RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA KASHI NA HUDU (4).

RAYUWAR ANNABI S.A.W KAFIN WATAN AZUMIN RAMALANA Part (4) DAGA TASKAR UMAR CHOBBE).

 

1.5 BAYANI AKAN TABBATAR DA KAMAWA WATA:

 

A Zamanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama baya soma Azumin Ramalana ba, face ya tabbatar da kamawar watan, ta hanyar samun shedar wani mutum daya da ya ga watan da qwayar idonsa, ko tabbatar da watan Sha’abana ya cika kwana talatin.

 

Wadannan hanyoyi biyu na tabbatar da kamawar Watan Azumi, na daga cikin martabobin da wannan addini ya kebanta da su, kuma wadanda suka lamunce masa dacewa da kowane zamani da kowane wuri, saboda komai nasa a fili yake, ta yadda gaba dayan mutane na iya zama sheda a kai.

 

Daga cikin Hadissan da ke tabbatar da dogarar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi a kan tabbatar tsayuwar watan Azumi, a kan ganin qwayar ido akwai:

 

Hadisin dan Umar Raliyallahu Anhu wanda ya ce: “Mutane sun sa ido ga neman ganin jinjirin watan Azumi, sai na gayawa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa tabbas ni na gane shi.

 

Sai kuwa ya kama Azumi, ya kuma umurci mutane da su kama.”

 

Sai kuma Hadisin dan Abbas Raliyallahu Anhuma wanda ya ce: “Wani Balaraben qauye ya zo wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yace: “Tabbas ni na ga jinjirin watan Azumi.”

 

Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa: “Ko ka yi imani da babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah? ” .

 

Shi kuwa ya karba masa da cewa: “Eh, na yi.”

 

Sai kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sake tambayarsa: “Ko ka yi imani da cewa, Muhammadu Manzon Allah ne?

 

Balaraben yace: “Eh, na yi.”

 

Daga nan sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yace wa Bilalu: “Tafi ka shelanta wa mutane kowa ya ta shi da Azumi gobe.”

 

Ka ga a cikin wadannan Hadissai, musamman ma na biyun, akwai babban darasi, da ke tabbatar da girman wannan addini. Wanda kuma ya kamata a ce Malamai da shugabannin wannan al’umma sun kwaikwaya. Wato su fahimci cewa kowane mutum amintacce ne kuma karbabbe a idon Shari’a, a mataki na farko.

 

Ba kuma za a qi karbar maganarsa ba a kan komai, sai idan wani mugun hali ya bayyana gare shi, wanda zai soki lamiri da adalcinsa. Ko kuma a wayi gari tare da fahimtar cewa, yana da qarancin hankali, ko kuma ba ya son kowa da alheri sai kansa.

 

Wannan ko shakka babu haka yake. Domin ka ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yarda da maganar Balaraben qauye a kan wani babban al’amari a Musulunci, wato Azumi, ba kuma tare da wani irinsa ya goya masa baya ba, shi Balaraben.

 

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi la’akari da kasancewar Azumin Ramalana ginshiqin addini ba, balle ya nemi shedar taron jama’a a kan tsayuwar watansa. Wannan aqida kuwa, ita ce abin da ya kamata masu tsananta wa mutane al’murran addini, su fahimta su kuma kama, tare da komowa a kan tafarki madaidaici.

 

Haka kuma daga cikin Hadissan da ke tabbatar da dogarar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi a kan cikar watan Sha’abana kwana talatin, kafin ya kama Azumi, idan ganin watan Azumi da qwayar ido ya faskara, akwai cewar da ya yi wa Sahabbai, su dogara a kan ganin qwayar ido ga watan ba hisabi ba.

 

Kuma su tabbatar da qarewarsa ta wannan hanya. Yace: “Kada ku kama Azumi sai an ga wata da qwayar ido. Haka kuma kada ku aje shi, sai an ga watan Sallah da qwayar ido.

 

Kuma kada ku yarda da wata hanya da ba wannan ba. Idan Kuma kuka kasa ganinsa saboda wani dalili, to ku bari sai watan Sha’abana ya cika kwana talatin.

 

Da zarar mutum biyu sun bayar da sheda, to ku kama Azumi, ku kuma aje idan irinsu suka bayar da shedar qarewarsa.”   Allah yasa muna fahimtar karatun.

 

Allah ya karbi Ibadun mu na wannan watan Albarkan ANNABI S.A.W. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button