Masallacin Sheikh Abulfathi Da Gidansa Ba Su Samu Âmbāliyār Ruwa Ba.
Masallacin Sheikh Abulfatahi Da Gidansa Ba Su Samu Âmbāliyār Ruwa Ba.
“A wani rahoto da mu ke samu mai kama da haka ya yi nuni da cewa; duk da irin Âmbāliyār Ruwan da aka yi a garin Maiduguri wanda ya ke kusa da wurin iyalan babban malamin addinin Musluncin suke, cikin hukuncin Allah Majiyar mu ya tabbatar mana Ruwan bai isa koda farfajiyar Masallacin Shehin ba da ake yi wa laƙabi da (Madinatu Sheikh Ahmad Abulfatahi Maiduguri) dake jihar Borno.
Bugu da ƙari rahoto ya ci gaba kamar haka, har ta gidan Shehin ruwan bai riske sa ba, duk da duba da irin ɓàrnàr da ruwa ya tafka a sakamakon afkuwar lamarin a anguwar.
“Sanarwar ta soma da cewa; dubban masoya da su guji yaɗa ji-ta-ji-tar cewa! Ruwa ya afka in da iyalan malamin suke, ana kira da kowa ya kwantar da hankalinsa.”
Daga Karshe kuma Khalifa Aliyu Sheikh Ahmad Abulfathi Na Sanar Da ‘Yan Uwa Cewa Za’ayi Zaman Maulidi Ranar Asabar 14/09/2024 Awayi Gari Ranar Lahadi 15/09/2024 INSHA ALLAH.
Sannan Khalifa Yace A Sanar Da ‘Yan Uwa Masu Zuwa Daga Garuruwa Daban Daban Cewa Yana Neman Alfarman su Dasu Hakura Da Zuwa Maiduguri Saboda Wannan Iftila’i Daya Faru A Jihar Borno.
Allah ya ƙara kiyaye gaba. Amiin Yaa ALLAH