Dole Gwamnatin Tarayya Dana Jihar Kaduna Tare Da Rundunar Sojojin Saman Najeriya Su Biya Hakkin Yan’ uwan Mu Da Aka Ka@she
JINANENSU, DA RAYUKANSU BA ZASU TAFI A BANZA BA…!
1- Shin jirgin daga ina yake?
2- Harin Bomb din daga su wa yake?
3- Akan wacce manufa akayi harin?
4- Idan kuskurene wanne yunkuri za’ayi domin biyar diyan rayukan da aka salwantar tare da kiyaye faruwar hakan nan gaba?
Rayuwar talakan Nigeria tayi arahar da a yau ko mutum nawa aka kashe, ba kowa ne ma ke tsayawa yana jero irin wadannan tambayoyin ba, mai yiwuwa saboda riskar amsoshinsu na bukatar jan gwagwarmaya wanda idan ba’a yi da gaske ba, shi mai neman amsar shima sai a turashi wajen wadanda ya kudurci gwagwarmayar akansu, hakan yasa sai dai abinda kowannenmu zai iyayi shi ne “Addu’ar nema musu gafarar ALLAH” tare da lulluba da bargon tsoro.
To zance na gaskiya idan muka tafi a haka, to a kullum darajar Jinanenmu zai dinga sauka kasa, a yayin da salwantar da rayukan al’ummarmu zai iya zama abu mai matukar arha.
Kaddara ma Jirgin Soji ne suka yi kuskuren sakin wannan Bomb din shikenan bayan wannan addu’oi da muke na nemawa mamatan gafara, babu inda zamu motsa akan hakan?
Idan ya zamo ana kashe mutane a irin wannan salo, sai ya zamo ba’a aiwatar da kowanne irin bincike domin daukar mataki, kada muyi tsammanin wata rana yan wasu kungiyoyin addini dake da tsattsauran kiyayyar Sufaye idan suka samu shiga aikin Soji, idan suka samu irin wannan dama, ba zasu ke kitsa irin wadannan hare-hare akan mutanenmu ba.
SABODA HAKA, IYA GUDUMMOWAR DA ZAMU IYA BAYARWA SHINE, MU FITO A MEDIYANCE MU BARRANTA DA WANNAN AL’AMARI, SANNAN KUMA MUYI TA KIRA HAR SAI GOBNATI TA DAUKI MATAKIN DA YA DACE, DOMIN BABU TA YADDA MATUKIN JIRGIN YAKI ZAI DANNA KUNAMAR SAKIN BOMB AKAN WASU TARON AL’UMMA, BA TARE DA SANIN SU WA YA HARABA?
SHIN ME YASA BAI SAKI KUNAMAR A BARIKIN DA YA TASO BA, ME YASA BAI SAKI A GOVERNMENT HOUSE BA, ME YASA BAI SAKI A WATA JAMI’A DAGA CIKIN JAMI’OI BA?
ALLAH YA GAFARTA MUSU, YA RAHAMSHE SU. AMIIIIN YAA ALLAH.