Ɗalibin Sheikh Dahiru Bauchi Yayi Fice A Fannonin Ilimin Addini Da Zamani A Duniya.

Ɗalibin Sheikh Dahiru Bauchi Yayi Fice A Fannonin Ilimin Addini Da Zamani A Duniya

 

Sheikh Ferfesa Muhammad Kabir Yusuf (Hamdani) daya daga cikin matasan Tijjaniyya kuma almajirin Sheikh Ibrahim Inyass dalibin Sheikh Dahiru Bauchi (RA) wanda yayi fice a bangarorin mabanbanta a duniyar ilmin addinin Musulunci dana zamani a kasashen waje. Ya samu lambobin girmamawa daga kasashen waje da gida Najeriya.

 

Farfesa Hamdani haifaffen garin Kano mazaunin birnin Abuja yana karantarwa a jami’a dake birnin tarayya Abuja, Malamin ya kasance marubuci na musamman wacce Allah ya kebance shi dashi da baiwa da kuma jarumta marubuci a fannoni da dama kamar Tafsiri, Hadisi, Nahwu, Fiqhu, bangaren Boko kuma yayi rubuce-rubuce a fannonin Computer science, Engineering, Cyber Security da sauran su.

 

Shehin malamin masanin ilmin Tafsirin Alkur’ani, Hadisi, Nahwu, Fiqhu, Balaga, Sarf, da sauran fannoni na ilmi addinin Musulunci. Malami ne a kasashen waje kamar Malaysia, Ethiopia, America, Canada, Egypt da sauran su.

 

Farfesa Hamdani shine sakataren kungiyar hadin-kan sufaye ta Najeriya wanda Sheikh Sharif Ibrahim Saleh yake shugabanta a kasa. Kuma shugaban kungiyar Fityanu Initiative ta kasa.

 

Muna addu’an Allah ya saka wa Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA da maficicin alkhairi, ya kara masa lafiya da nisan kwana.

 

Allah ya kara wa Farfesa Muhammad Kabir Yusuf Hamdani lafiya da nisan kwana ya kara himma da daukaka da juriya wurin hidimtawa addinin Musulunci da Tijjaniyya. Amiin

 

Babangida Alhaji Maina

Founder Tijjaniyya Media News.

Back to top button