KIRA ZUWA GA HUKUMAR Hisbah Board Kano Hisbah Board.

KIRA ZUWA GA HUKUMAR Hisbah Board Kano Hisbah Board

 

A Game da Wani Matashi Mai Da’awar Malanta.

 

 

1~Mun sani Cewar an kafa wannan hukuma ne domin Umarni da kyakykyawa sannan tayi hani da mummuna,wannan aiki Kuwa bashi bukatar duba bangare su wane da wane ko daga Ina Barna ta bayyana wajibi ne ayi kokarin kauda ita

 

2~ Tabbas mun sani ba zai buya ga Wannan hukuma ba,bullar wani matashi da yake da’awar Malanta Mai Suna Adam Abdallah,inda jama’a suke ganin bidiyon sa Yana yawo a kafafaen sada zumunta Yana barna da zagin Allah da canjawa Annabi Sallallahu alaihi wasallam magana bisa jahilci.

 

3~ An jiyo shi a wani Clip nashi Yana Karanta Alqur’ani har Yana kafirta Allah saboda jahilci,sannan an jiyo shi Yana jirkita ayoyin Alqur’ani Yana bata hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi,a tare da hakan Yana yiwa kan sa kirarin cewa shine عالم العلماء.

 

4~A saboda haka ne muke Jan hankalin Wannan hukuma da lallai tayi bincike kan wannan Matashi Mai Da’awar Malanta sannan ta dakatar da shi daga wannan barna da yakewa Musulunci da Musulmai,idan da hali ta dauki nauyin saka shi a makaranta domin koyon ilmi.

 

Wannan Clip dake kasa Samfur ne da zai tabbatar da Cewar lallai wannan mutun jahili ne tammi da baya gane abubuwa

Share

Back to top button