A Musulunci Ba Wani Littafin Daya Kai Qur’ani A Matsayi Da Falala Kasancewar Ya Sauka Ga Mafifincin Annabi SAW Ga Mafificiyar Al’umma.

DAGA TASKAR AL-QUR’AN ZUWA GA MUMINAI

 

A Musulunci ba Wani Littafin daya Kai Qur’ani a matsayi da Falala Kasancewar ya Sauka ga mafifincin Annabi saw ga mafificiyar Al Umma.

 

Don haka ne, aka wajabta Imani dashi da karanta shi da aiki da shi da karantar dashi tareda kiyaye Alfarmarsa data mahaddatansa.

 

Qur’ani da Hadisai da yawa sun kwadaitar kan Yawaita Karatun Qur’ani: “Ku karanta abin da ya sauwaka daga Qur’an ” (Muzammil 4).

 

“Wanda ya karanta harafi 1 a Qur’an zai samu ladar 10, a Kowane Harafi, ba Ina nufin Alif Lam Mim ba, Alif Harafi Lam Harafi, Mim Harafi.”

Tirmiziy, Alhakim da ga Ibn Mas’ud RA.

 

“Mafi Alherin Ku, Wanda ya koyi Qur’an Kuma ya ke koyar dashi”(Bukhari, Muslim, Abu Daud, Nisa’i, Ibn Majah, daga Usaman bn Affan RA)”

 

“Wanda karanta Qur’ani da ZIKIRI ya shagaltar dashi daga rokonNa zan Bashi fiye da abin da nake baiwa Masu rokoNa. Kuma fifikon Zancen Allah akan sauran Zantuka kamar fifikon Allah akan halittarSa (Hadisil Qudsi) Tirmiy daga Abi Saidin Alkhdry RA

 

A Wani Hadisin Annabi saww cewa yayi: “Idan bawa ya yi khatamar Qur’ani (Ya karanta ya Sauka) Mala’iku Dubu 60, zasu yi masa Salati, a lokacin Khatmar sa (Dailami…..Amr bn Shuaib)

 

Wannan ana Magana ne, akan Wanda zai iya Karamtawa tun daga farko Qur’ani har karshen, amma nasani akwai Musulmi da yawa da bazasu iya karanta Qur’ani gaba dayansa ba.

 

Irin Wadannan Mutane kenan Wannan Falalar ta KUBCE Masu, ko kuwa? Idan bata KUBCE Masu ba kuwa, ta Yaya zasu amfana? Wannan shi ne abin da zanyi Magana akai a Rubutu na gaba insha Allah. FALALAR ALLAH DA YAWA

 

Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau 20/0/22. 19/12/1443@H

Back to top button