TA FARU TA KARE: Malam Abduljabbar Nasiru Kabara Ya Tabbatar Da A Yanke Masa Hukunci Da Gaggawa.

Kotu ta yanke wa Sheikh Abduljabar hukuncin ki@sa ta hanyar rataya

 

Babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano dake arewacin Najeriya ta yanke wa Malam Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin ki#sa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

 

An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola yace an same da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.

 

Daga cikin tuhumar da ake masa, hadda zargin wa’azinsa zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano tare da bantanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ﷺ da iyalan gidan sa wato matan Manzon Allah SAW har ma da sahabban sa.

 

Sheikh Malam Abduljabar Nasiru Kabara yayi magana ta karshe inda ya ce lauyan da ke kareshi bai san shi ba kuma baya neman afuwa saboda a cewar sa bai aikata laifi ba, don haka a gaggauta yanke masa hukunci ko wani iri ne.

 

A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓata@nci ga addinin Islama da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa, inda daga baya aka shirya mukabala kamar yadda ake ikrari a koda yaushe. Daga bisani malaman da suka gabatar da tambayoyin a gare shi kuma ba’a samu ingantatuttun hujjoji a gare shi ba.

 

Inda shugaban mukabalan ya tabbatar da magagganun da ake zargin sa dasu ya kuma mika rahoton sa ga hukumar shari’ar Musulunci ta jihar Kano.

 

Daga: BBC Hausa

Share

Back to top button