KISSA

  • Watarana ANNABI (S.A.W) Yana Tafiya a Bayan Garin Madina, Sai Ya Ji An Kira Shi: Ya ANNABIN ALLAH (S.A.W)!

    Watarana ANNABI (S.A.W) Yana Tafiya a Bayan Garin Madina, Sai Ya Ji An Kira Shi: Ya ANNABIN ALLAH (S.A.W)! Ya ANNABI ALLAH (S.A.W)!

     

    Sai ANNABI (S.A.W) Ya Duba Baya Bai Ga Kowa Ba Sai Ya sake Jin Kiran Sai Yabi Inda Sautin Yake Fitowa.

     

    Da Ya Isa Wajen Sai Ya Iske Wata Barewa a Daure, a Gefe Kuma Ga Wani Balaraben Kauye Yana Kwance Yana Barci.

     

    Sai Barewa Ta Ce Da Shi: “Ya RASULULLAHI! Wannan Mutumin Ya Farautoni Alhali Ni Ina Da ‘Ya’ya Guda Biyu a Wancan Kogon Dutse, Ka Taimaka Min Ka Sake Ni Na Je Na Shayar Da Su Nono Sannan Na Dawo”

     

    Sai ANNABI (S.A.W) YaCe:”Anya! Kuwa Zaki Dawo?”

     

    Sai Barewa Ta Ce”Idan Har Ban Dawo Ba ALLAH Yayi Min Azabar Da Zai Yiwa Mai Cin Rashawa”

     

    Sai ANNABI (S.A.W) Ya Kwance Ta Tafi.

     

    Da Barewa Ta Cika Alkawari Ta Dawo

    Sai ANNABI (S.A.W) Ya Kama ‘Kafarta Yana Kokarin Daureta Da Igiya Sai Balaraben Kauye Nan Ya Farka Daga Bacci,

     

    “Kai Ne Fansar Uwata Da Ubana Ya Manzon ALLAH.

     

    Ni Ne Na Farauto Ta Ko Kana Da Bukata.?”. Inji Wannan Balaraben Kauyen

     

    Sai ANNABI (S.A.W) YaCe: “Na’am! Ina Da Bukata”

     

    Sai Balaraben Qauyen Nan Yace: “Na Baka Ita Ya RASULULLAHI”

     

    Sai ANNABI (S.A.W) Ya Saketa Ta Koma Wajen Ya’yanta Tana Tafiya Tana Cewa:

     

    “Na Shaida Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai ALLAH. Na Kuma Shaida ANNABI MUHAMMAD MANZON ALLAH Ne”.

     

    DARASI:-

    Jama’a Idan Muka Duba Da Idon Basira Zamu Ga Abubuwan Da Wannan ‘Kissa Take Koyarwa Sune Kamar Haka:-

     

    1. CIKA ALQAWARI

     

    2. TSANANIN TAUSAYIN UWA AKAN ‘YA’YANTA

     

    3. NEMAN HALAL TA HANYAR FARAUTA

     

    4. DABBOBI KANSU NA TSORON AZABAR MAI CIN RASHAWA.

     

    YA ALLAH! KA QARAMANA SOYAYYAR ANNABI S.A.W BIJAHI S.A.W. AMEEN

     

    Via Umar Chobbe

  • KISSA: Kissar Wata Mata Tsohuwa A Zamanin Manzon Allah SAW.

    A Zamanin ANNABI (S.A.W) anyi wata mata tsohuwa mai masifar rikici da raki, ita wannan mata ta kasance kullun saita kawo kara gurin ANNABI (S.A.W) cewa anyi mata kaza, ko tace masa yara sun takura mata.

     

    Ana cikin haka wata rana ta shigo gidan ANNABI (S.A.W) domin takai masa kara, tana shiga saita tarar da killishi a gabansa, sai tace menene wannan sai yace mata kilishi ne, bayan ta gaya masa matsalarta, kafin ta tashi sai ya dauko kilishin yace ga wannan naki ne

    .

