SHARHI KAN MAGANAR MAQARI: Zancen Farfesa Ibrahim Maqari Akan Hawa Yara Kanana Mumbarin Wa’azi.

WADANDA SUKA TSARGU, SUN FAHIMCI ZANCEN SIFFARSU TAKE “SIFFATAWA”.

 

Su yaran da suka cika shafukansu da rubuce-rubuce na zagi da gugar zana gareshi, dalilin wannan rubutu, na rasa azanci da hikimarsu, domin shi dai Maulana Prof. bai fadi illa ko kuma amfanin hakan ba, balle wasu ko wani ya fassara hakan da cewa sukarsa ake ko kuma kyara.

 

Amma idan muka dubi zancen a Mahanga ta lura, zamu samu wajibine irin wadannan yaran su tsargu, harma suyi ta raddace-raddace marasa wata ma’ana, domin kuwa, shi wannan zance ilmine a cure wanda ke bayar da haske zuwa ga fadin MANZON ALLAH (S.A.W) cikin hadisan da yayi bayanin alamomin karshen Duniya.

 

Kamar yadda yazo cikin Fadinsa a hadisin da Sayyadina Abdullahi Bn Umar (R.T.A) ya ruwaito: ANNABI (S.A.W) yake cewa

 

إن الله لا يقبض العلم انتزاعًا ينتزعه من العباد، ولكن يقبض العلم بقبض العلماء حتى إذا لم يُبْقِ عالمًا اتَّخذ الناس رؤوسًا جهالاً، فسُئِلوا فأفتوا بغير علم؛ فضلوا وأضلوا

 

Ma’ana: Lallaine ALLAH bazai dauke ilmi ta hanyar karbeshi daga bayinsa ba, amma zai dauke ilmine ta hanyar dauke rayukan Malamai (Masanan gaske) har zai zamo babu wani Malami da zai rage face zasuke bin Jahilan Jagororin (Addini), kuma za’ake tambayarsu fatawa su kuma su bayar ba tare da Ilmi ba, su wadannan batattune, kuma masu jan mutane zuwa ga hallaka. (Bukhari).

 

Idan muka lura da wannan hadisi da kyau, to yana bayyana mana zahirar yaune, domin kuwa zaka samu akasarin jagororin Ilmi Malamai idan suka koma zuwa ga ALLAH, to sam ba’a samun kwatankwacinsu da suke maye gurabensu, face za’a samu bayyanar matasa dake hawa kan Mimbarorinsu, suna masu aibata su Jagororin Ilmin, tare da bayar da fatawowi da babu dandanon Ilmi cikinsu, wadanda ke shiryarwa zuwa ga bata ga hallaka, zaka samu mutum na takama da Academic Tittle, amma mas’alar dake cikin ahalari sai ta gagareshi warwarewa, ayayin da shine karanto hadisai da ayoyi yana ta daura mabiya akan hallaka.

 

Yanzu bai ishemu Misali ba, abinda ke wakana ko a Social Media, yadda al’amuran Addini suka har gutse, kullum sai sabbin fatawowi ake ta kirkiri, akan rashin fahimtar nassosin da ake karantawa.

 

SABODA HAKA, SU WADANDA SUKA TSARGUN, HAR SUKE TA SAKIN ZANTUKA NA RASHIN KUNYA, TO SUNE WADANDA SHI ZANCEN KE SIFFATAWA.

 

ALLAH YASA MU DACE. AMIIN YAA ALLAH

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua

Back to top button