MAULUD

  • Yanda Aka Fara Halartan Taron Mauludi Manzon Allah SAW A Khaulaq.

    MAULUD NABIY 2024

     

    Al’ummar musulmai na fadin duniya a wannan watan na Rabiul Awwal suke gudanar da gagarumin bukukuwan taron Mauludi Manzon Allah SAW don muna murna da watan da aka haife shi a kalandar Hijiriyya.

     

    Dubban mutane daga sassan fadin duniya suna halartan Maulud na Khaulaq dake kasar Senegal wanda Maulana Sheikh Ibrahim Inyass Al-Khaulaq RA ya sassan fadin wafatin sa.

     

    Wanna taro shine na 48 da fara shi wanda yake gudana a Madinatu Baye Khaolack Senegal.

     

    An shirya komai don fara gudanar da wannan taron Mauludi kamar yanda aka saba duk Shekara karkashin Jagorancin Khalifa Muhammadu Mahy Inyass

     

    Allah yasa ayi lafiya alhamdulillah.

  • Gamsashen Hujjar Yin Mauludi Daga Sayyadi Abul Fath Sani Attijjany.

    Tattaunawa ta musamman kan watan Maulidi tare da Sheikh Abul Fathi Sani Attijaniy.

     

     

    Alhamdulillah, Allah ya saka masa da alkhairi. Amiiiin Yaa ALLAH

  • Ga Watan RABIUL-AWWAL Ya Kama, Bama Tare Da Su(A Zahiri), Amma Muna Da Yaƙinin Kuna Mafi Amincin Wurin.

    GA WATANKU YA KAMA.

     

    Sayyadi Sunusi Sadi Umar

    Sayyadi Zakiru Yahya Lafia,

    Sayyadi Mahir Abdur Rahaman Nguru

     

    Daga Kamawar Wannan Watan RABIUL – AWWAL Waɗannan Taurarin Cikin Hidimar SHUGABA (S.A.W), Masoya MANZON ALLAH (S.A.W), Sune Suke Ta Yawo a Cikin Zuciyata.

     

    Ga Watan RABIUL-AWWAL Ya Kama, Bama Tare Da Su(A Zahiri), Amma Muna Da Yaƙinin Kuna Mafi Amintaccen Wuri, Kuna Tare Da MANZON ALLAH(S.A.W), Muna Da Yaƙinin Hakan.

     

    Muma ALLAH Ya Mana Ya Taku, Ya Kyautata Namu Ƙarshen.

     

    ALLAH Ya Ƙara Muku Kusanci, Ya Jaddada Rahma a Gare Ku, Don Alfarmar HABIBULLAHI (S.A.W). Amiin Yaa ALLAH

     

    Daga: Othman Muhammad

  • Duk Wanda Baya Maulidi To Ba Musulmi Bane, Inji Prof Ibrahim Maqary.

    Duk Wanda Baya Maulidi To Ba Musulmi Bane, Inji Prof Sheikh Ibrahim Ahmad Maqary.

     

    Babban limamin Masallachi Abuja Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary Hafizahullah ya bayyana cewa ka nuna farin ciki da sabuwar Manzon Allah SAW wajibi ne ga dukkan wani musulmi.

     

    Ya kara da cewa duk wanda baya son Annabi Muhammadu saw ba musulmai bale, soyayyan shine a bayyane ko a zuciya. Ka nuna jin daɗin zuwan ma’aiki Sallallahu Ta’ala Alaihi Wasallam a zuciyar kayi Maulidi kenan, Ba dole sai ka tara mutane ba. To kenan duk wanda baya son Mauludi ba Musulmi bane.

     

    Don haka duk wanda baya murnan zagayowar watan Maulud to ba musulmi bane.

     

    Allah ya karawa Maulana Sheikh Farfesa Maqary lafiya da kwanciyar hankali. Amiin

  • Babu gurin da nake jin dadin kasancewa kamar gurin Maulidin Manzo S.A.W ” ~ Sarkin Bichi

    Babu gurin da nake jin dadin kasancewa kamar gurin Maulidin Manzo S.A.W ” ~ Sarkin Bichi

     

    Mai Marataba Sarkin Bichi, Alh. Nasiru Ado Bayaro, ya ce babu wajen da yake jin dadin kasancewar sa a Duniya face wajen taron Maulidin Annabi S.A.W.

     

    Alh. Nasiru Ado Bayero, ya bayyana hakane a daren Asabar a wajen taron Maulidin da Mahmud Sa’eed Adahama, ya shirya a Unguwar G.R.A da ke Kano.

     

    Mai Martaban ya ce, ” ba karamin farin ciki yake ji ba, idan akace ya halarci taron maulidi “.

     

    Daga cikin wadanda suka halarci Maulidin, akwai Shugaban majalissar Shura ta jihar Kano, Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, inda ya ce rashin shugabanci na gari da bin doka da Oda da kyakkyawar mu’amula, wasu muhimman abubuwa ne da sai an gyara su za’a samu Al’umma ta gari.

     

    Taron Maulidin da aka gudanar cikin Sa’o’i dai, ya maida hankali ne kan kara bayyanawa Al’umma daraja da girman da Manzo S.A.W ke da shi a wajen ALLLAH madaukakin Sarki, kamar yadda masu jawabi su kayi.

     

    Daga Nazeer Bashir Tsamiya.

Back to top button