    Sai wannan tsohuwa tacewa fiyayyen halitta, kaga bakin nawa babu hakora bazan iya taunawa ba,

    .

    Sai ANNABI (S.A.W) ya karbi kilishin ya saka a bakin sa, ya ciccira mata yadda zata iya taunawa,

    .

    Sannan sai ANNABI (S.A.W) ya mika mata Tsohuwa ta dauki kilishin ta fara ci

    .

    A take a wurin sai anji ta fara yin salati ga ANNABI (S.A.W)

    .

    Bayan kwana biyu sai daya daga cikin matan ANNABI (S.A.W) suke tambaye shi cewa:

    .

    Ya ANNABIN ALLAH yanzu wannan tsohuwar sai dai kawai ta shigo gidan tana salati kawai, kuma ta gaishemu ta koma, amma ta daina kawo karar kowa?

    .

    Sai ANNABI (S.A.W) yace kun manta da

    ranar dana bata kilishi?

    .

    Sai matan suka ce kwarai kuwa mun tuna da wannan Ranar!

    .

    Sai ANNABI (S.A.W) yace to ai Albarkar nyawun dake bakina ne wanda ya taba

    kilishin Shine ALLAH ya kawar mata da duk wata damuwan ta anan duniya.

    .

    Kaji fiyayyen halitta kenan. Umar chobbe ne ke gaisheka Ya Rasulullah

    .

    YA ALLAH ka BAMU ALJANNA ALBARKAN NYAWUN BAKIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W).

    .

    Ya Allah kasa Albarkan Nyawun ANNABI S.A.W Ya Kawar Mana da Dukkan Damuwanmu Duniya da lahira Muma Bijahi S.A.W. Amiin

  • Wata Rana Wani Dattijo Yana Tafiya(Tare Da Muqarrabansa), Suna Cikin Tafiya Sai Suka Biyo Ta Wajen Wani ‘Kududdufi.

    Wata Rana Wani Dattijo Yana Tafiya(Tare Da Muqarrabansa), Suna Cikin Tafiya Sai Suka Biyo Ta Wajen Wani ‘Kududdufi, Dattjon Nan Ya Tura Wani Daga Cikin Muqarraban Nan Nasa Da Yaje Ya ‘Debo Masa Ruwa(a Wancan ‘Kududdufin) Saboda Yana Jin ‘Kishirwa.

     

    Wanda Aka Aika ‘Din Ya Tashi Yaje Don Ya ‘Debo Ruwan Kamar Yadda Dattijon Nan Ya Bukata, Zuwansa Ke Da Wuya Sai Ga Wani ‘Dan Maraqi Ya Shigo Cikin Ruwan Shima Zai Sha, Saboda Haka Sai Ya Zama Duk Ya Dagula Ruwan Laka Da Ta6o Duk Suka Canjawa Ruwan Kala/Launi.

     

    Wannan ‘Dan Aiken Yayi Tunanin Cewa:”Ta Yaya Zan Kaiwa Dattijon Nan Wannan Ruwa Mai Datti???”, Sai Ya Dawo Ba Tare Da Ya ‘Debo Ruwan Ba Yake Shaidawa Dattijon Nan Cewa; Ruwan Ne Wani Maraqi Shiga Ya Damashi Duk Datti Ya Taso Shi Yasa Bai ‘Debo Ba, Bayan Ya Jira Zuwa Wani ‘Dan Lokaci, Sai Dattijon Nan Ya ‘Kara Tura Wannan Mutumin Da Yaje Da Farko Akan Ya Koma Ya ‘Debo Masa Ruwan, Ya Koma Nanma Ya Ga Har Yanzu Dai Ruwan Akwai Dattin. Ya Dawo Ya Sanar Da Dattijon Nan Haka.

