ALLAH ka yi Mana don Son ANNABI Wannan shi ne Shari’a ta Yarda da shi, in Ba’a Gane ba, a Tuntubi Malaman Sunna.

WARWARE ZARE DA ABAWA;

 

Bello Ali Abdullahi Mashema Yana Cewa;

 

“ALLAH ka yi mana don Son ANNABI wannan shi ne Shari’a ta yarda da shi, in ba’a gane ba, a tuntubi malaman sunna”

 

*. AMSA; Wasu Daga Bani-Ƙungiya (Irinsu; Bello Ali Abdullahi Mashema); Sun Yarda Za’a Iya Roƙon ALLAH Yayi Don ANNABI(S.A.W), Amma Mutum ‘Dan’uwanka Sai Dai WAI KA CE MASA DON SON ANNABI(S.A.W) To…!

 

Ba Mu Hana Ku Riƙe Fahimtarku Ba, ‘Kila Kuna Da Hujja. Amma Ga Ta Mu Hujjar:

 

Ya Inganta Cewa; Ibadunmu Za Su Gajiya Ranar Alƙiyama a Wurin Ceto, Har Sai ANNABI MUHAMMAD(S.A.W) Ya Sanya Baki. Hakan Yasa Muka Gamsu Da Cewa; ANNABIN(S.A.W) YAFI IBADA GIRMA A WURIN ALLAH(S.W.T), To Shi SON ANNABIN(S.A.W) Da Kuka Yarda Ayi Don Shi, Shima Nau’in Ibada Ne, a Fahimtarmu.

 

Don Haka ANNABIN(S.A.W) Yafi Soyayyar Tasa a Wurinmu. In Dai Bawa Zai Roƙi Bawa Yayi Don WATA IBADA TASA KAMAR SOYAYYA, To Yafi Cancanta Ayi Don Wanda Yafi Ibadar – WATAU ANNABI MUHAMMADU(S.A.W).

 

Bahaushe Kansa Ya Kan Ce;”ANA BARIN HALAL KO DON KUNYA”. Don Haka In Yanzu Wani Zai Zo Ya Ce Ka Yi Masa Wata Alfarma Don Mahaifanka Zaka Yi. Yin Hakan Bai Zama Shirka Ko Riya, Don Musulmin ‘Kwarai Yana Ganin Girman Iyaye Cikin Girman ALLAH, Yana Son Su Cikin Soyayyar ALLAH.

 

Don Haka Yin Wani Abu Don Nuna Isarsu a Wurinka Kamar Amsa ‘Kiran ALLAH Ne Mai Cewa:

 

…….لا تقل لهما اف ولا تنهرهما، وقل لهما قولا كريما…….

 

In Dai Kyakkyawan Zance Zai Sanya Iyayen Mutum Farin Ciki Da Shi, To ‘Karara Yake Nuna Masu Sun Isa Da Kai, Zai Sanya Su Fiye Da Haka.

 

Ya Zo a Ruwayoyi Barkatai Cewa; Sahabbai Su Kan Ce;”Bi Abi Anta Wa Ummeey Ya RASULALLAHI(S.A.W)”, WATO; IYAƳENSU DA SU FANSA NE GA ANNABI(S.A.W), Ma’ana; Sun Bayar Saboda ANNABI(S.A.W).

 

Malam Bello Sai Ka Bari Sai Ranar ‘Kiyama Yayin Da Ibadun Suka Kasa Sai Ka Je Ayi Maka Don Wata Ibadar MU MUN TSAYA GA ANNABIN(S.A.W).

 

ALLAH Ya ‘Kara Tsare Mana Imaninmu, Ya ‘Kara Mana Ganin Girma Da Qadarin ANNABINMU(S.A.W) Ameeen.

 

Daga: Othman Muhammad.

Back to top button