Mutumin Da Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW, Wato Salman Rushdie Na Cikin Yanayi Na Rai A Hannun Allah.

Salman Rushdie In Maye Ya Manta…

 

Mutumin Da Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW, Wato Salman Rushdie Na Cikin Yanayi Na Rai-Kwakwai Mutu-Kwakwai,

 

A shekarar 1989 jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Ruhullah Khumaini (QS) ya ba da fatawar kisan marubucin littafin The satanic verses (Salman Rushdie) wanda a ciki ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAWA). Tun daga lokacin ya dinga fuskantar hare-hare, wanda yake tsallake rijiya da baya. Ya kasance karkashin kulawar tsaro mai tsauri bisa sanya idon hukumar leken asirin Ingila Ml6. Yayi bankwana da dukkan wata walwala da shiga mutane sakamakon abin da ka biyo baya.

 

Wadanda suka fassara littafin zuwa wasu harasan na duniya sun fuskanci na su harin kamar Hitoshi Igarashi wanda ya fassara shi zuwa japananci. An kai masa hari a 1991. Sannan William Nygaard dan Norway da Aziz Nesin dan Turkiyya da ya fassara zuwa Turkanci.

 

Kwatsam jiya juma’a 12/08/2022 sai ga labarin cewa wani mai neman yardar Allah ya kaddamar da hari da wuka ga wannan tsinanne a Amurka, lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taro.

 

Amincin Allah ga gwarzon kare martabar Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi Imam Ruhullah Khumaini. La’anta ga makiyan Manzo da masu ba su kariya har izuwa ranar kiyama.

 

Daga: Aminu S Miko

Share

Back to top button