     

    A Karo Na Uku Ya ‘Kara Umartar Wannan Mutumin Da Yaje Ya ‘Debo Ruwan, Da Yaje Kuwa Sai Ya Tarar Da Dattin Ya Kwanta ‘Kasa, Ruwan Ya Zama Fari Tas Mai Hasken Gaske. Sai Ya Sanya ‘Kwaryarsa Ya ‘Debo Ruwan Ya Kawowa Dattijon Nan.

     

    Dattijon Nan Ya Kalli Ruwan Sannan Ya ‘Daga Kai Ya Kalli Mutumin Nan Da Ya Aika Ya Ce Masa:”To Kalli Abin Da Ka Yi(Hakuri) Har Ka Sanya Wannan Ruwan Ya Zama Mai Tsafta, Kai Yi Hakuri Har Ka Bari Ya Kwanta Sannan Ka ‘Debo. Don Haka, ZUCIYARKA(Ko Kuma In Ce Ranka/Ruhinka) Ma Haka Take, Lokacin Da Take Zama Cikin ‘Kunci Da Damuwa(Wani Ko Wani Abu Ya Dagula Maka Ita), To Ka Bata ‘Dan Lokaci Qalilan Zata Zama Mai Kyau Da Tsafta Ta Kuma Samu Nutsuwa.

    Ba Lalle Sai Ka Sanya Mata ‘Karfi Ba Ko Takurata Wajen Nutsar Da Ita. A’a Idan Ka Samu Kanka a Cikin Irin Wannan Yanayin Na ‘Bacin Rai Ko Fusata Ko Dai Wani Abu Makamancin Hakan; KA TUNA CEWA DA AMBATON ALLAH TA’ALA DUKKAN ZUKATA KE SAMUN NUTSUWA, SAI KA MAI DA LAMURANKA GA ALLAH TA’ALA TA HANYAR YAWAITA AMBATONSA DA KUMA NEMAN GAFARARSA.

     

    ALLAH Ta’ala Yasa Mu Zamto Cikin Zakirai a Ranar Da Dukiya Bata Amfani Balle ‘Yaya Ameeeeeeen.

     

    Othman Muhammad

  • KISSA: Wata Rana A Madina Umarul-Futy Ya Kai Ziyara Wajen Sheikh Muhammad Ghali A Madina.

    ƘISSA; SHEHU UMARUL-FUTY (R.A).

     

    1. Wata Rana a Birnin MADINA, SHEHU UMARUL FUTY (R.A) Ya Kai Ziyara Wajen Shehunsa Wato Babban Waliyin Nan SHEIKH MUHAMMADUL GHALI(R.A) Dake Zaune a MADINA,

     

    Da Ya Je Ƙofar Gidan Sai Ya Ɗaure Dokinsa a Waje Ya Shiga Gidan, Yayi Sallama Ya Shiga Ya Zauna Tare Da Shehunsa Suna Zantawa.

     

    Suna Zaune Suna Magana Sai Aka Yi Sallama a Ƙofar Gida, Da Jin Haka Sai Sheikh Muhammadul Ghali(R.A) Ya Fita Waje Ya Ga Waye Yake Sallama.

     

    Ashe Wani SHARIFI Ne(Jinin MANZON ALLAH (S.A.W) Bayan Sun Kammala Gaisawa Da Wannan Sharifin, Sharifin Zai Koma,

     

    Sai Muhammadul Ghali(R.A) Ya Rasa Wacce Hadiya Zai Bashi, Kawai Sai Ya Kunto Dokin Shehu Umarul-Futy(R.A) Ya Bashi a Matsayin Hadiya, Ya Tafi Da Shi, Ba Tare Da Ya Sanar Masa Ba.

     

    Sheikh Muhammadul Ghali(R.A) Ya Koma Gida Bayan Sun Kammala Zantawa Da Ɗalibinsa; Ya Tashi Zai Tafi, Sai Ya Rako Shi Zuwa Ƙofar Gida.

     

    Sai Shehu Umaru Futy(R.A) Ya Ga Dokinsa Baya Nan Ya Ce; “Ina Doki Na???”

