Muna ALLAH Wadai Da Cin Mutuncin Almajiranci A Tashar Arewa 24.

MUNA ALLAH WADAI DA MANA KISAR DA AKE MA ALMAJIRAI A WANNAN SHIRI “MANYAN MATA”

 

Bama musawa, lallai duba ga yanayin chanjawar zamani da bukatar samun gyare-gyare a harkar Almajiranci, amma irin wannan salo da tashar @Arewa 24 ke bi na kokarin cusa kyamar harkar Almajiranci a tunanin al’umma ta hanyar amfani da irin wadannan fina-finai da ake nuna Almajirai ne ke rikidewa su dawo bata gari dake addabar Al’umma, lallai wannan wani yakine shiryayye da aka tunkari Almajirai da shi, kuma babban manufar shine yaki da karatun Alkur’ani.

 

A mai-makon su shagala da shirya Fim wanda ciki za su ke jan hankalin Shugabanni akan su kula da harkar Almajiranci ta hanyar sanya hannu wajen tallafawa sha’anin, amma sai al’amarin na su ya zamo Almajirancin suke son yaka kai tsaye su kawar da shi.

 

Muna masu kiransu da yaren da zasu fahince mu, lallai da bukatar su dakatar da wannan mummunan kudurinsu na su na kwangilar Yahudawa, domin lallaine ba’a kawo gyara ta hanyar muzantawa da kuma cin fuskar wadanda ake so a gyarawa.

 

MUNA FATAN SAKON MU ZAIJE GARESU, KUMA ZASU DAUKI MATAKIN KAWO GYARA.

 

Daga: Muhammad Usman Gashua.

Share

Back to top button