ZABEN 2023: Kowa Yake Ya Zabi Wanda Yake So, Amman Ku Zabi Shugaba Nagari. Inji Sheikh Dahiru Bauchi OFR RA.

YA DACE JAGORORIN KUNGIYA SU NAKALCI IRIN WANNAN HIKIMAR WAJEN JAGORORIN SUFAYE.

 

A zabukan 2011 da kuma 2015 wasu daga Maluman Kungiya sun ayyanawa mabiya yan takarar jam’iyyun da suke so su zaba, karshe dai duk dadin bakin da sukayiwa mabiya aka fuskanci akasinsa kowa yaji a jikinsa, to sai gashi yanzu ma wasunsu na son mai-maita kuskure ta hanyar yin abinda suka yi a baya.

 

Ka duba jawabi mai cike da wayewa, yadda Maulana Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, da Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A) suka fayyacewa dukkanin mabiya akan, kowa ya zabi wanda ya kwanta masa a rai, wanda hakan matakine da babu wani guda da zai kuka dasu har abada, idan aka samu akasi a mulkin wani shugaba da ace sun ayyana shi.

 

ALLAH YA GANAR DA JAGORORIN WAHABIYA GA RUNGUMAR WANNAN HIKIMAR, WALA’ALLAH SA RAGE DUMLMIYAR DA MABIYA. AMIIN YAA ALLAH.

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button