GASKIYAR MAGANA AKAN BAWA FARFESA IBRAHIM MAQARI LIMAMCI MAKKA.
AKWAI HANYOYI MASU SAUKI NA GANE SAHIHANCIN LABARI KO RAUNINSA A MEDIA.
1- Idan labari yazo maka akan wani mutum, game da samun wani ci gaba, ko kuma fadawa wata jalalar, ko kuma akan wani abun dake da alaka dashi, to ka tsaya kayi nazarin inda labarin ya fito:-
1- Shin shi mutuminne ya bayyana da kansa ta hanyoyin da yake bayyanawa Duniya al’amuransa kamar shafukansa na sada zumunta, ko kuma anji labarin wajen wani makusancinsa da aka san lallai shi zai san duk abinda ya shafesa..?
2- Sannan shi mai bayar da labarin, shin ya fadi inda ya ciro labarin, ko kuma mahallin da labarin ya fito, shin akwai shaida na wata sahihiyar takarda, Video, ko kuma Audio dake tabbatar da sahihancin labarin, wanda idan aka bibiyi daya daga cikinsu zai kai mutum ga ainashin inda labarin ya fito.
Amma haka kawai wasu ke busar iska su rubuta abinda sukeso ta hanyar kawo abinda zaaija hankulan mutane zuwa garesu, da niyyar tara mabiya a shafukansu na Jaridu, su kuma mutane sai su aminta dasu ba tare da yin bincike ba, wala’Allah saboda kyautata musu zato.
Ban gaskata ko karyata wannan labari ba, amma a bisa ga dukkan ma’aunai labarin bai fito da siffar sahihanci ba, baldai fatanmu ALLAH ya cirar Maulana Prof. zuwa ga kololuwar alkairi, alfarmar MANZON ALLAH (S.A.W) ya tsare shi dukkan sharri.
ALHAMDULILLAH.
Daga: Muhammadu Usman Gashua