Darikar Tijjaniyya: Sheikh Idris Fogun Bida, Wanda Yada Darikar Tijjaniyya Da Faila A Al’umman Nufawa.

Sheikh Idris Fogun Bida, daya daga cikin manyan zaratan shehunnan da suka yada darikar Tijjaniyya da Faila a al’umman Nufawa

 

Sheikh Idris Fogun Bida, asalinsa mutumin garin Dandume ne dake jihar Katsina, Bafulatani ne ta uwa da uba, ya zo Zariya neman ilimi inda yayi karatu mai zurfi a hannun Sheikh Adulkadir Zaria RTA.

 

A lokacin da mutanen Bidda (Babban garin Nufawa) dake jihar Neja, a karkashin jagorancin madakin Nupe suka roki Shehu Abdulkadir Zariya da ya basu Malami wanda zai koyar da su karatu da addini sai ya tura musu Sheikh Idris Fogun Bidda, Madakin nupe yayi masa masauki a anguwan fogun cikin tsakiyan garin Bidda inda ya fara koyarwa a nan, daga bisani kuma wannan wuri ya zamo babban zawiyya wanda ta kunshi masallaci da makaranta, ya koyar da dubbannin mutane karatu wadanda da yawa daga ciki suka zama manyan malamai wadanda suka kafa zawiyoyi da makarantu a garin Bidda da sauran garuruwan nufawa.

 

Ya yada darikar tijjaniyya da faila a cikin al’umman nufawa, Zawiyyarsa ta zamo babbar mashaya ga dukkan yan darika da failan Shehu, itace ta zamo babbar masaukin da take karbar manyan bakin Shehunnai da sharifai daga kasashen Najeriya da Nijar da Senegal da Morrocco da Muritania, a dalilin haka sunan layin da yake zaune a anguwan fogun ya koma ‘Tudun Faila’.

 

Shehu Idris Fogun Bida ya rasu a shekara 1995 a garin bida, dubun dubatan musulmai suka halarci janazarsa wanda a wannan lokacin al’umman Bidda suka shaida cewa tunda suke basu taba ganin janazar da ta tara mutane da yawa kamar janazarsa ba.

 

Yayi talifofi da yawa da yaren Larabci da Hausa.

 

Allah ya jikansa ya gafarta masa, ya hadashi da manzon Allah SAW. Amiiiin

Share

Back to top button