Sheikh Dahiru Bauchi OFR Ya Mika Sakon Jaje Bisa Iftila’in Daya Faru A Jihar Jigawa.

SAKON JAJANTAWA BISA IFTILA’IN DA YA FARU A JIHAR JIGAWA A AREWACIN NIGERIA.

 

Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi R.T.A Yana Mika Saqon Jaje Bisa Iftila’i da Ya faru Na Gobara Wadda Yayi Sanadiyar Konewan Wasu Daga Cikin Yan’uwa Musulmai a Garin Majiya Karamar Hukumar Taura Jihar Jigawa.

 

Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi R.T.A Yayi Addu’a Ta Musamman a Wadannan Marigaya da Niyan Allah Ya Gafarta Musu Allah Ya Musu Rahama Allah Ya Yafe Musu Kurarensu.

 

Iyalansu Allah Ya Basu Hakuri Allah Ya Basu Juriya na Rashin da akayi Allah Ya Karbi Bakwancin Su.

 

Maulanmu Sheikh Yayi Kira da Dukkanin Musulmai Baki Baki Daya Babba da Yaro Mace da Na Miji

 

In Munyi Salloli Guda (5) da Mukeyi a Rana Kar Mu Tashi Sai Mun Karanta (ISTIGFARI) 100 a Kowace Bayan Sallar Farillah da Niyyan Allah Ya Kawar Mana da Kowani Bala’i a Wannan Kasa Tamu Nigeria.

 

Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi R.T.A Ya Kara da Cewa Kar Mu Sake Mu Cigaba da Kusantar Allah Kar Muyi Wasa Mu Tattara Komai Mu Mika Ma Allah Tabaraka Wata’ala.

 

Allah Zai Yaye Duk Wani Bala’i a Wannan Kasa Tamu Ta Nigeria.

 

Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Khadimul Faida) Shine Yayi Wannan Jawabi A Madadin Sheikh Dahiru Bauchi.

 

Allah Ya Bamu Lafiya Da Zaman Lafiya A Najeriya. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button