Za’a gina babban katafaren cibiyar haddar Alkur’ani mai girma ta zamani a jihar Bauchi mai suna “Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA”

ALBISHIRIN KU MUTANE SHEIKH DAHIRU BAUCHI RA.

 

Za’a gina babban katafaren cibiyar haddar Alkur’ani mai girma ta zamani a jihar Bauchi mai suna “Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA” wanda mai girma gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulƙadir Ƙauran Bauchi ta dauki nauyin ginawa.

 

Gwamnan jihar Bauchi Senator Bala Abdulƙadir Ƙauran ya fadi hakan ne, a yayin da yakai ziyara girmamawa ga babban malamin a gidan sa dake titin Bauchi zuwa Gombe, inda ya tabbatar da fara aikin cikin kan-kanin lokaci da rardan Allah.

 

Muna alfahari da wannan katafaren aiki, Muna addu’an Allah ya saka masa da alkhairi, ya karawa Maulana Sheikh lafiya da nisan kwana albarkacin Manzon rahma SAW. Amiiiin

 

Babangida Alhaji Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button