Inna’lillah Wa’nna Ilaihir Raji’un: Allah Ya Yiwa Mai Kula Da Mukallan Ka’abah Rasuwa.

Babban jagora mai kula da dakin Allah Ka’abah ya rasu, Dr. Saleh bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi.

 

Ya rasu yana da Shekaru 109 a duniya, ya kuma shafe shekaru 77 a duniya yana hidimtawa Ka’abah (Dakin ALLAH Ubangiji Madaukakin Sarki).

 

Shine marigayin ya fito daga kabilar Shayb daga gidan Qusay bin Kilab, Zuri’ar su ce ke rike da makullin Ka’abah tun zamanin Jahiliyya har zuwan Manzon ALLAH Annabi Muhammadu ﷺ.

 

An sami takardama bayan fatahu Makka wanda har Allah ya saukar da Ayar Alkur’ani mai Girma dake goyon bayan kabilarsu akan mayar da makullin zuwa ga ɗan kabilarsu..

 

Wanda hakan yayi silar shigar da yawa daga cikin yan kabilarsu cikin addinin Musulunci.

 

Allah ya gafarta masa ya kyautata makwancin sa. Amiiiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button