Zancen Maulana Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari Hafizalullah Yayi Gaskiya.

PROF YAYI GASKIYA CIKIN ZANCE SA.

 

Maganganun da prof maqari RTA yayi a jikin wannan hoton, gaskiya ne amma irin mai dacin nan da ba kowa yake son ji ba.

 

Tabbas cin haram, rashin biyayya ga iyaye da cutar da bayin Allah, zasu nesanta duk mai yin su daga samun yardar Allah sai dai saboda falalar sa in already ya zabi mutum ba wai ijtihadin sa zai kai shi ba. Kafin kuwa ya hau muqamin wulayar in dai an zabe shi saboda falala, toh zai samu shiriya sannan ya hau muqamin.

 

1. BIYAYYA GA IYAYE: Idan har furta UFFAN ga mahaifiya zai hana sahabin Annabi SAW furta kalmar shahada lokacin rasuwar sa, tabbas sabawa iyaye zai hana ordinary mutum samun wulaya. Idan har girmama uwa da hidimta mata yana cikin abinda yasa fir’auna samun daukaka a duniya, tabbas hidima ga iyaye zai daukaka wanda yayi imani da Allah zuwa ga wulaya.

 

2. CUTAR DA BAYIN ALLAH: Imam gazali lokacin da ransa ya fita, sai ya tafi sama zuwa fadar Allah. Allah yace masa yau ran ka ya dawo gareni, me ka tanada? Imam gazali yayi ta lissafo ibadu, amma Allah yace masa “duk ban karba ba”. Ran nasa ya juya zai sakko duniya sai Allah yace dakata gazali, ka tuna ranar da kake rubutu sai Quda ya sauka kan alqalamin ka bayan ka dangwalo tawada kace a ranka “qila wannan qudan qishi yake ji bari in barshi yasha”? Gazali yace na tuna Allah, Allah yace to saboda wannan shayarwar da ka yiwa Qudan nan zan baka aljanna.

 

Shayar da Quda ne ya samarwa gazali rahmar Allah duk tarin ibadun sa, toh da ya cutar da qudan nan saboda zalunci fa?

 

Shehu Ibrahim Inyass RTA na cewa “kar ka cutar da halittu ya kai dan’uwa na, domin halittun nan bayin Allah ne, kai ma ba zaka yarda a cuci bawan ka ba koda shine yayi laifi ballantana Allah, kaji tsoron ubangijin ka.

 

3. CIN HARAM: Shehu Abulfathi yana cewa akwai haram din da istigfari ba ta kankare ta sai dai imtihanin Allah kamar a daurawa mutum talauci, ciwo, yunwa ko annoba.

 

Annabi SAW yana cewa “Mutumin da cin sa haram, shan sa haram, wurin zaman sa haram, tufafin sa haram, tayaya Allah zai karbi addu’ar sa? Toh kaga wanda Allah baya karbar addu’ar sa taya wuridin sa zai samar masa da wulaya?

 

Shehu Ibrahim Inyass yace CIN HALALI tsantsa yana tsarkake zuciya ya qara mata imani.

 

Dan haka yan’uwa mu bar yaudarar kan mu, hanyar Allah yadda take a jiya, haka take a yau da gobe. Abinda magabata suka kiyaye, dole sai mun kwatanta a yau sannan za mu taka sawayen su a fadar Allah.

 

Faidha ta gajarce mana nisan tafiyar ne sannan ta kawo guzuri bayan da saka mu a jirgin sama, amma wajibi ne a kiyaye haqqoqin Allah da na bayin sa.

 

WANDA BAYA TSORON RAINA IYAYEN SA KO CIN HARAM KO CUTAR DA BAYI SABODA YANA TUNANIN AKWAI WANI ABU DA YA KAMA, TOH DA SANNU WANNAN ABUN ZAI RABU DASHI.

 

✍Sidi Sadauki

Back to top button