RASUWA

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un, Allah Ya Yiwa Masoyin Manzon Allah SAW Rasuwa Nura Mustapha.

    INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

     

    Allah yayi wa Nura Mustapha Waye cikkaken masoyin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama (Director IZZAR SO Series) rasuwa.

     

    Anyi Jana’izar sa da karfe 11 A Gidansa dake Goron Dutse Primary dake jihar Kano.

     

    Nura Mustapha yayi amfani da Film ɗin sa na Izzar so wajan haskawa duniya matsayin riƙon amana da kuma muhimmancin tsayawa akan gaskiya da uwa uba soyayyar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) wanda abana ma har Maulidin Annabi SAW sukai cikin shirin.

     

    Muna Addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa kura-kuransa, Allah yasa Aljanna ce makomarsa. Idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani. Amiin

Back to top button