uwa na kuka saboda tausayin halin da yaran zasu shiga, a yayin da shi kuma mai yiwuwa yana halin farin ciki saboda abinda ya riska na rahamar ALLAH, a gefe guda kuma ALLAH ya tsara wata hanyar da zai ciyar da yaran da su mutane basu san da ita ba, to kaga anan dole a korewa ALLAH siffar tausayi irin wannan na bayi, a kusanto da siffarsa ta Al-warisu, Al-Wali da sauransu.

 

TAUSAYI A CIKIN BAYI SIFFACE TA KAMALA TA FUSKAR TAIAMAKO TSAKANINSU, TA KAN ZAMA TAWAYA IDAN BA’A AJE TA AN AIKATA ABINDA YA DACE BA KAMAR DAI HIKAYAR MARAS LAFIYA, LIKITA DA MASU JINYA, HAKA ZALIKA JINKAI, GAFARA DA RAHAMA SIFFOFIN DAUKAKA NE GA ALLAH, DA HANYAR AIWATAR DA SU TSAKANIN BAYINSA SIFFAR TAUSAYI IRIN NA BAYI KE KORUWA GARESHI, A GEFE GUDA KUMA ALLAH NA DA SIFFOFI NA JALALA DA YAKE HORO KO AZABA DA SU GA BAYIN DA SUKA RAYU CIKIN ZALINCI

 

WALILLAHI MASALUL A’ALA, WALLAHU A’ALAM.

 

ALLAH YA HASKAKA MANA ZUKATA DA FAHIMTAR ADDININSA YA TSARE TSUKE FAHIMTA. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button