     

    Sai Muhammadul Ghali(R.A) Ya Ce: Na Bawa Wani Sharifi Ne Dokinka Hadiya.

     

    Da Jin Haka Sai Shehu Umarul-Futy(R.A) Ya Ce;

     

    “ALHAMDU LILLAHI! INA MA ACE NI NE DOKIN DA AKA BAIWA WANNAN SHARIFI HADIYA, YA HAU BAYA NA”.

     

    Take Ya Nuna Farin Cikinsa Da Hakan, Ya Yiwa Shehunsa Godiya, Suka Yi Sallama Ya Koma Gida.

     

    To Fa Kun Ji Yanda Manyan Salihan Bayin ALLAH Suke Girmama Sharifai(Jinin ANNABI (S.A.W) Da Shehunansu.

     

    NOTE; Misalin Kwatankwacin Yanda Abin Yake Don Mu Gane Girman SADAUKARWAR Da Yayi; Kamar Yanzu Ne SHEHUNKA Yayi Kyauta Da Motarka Dalleliya Ba Tare Da Saninka Ba.

     

    ALLAH Ya Ƙara Mana Soyayyar Ahlul-Bayti(A.S) Da Waliyai Ya Bamu Ƙarfin Yi Musu Hidima, Ya Ba Mu Albarkar Masu Albarka Irinsu Mujahid Sheikh Umarul-Futy (R.A) Ameeen

  • Wani Dattijo Ne Jikokin Sa Suka Ce Sunan So Ya Basu Labarin Wanda Yafi Kowa Jarumta a Cikin Al’umma

    LABARIN WALIYYI ABJADU

     

     

    Wani dattijo ne jikokin sa suka ce suna so ya basu labarin wanda yafi kowa jarumta a cikin al’umma, kuma wanda jarumtar sa ta amfanar dashi da musulmi a duniya da lahira, shine ya basu labarin WALIYYI ABJADU.

     

    Tsohon yace, A wata qasa daga qasashen duniya mai suna DAURUL FALAK, an haifi wani kyakkyawan yaro a ranar da rana ta fito bayan hasken wata ya kau, cikin wata daga watannin arabiya wanda tayi daidai da shekara a shekarun miladiyya. Sunan mahaifin yaron KAUKAB, sunan mahaifiyar sa BURUJ.

     

    Wannan yaron tun tasowar sa har yakai shekaru 18, bashi da aiki sai wayannan abubuwan:

     

    1. Tsantsar tauhidi, kiyaye sallar Farilla sau biyar a jam’i da azumin watan ramadana.

     

    2. Karatun kur’ani daidai gwargwado da neman ilimi.

     

    3. Koyi da sunnonin Annabi SAW da kuma kokarin biyayya ga iyaye bisa umurni da hani.

     

    Mutanen garin suna qaunar sa sosai har suke masa laqabi da ABJADUL ISLAM. Bayan ya shekara 18 sai yayi mafarki da wani balarabe, yace masa sunana BADDU (بط) ina so ka shiga duniya domin neman yardar Allah ta hanyar koyi da bayin sa waliyai.

     

    Yana farkawa ya nemi iznin iyayen sa ya shiga duniya, sai yaje wata qasa a qasashen yamma, ya gamu da wani waliyyi ana kiran sa KHATMUT TIJJANI. Ya nemi iznin zama dashi sai yace masa “maraba da zuwa Abjadu, ai nasan da zuwan ka, toh ni dai bani komai sai abubuwa guda uku, amma duk wanda ya riqe su sai ya shiga aljanna ko baya so, sune”:

     

    1. Istigfari 100, Salatil Fatihi 100, Hailala 100 bayan sallar asuba da na la’asar.

     

    2. Istigfari 30, Salatil Fatih 50, hailala 100, jauhara 12 sau daya a rana kullum.

     

    3. La ilaha illallah ba adadi ranar juma’a bayan sallar la’asar gabanin faduwar ranar har magariba.

     

    Wannan saurayin yace zai iya, waliyin nan yace toh naji amma akwai sharadi, dole ka daina neman madadin wani waliyyi in ba ni ba, ba zaka hada wannan wuridin da wuridin wasu waliyai ba, ba zaka daina yin wannan wuridin ba har mutuwa, saurayi yace da himmar ka maulana an gama. Waliyin nan yace to daga yau sunan ka ABJADUL IMAN.

