BABU RUWAN KA DA ABINDA AKE YAYI, KAYI ABINDA KA IYA KO KAKE DA HALIN YI, DUNIYAR BA ZAMA NA DINDINDIN AKE BA.

MU MUKA SA RAYUWA TAYI TSADA

 

 

Mu ne muka sa rayuwa tayi mana tsada saboda mun yi watsi da abubuwan da muka yi gado, mun rungumi abubuwan da ba namu ba.

 

A tsammani na, babu ɗan gata kamar ɗan arewa wanda yake musulmi, saboda rayuwar arewa ko ince rayuwar bahaushe akwai sauki da tsari a cikin ta, sannan shigowar musulunci rayuwar tasa kuma sai ta ƙarawa rayuwar armashi saboda Annabi Muhammadu SAW ya fi kowa iya sauƙaƙa rayuwa ga ɗan Adam.

 

Mu fara da fannin gine-gine, a kullum kowannen mu, kokarin mantawa yake yi da tsarin gini wanda ake yi shekaru ashirin baya, wato ginin block da rufin kwano da tagogi na karfe tareda fentin ruwa, yanzu kowa kokari yake yi yayi ginin bungalow na block bayan an zuba madarar kankare a ƙasa sannan ayi rufi na holoƙo, ayi POP, bangon kuwa kafin fenti sai anyi masa sarrafe-sarrafe, kayan daki kuwa an daina yayin na Nigeria sai na kasar waje, wanda bai karɓi tsarin ginin shekaru ashirin baya ba, tayaya kake tunanin ma zaiyi ginin shekaru ɗari baya wato ginin ƙasa wanda har a masarautu su ake yi a baya?

 

In muka dawo fannin abinci, zogale, rama, tafasa, da sauran lafiyayyun ganyayyakin da muke ci a da a matsayin abinci, yanzu sun zama duk wanda kaga yana amfani dasu, a matsayin larurar magani yake amfani dasu ba abinci ba. Babu ruwan mu da tsakin pate-pate sai couscous, babu ruwan mu da garin masara ko hatsi sai semovita, ba ruwan mu da gurasa sai shawarma da sauran su, duk wani abincin mu na asali wanda ake ci domin a ƙoshi ko saboda ƙwalama, wayanda suke da sauƙin haɗawa, sun zama mana abin ƙyama. Har ruwa, in aka zo gidan ka babu fridge da bottle water, kamar ka kashe baƙon sarki haka zaka dinga jin kunya alhalin ruwan fridge din cutarwa gareshi, na tulu yafi lafiya.

 

Toh ballantana kuma fannin ababen hawa, jaki ya zama abin kwaso kaya a wasu wuraren a ƙauye, doki ya zama abin sport, raƙumi kuwa an barwa buzaye kayansu sai in ana so ayi bikin alfarma za a siyo a yanka, kowa burin sa mota ko jirgi yanzu, babu ruwan kowa da ababen hawa na da masu albarka da daraja, kai hatta keke mai taya biyu, in zaka hau yanzu sai anyi ma kallon talauci ya maka katutu ko kuma mai tumbin yasin yayi nasara a kan ka.

 

In ko aka dawo fannin sana’a ko kasuwanci, mafi yawan mu abinda muka gada a gidan mu bamu iya shi ba ko bama yi, bamu damu mu iya din ba ko muyi shi saboda muna ganin wahala ne ko rashin wayewa. Misali ba lallai bane a yanzu ka samu jikan wanzamai ko masunta ko makera wanda yake kan sana’ar kakannin sa, an watsar an shiga duniya yin sabon abu, ko kuma ana jira a samu aikin gwamnati, alhalin sana’ar gadon nan mafi yawa jarin da zaka buƙata bai wuce naira dubu biyar ko goma ba, albarkar da zaka samu kuwa Allah kaɗai ya san shi, amma ba za muyi ba.

 

Mu waiwaya mu tuna asalin mu da abincin mu da rayuwar mu da al’adun mu, mu rayasu domin samun sauki a wannan cakuɗaɗɗiyar zamanin. Maganar gaskiya fa, komi iya mulkin Shugaba, komi kyan ƙasa, komi yawan kuɗin da za ka samu, dole fa ka sani, rayuwar nan kowa da yadda Allah ya tsara masa, kuma wanda ya huta kuwa shine wanda ya tafiyar da rayuwar sa dai-dai da mukamin sa.

 

BABU RUWAN KA DA ABINDA AKE YAYI, KAYI ABINDA KA IYA KO KAKE DA HALIN YI, DUNIYAR BA ZAMA NA DINDINDIN AKE BA.

 

✍️Sidi Sadauki

Back to top button