Nasiha Mai Matukar Muhimmanci Ga Daukacin Al’ummar Musulmai Baki Daya.

YI KOKARI KA KIYAYE WANNAN.

 

Daga MALAM UMAR SANI FAGGE

 

(1). Karka rinka yin fitsari a wurin da kake yin wanka, domin hakan yana gadar da yawan

mantuwa.

 

(2). Karka rika kwantawa barci bayan ka

cika cikinka da abinci, domin yin hakan yana

gadar da mutuwar zuciya.

 

(3). karka rika yawaita kallan al’auranka ko ta wasu, domin yin hakan yana sa dakikanci

da nauyin kwakwalwa wajen fahimtar abubuwa.

 

(4.). kar karika yin bacci bayan sallar

asuba har sai rana tafito, domin yin hakan na

janyo tsiya da talauci.

 

(5). kar ka sha madara bayan kaci kifi, domin yin hakan yana gadar da kuturta.

 

(6). karka ci ko sha alhali kana da janaba, domin yin hakan makarohi ne, kuma yana jawo

raunin jiki.

 

(7) karka rika hassada ko munafunci da

ha’inci, domin suna da hatsari ga lafiya, sukan

kuma haifar da cutar hauka, gashi kuma suna

bata ayyuka masu kyau.

 

(8).karka rika yawan kukan babu ko ka yi ta tallan talaucinka afili. Yin hakan yakan dawwamar da mutum cikinsa.

 

(9) karka rika kwanciya barci alhali kana jin fitsari, yin hakan yana haifar da mutuwar

mazakuta.

 

10. Duk wanda yadau hannunsa mai albarka ya tura wannan saqon, ya Allah ka nuna masa manzo( SAW) acikin mafarkinsa. Ameen

 

Daga: Nauwas Shareef

Back to top button