     

    Haka saurayin nan yayi ta kokarin kiyaye wuridin nan daidai gwargwado har ya shekara 40, a lokacin sai khatmut Tijjani yace masa yanzu ka kai muqamin da zan turaka wurin babban da na, in kaje zai maka aure bayan ka tsallake ayyukan da zai saka ka.

     

    Kwanci-tashi sai ABJADUL IMAN ya isa garin da khatmut Tijjani ya labarta masa amma sai an tsallake wani teku ake isa garin. A bakin tekun an rubuta SUNAN WANNAN TEKUN FAIDA, TAKA DA QAFARKA KA WUCE IN AN MAKA IZNIN ZUWA. Ai kuwa Abjadu sai ya fara taka ruwan nan bai nitse ba, amma yana zaton zai dade bai kai tsakiyar ruwan ba, sai yaga taku 7 ya kaishi garin dake tsakiyar ruwan, an rubuta BARKA DA ZUWA GONAR ARUFAI.

     

    Bayan ya shiga sai ya ga jama’a kowa ya shagala da kanshi, babu mai magana da wani, Yana isa fadar garin sai ya shiga ya miqa takarda, aka kaishi wurin Sarki wanda shine babban yaron khatmut Tijjani. Yayi masa maraba sannan yace masa, zan maka aure amma sai ka tabbatar min da cewa za ka iya riqe mata. Shiga ga daki can ka dinga karanta abinda ka gani a jikin bangon dakin har sai ka fahimci yadda ake noma ba tareda fartanya ko galma ba, da yadda ake mutuwa ba tareda an daina numfashi ba.

     

    Bayan dan lokaci, Abjadu ya zo gun sarki da amsoshi gamsassu, sarki yace lallai yanzu kam ka cancanci aure, zan aura maka mata biyu a lokaci daya, kuma sunan ka ya zama ABJADUL ISHAN daga yau. Saurayi yayi godiya, aka daura masa aure da mace biyu, ta farko sunan ta BARA’ATU, ta biyu sunan ta FANAITU.

     

    Alhamdulillah! Yara kunji labarin waliyyi Abjadu wanda yafi kowa jarumtaka da amfanuwa tareda amfanarwa. Iznin fita neman ilimin a farko Annabi yayi masa, na biyu Shehu Tijjani yayi masa, a qarshe kuma ya samu damanar Shehu Ibrahim akan FA ASGARU ATBA’IY BARI’UN MINASH-SHIRKI wato har abada ba zai yi shirka ba, kuma FA ASGARU ATBA’IY UNILU FANA’A wato ya samu qarewa cikin zatin Allah.

     

    Wannan labarin bushara ne ga dukkan batijjane, da iznin Annabi ka sadu da Shehu Tijjani, da iznin Shehu Tijjani ka sadu da shehu ibrahim, saduwa da Shehu ke tsallakar da mutum daga sharrin duniya amma in ka yi tarbiyatul azkar bayan zuciyar ta cika da sadiqar soyayya da hidima gareshi.

     

    Mu qara riqe abubuwan da muke kai, wallahi a yau mu Allah yake dubawa yake saukar da rahmar sa, fushin sa ga halittu kuma domin mu yake Afwa, mune nashi, mune masoyan shi, mune bayin sa na haqiqa.

     

    Allah kayi tsira da aminci ga Annabi Muhammad, ka ninka yardar ka ga katimul wulaya, ka cigaba da daukaka sunan sahibul faida.

     

    ✍ Sidi Sadauki.

Back to top button