Yadda Aka Gudanar Da Babban Taron Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani RA A Garin Gombe Karo Na Bakwai (7).
AN GUDANAR DA TARON MAULUDIN TUNAWA DA SHEIKH AHMADU TIJJANI (RA) A GOMBE.
Daga Babangida A. Maina
Al’ummar musulmi mabiya Darikar Tijjaniyya sun gudanar da taron mauludin tunawa da Sheikh Ahmad Tijjani Ra(Mai Darikar Tijjaniyya) wanda aka gudanar a filin wasa na Pantami dake birnin Gombe karo na bakwai (7) tare da zagayowar ranar samuwar sa shekara ta 294 da haifuwa.
Taron mauludin wanda aka saba gabatarwa duk shekara – shekara a jihohi dake najeriya don tunawa da irin gudummawar da shehin malami ya bawa addinin Musulunci da darikar Tijjaniyya da kuma koyar al’ummar Musulmai musamman a Najeriya muhimmanci zaman lafiya a kasa baki daya.
Taron ya samu halartar manyan baki daga sassan duniya kamar Algeria, Morocco, Senegal, Sudan, Niger, Camoroun da kuma wasu ƙasashe mabanbanta.
Taron ya samu halartan babban Khalipha Tijjaniyya na duniya Sheikh Khalifa Ali Bel Arabi tare da tawagarsa, babban malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Gwamnan jihar Gombe wanda Hon kwamishina Magudu da Hon, kwamishina Magaji Gettado suka wakilce shi, wakilan Gwamnoni daga jihohin Bauchi, Yobe, Adamawa, da kuma Borno suka turo wakilai. Tare da manyan sarakunan gargajiya da kuma wakilan masarautu.
Cikin jawabai mabanbanta shugaban taron Khalifa Sheikh Ali Bel Arabi bayyana cewa mu riƙe soyayyan Manzon Allah saww da waliyan sa musamma Sheikh Ahmad Tijjani mai Darikar Tijjaniyya da kuma koyi da ayyukan sa da dabi’un sa a duk cikin rayuwar mu. Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA ya godewa daukacin al’ummar Musulmai da suka samu halartan wannan taro, inda yace Allah ya sakawa kowa da alkhairi ya biya bukata, ya maida kowa gida lafiya alhamdulillah.
Cikin manyan baki da suka samu halartan akwai Shehunai, mudaddamai, khalifofi, da sauran yan uwa masoya Manzon Allah SAW.
Allah ya sakawa kwamitin shirya wannan taro, da jama’an tsaro yan’agaji na kowanne bangare
Allah yasaka ma kowa da Alkhairi, Ameen
Allah ya kara wa Sheikh Dahiru Bauchi RA, da nisan kwana kara masa Lafiya mai maida kowa gida lafiya, Albarkan Manzon Allah SAW Amiin
Daga: Babangida A. Maina
National Director Fityanu Media
Founder MD/ CEO Tijjaniyya Media News