SHIN DA GASKE RAHOTON BBC HAUSA, YA SABAWA FADIN MANZON ALLAH (S.A.W) GAME DA TSAKA..?
SHIN DA GASKE RAHOTON BBC HAUSA, YA SABAWA FADIN MANZON ALLAH (S.A.W) GAME DA TSAKA..?
Babu shakka, an samu dumamar yanayi a Media tun bayan bayyanar wannan rahoto zuwa yanzu, amma sai dai da bukatar mu fadada nazari matuka, domin ganin shin abinda suka kawo tanaqud ne ga zancen MANZON ALLAH (S.A.W) game da matsayin Tsaka a musulunci, ko kuma dai mu ne muka kuskure ta hanyar rashin aje abubuwa a mahallansu.
MENENE MATSAYIN TSAKA A MUSULUNCI.
Ita wannan dabba, ta kasance cikin jinsin dabbobi da ta gaji la’ana daga magabatanta, hakan kuwa ya faru ne ko a lokacin da Sarki Lamarudu da jama’arsa suka hura wuta, da nufin kone ANNABI IBRAHIM (A.S) aka nemi wa zai je ya shiga cikin ramin ya dosanawa makamashin wuta aka rasa, karshe dai ita “Tsaka” ta karbi wutar taje ta dosana (Bukhari da Muslim).
Sai ta kasance cikin jinsin dabbobin da ANNABI (S.A.W) yayi umarni da kashewa kamar: Kunama, Maciji, Bera, Mahaukacin kare da sauransu.
Har ma ya zamto yawan ladan kasheta na bambanta tsakanin bugun farko, ko na biyu ko kuma bugu na uku kamar dai yadda yazo a hadisi cikin fadin MANZON ALLAH (S.A.W)
من قتل وَزَغًا في أول ضربة كتب له مائة حسنة، وفي الثانية دون ذلك، وفي الثالثة دون ذلك
Ma’ana duk wanda ya kashe “TSAKA” a bugun farko to yana da lada dari, wanda ya kashe a bugu na biyu yana da lada sabanin haka, wanda ya kasheta a bugu na uku shima na da lada sabanin haka. (Muslim).
Ko da yake akwai bayanai na tsoratarwa dadama akanta wadanda wasunsu basu inganta ba, wasunsu kuma daga al’adu ne da sauransu.
GAME DA RAHOTON BBCHAUSA DA KUMA FADIN MANZON ALLAH (S.A.W) GAME DA TSAKA..
Idan mun lura da kyau, su BBCHAUSA sun gayyaci likita ce ta basu bayani akan tsaka, abinda duk zata fadi kuwa ilmi ne da ta samu daga binciken kimiyya, shi kuwa binciken kimiyya ana yinsa ne a lab, su kuwa na’urorin dake lab suna iya gano abinda yake na zahiri ne kadai, basu iya gano abinda yake na illar la’ana, badini, ko kambun baka da sauransu.
Baka lura ba idan masu kambun baka suka kama mutum, ko Aljanu suka shiga jikin wani, idan akaje Asibiti basu iya gano cutar, duk binciken da za’ayi amma rashin ganowarsu na kore illar da Aljanu da masu kambun baka ke haifarwa ? To mai yiwuwa tsaka itama illarta irin jinsin wannan illar ne, ko dan duba da cewa “La’anar da ke tattare da jinsinta ita la’ana ce daga magabata tsarkaka”.
Saboda haka, duk yadda za’ayi amfani da na’ura mai yiwuwa baza’a iya gano illarta ba, amma kuma illarta na iya shafar wanda ya ma’amaltu da ita, saboda abinda take tattare da shi na la’ana.
Saboda haka, lallai bincikensu ba kishiya ba ne ga abinda yazo a Musulunci idan muka aje komai a mahallinsa, domin su sunyi bincike ne da abinda suke iya gani su gano da na’ura, ayayin da akwai dimbin abubuwa da ALLAH ya hijabantar da idanu ga iya riskarsu, kuma rashin riskar idanu ko na’aura bai nuna rashin kasancewarsu.
ILLA DAI ABINDA YA DACE SUYI SHINE SU GAYYATO MALAMIN ADDINI DA KUMA LIKITA SU TATTAUNA, DOMIN A AJE KOMAI A MAHALLINSA, SANNAN SALON RUBUTUN DA SUKA YI SHIMA KAMAR AKWAI RASHIN DUBA BANGARE BIYU KAFIN FITO DA SHI, YA DACE SU GYARA HAKAN.
ALLAH YA KYAUTA. ALHAMDULILLAH