MAULUD

  • Yadda Kanawa Suka Kawata Bikin Takutaha Na Shekara Ta 2023, Domin Nuna Kaunarsu Ga Annabi SAW.

    KANO GARIN MASOYA ANNABI, MADINAR NIJERIYA.

     

     

    Yadda Kanawa Suka Kawata Bikin Takutaha Na Bana Domin Nuna Kaunarsu Ga Annabi SAW.

     

     

    Duk da yanayin talauci da ake ciki da tsadar rayuwa hakan ba ta hana a’lummar Jihar Kano bikin murnar zagayowar haihuwar Mafificin Halitta Annabin tsira mai ceton mai kaunarshi.

     

    Sharif Sani na daga cikin wadanda suke kara kawata murnar wannan ranar, tun a sanyi safiya dai al’umma ke ta shigowa cikin birnin Kano domin nuna jin dadi da haduwa da abokan arziki masoyan Annabi SAW.

     

    Garin Kano an tashi da lullumi mai alamar hazo kuma babu rana bare zafinta a cikin wannan yanayin ake cigaba da gudanar da zagaye gurare gurare inda akansan akwai masoya manzon Allah ana ta girka abinci ana bayarwa sadaka.

     

     

     

     

    Hakika bana tafi bara kyawun tsari dakuma yawan alumma masu nuna jindadi hadi da yin hidima.

     

    Daga Abdulwahab Sa’id Ahmad.

     

  • Duk Wanda Ya Kushe Mauludi Bagidaje Ne Ba Malami Bale. Inji Sheikh Prof, Umar Sani Fagge.

    Shahararren malamin Addinin Musulunci kuma babban sufi mabiyin darikun sufaye Sheikh Prof, Umar Sani Fagge yana cewa;

     

    …Duk Wanda Kushe Mauludi Bagidaje Ne Ba Malami.

     

    Sheikh Umar Sani Fagge ya kara da bayyana cewa: ASALIN MAULUDI A QUR’ANI DA HADITH

     

    Shi Mauludi a wurin Masoya Manzon Allah SAW yana nufin Murna da farin ciki da samuwar Manzon Allah SAW a matsayin shi na Rahama ga duk halittun Allah ta hanyoyi da dama kamar yin taro a bada tarihin Manzon Allah SAW, ajiyar da masoyi dadi dajin Qasidun Manzon Allah SAW, aciyar da mutane dan Annabi SAW kuma a sada zumunci da yanuwa duk don Murna da Farinciki da Samuwar Rahamar Allah Annabi Muhammadu SAW.

     

    Allah (SWT) yayi mana Umarni dayin Farin ciki da Murna da Manzon Allah SAW kamar yadda Alqur’ani ya gaya mana a Suratul Yunus aya ta 58.

     

    قُل بِفَضلِ اللَّهِ وَبِرَحمَتِهِ فَبِذٰلِكَ فَليَفرَحوا هُوَ خَيرٌ مِمّا يَجمَعونَ

     

    Ka ce: “Da falalar Allah da rahamarSa, saboda wannan suyi farin ciki .” Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.

     

    Allah yafaɗa mana yin Farinciki da samun Falalar Allah da Rahamar sa. Yafi dukkan abunda muke tarawa. Kuma Rahamar Allah a wannan ayar shine Annabi Muhammadu SAW kamar yadda Alqur’ani da hadisai suka nuna mana.

     

    Imam Assayudi ya kawo a Tafseerinsa yace :

     

    واخرج ابو الشيخ عن ابن عمر رضي الله عنه في الأية قال :

    Abush Sheikh ya fitar daga Sahabin Manzon Allah SAW Abdullahi bn Abbas yace akan wannan ayar :

     

    فضل الله العلم ، ورحمته محمد صلى الله عليه وسلم. قال تعلى ؛

     

    Falalar Allah shine Ilimi,

    Rahamar Allah shine Manzon Allah SAW.

    Domin Allah madaukakin Sarki yana cewa :

     

    وما ارسلناك الا رحمة للعالمين

    Bamu aikoka ba Ya RasulalLaH face Rahama ga talikai.

     

    Sannan Hadisai sun tabbatar mana cewa Manzon Allah SAaw shine Rahamar Allah.

     

    1.Hakim ya ruwaici hadisi a Mistadrak hadisi na 100

     

    عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال : يا ايها الناس ، انما انا رحمة مهداة.

     

    Manzon Allah SAW yace : yaku mutane lallai ni Rahama ce kyauta da Allah ya baku. .

     

    Masha Allah; Allah ya kara mana kaunar Manzonsa (saw) Yabarmu soyayyan Annabi ﷺ. Amiiin Yaa ALLAH.

  • GWANIN BAN SHA’AWA: Yadda Kananan Yara Suka Gudanar Da Mauludin Manzon Allah a Zariya. 

    GWANIN BAN SHA’AWA: Yadda ƙananan yara suka gudanar da maulidin manzo a Zariya.

     

    Daga Barista Nuraddeen Isma’eel

     

    “Wani abun ban mamaki na wasu ƙananan yara wanda duk cikarsu haifaffun garin Zaria ne jihar Kaduna, inda suka sabunta maulidin Fiyayyan halitta Annabi Muhammadu (SAW).

     

    “Shi dai wannan maulidin na ƙananan yaran sun saba gudanarwa a duk shekara kamar yadda rahoton hakan ke riskan Alfijir Hausa.”

     

    Yadda al’amarin maulidin ke tafiya cikin tsari da ƙayatarwa a halin yanzu haka, ganin yadda yaran ke gayyatar yayasu-yayasu Sa’o’in juna daga unguwanni daban-daba domin halartar wannan gagarumin Mauludin.

     

    “Rahoton na cigaba da bayyanawa kamar haka harda gagarumin walima da yaran ke shiryawa bayan kammala maulidin Fiyayyan halitta Annabi Muhammadu ( SAW).

     

    “Wannan maulidin ya gudanane a ranar juma’a 11/11/2022 a bakin kasuwanci Zariya cikin wani unguwa da ake kira a unguwar ƙarfe Gidan Hajiya ladi mai waina.”

     

    Allah ya saka masu da mafificin alkhairi, ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW. Amiiiin

  • An Sanya Maulidi Cikin Kundin Tsarin Tarukan Da Za’a Rinƙa Gabatarwa Duk Shekara A Saudi Arabia .

    Hukumomin Kasar Saudi Arabiya Sun Sanya Bikin Maulidi Cikin Jadawalin Taruka A Fadin Kasa.

     

    A wannan shekara 1444 AH ne hukumomin kasar Saudi Arabiya suka shirya taro na musamman a watan Rabi’ul Awwal (Mauludi) da sunan Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW wanda suka gayyaci malamai sama da ɗari da hamsin 150 waɗanda aka gayyato daga ƙasashe hamsin a faɗin duniya kuma ya ɗauki ƙwanaki ana gabatarwa kuma sukayi ma taron Maulidin da laƙabi da taken:

     

     

     

    “ƊA’A TARE DA DARAJOJI A CIKIN RAYUWAR MANZON ALLAH MAI TSIRA DA AMINCI DA KUMA TASIRINSU GA DUNIYA GABA ƊAYA”

     

    “القيم الاخلاقية في السيرة النبوية واثرها في قيم السلام العالم”

     

    Cikin wadanda suka gabatar da jawabai akwai Maulana Prof. Ibrahim Maqary, shima yana ɗaya daga cikin malaman da aka gayyata kuma ɗaya daga cikin ginshi ƙai a gurin gabatar da taron wanda ya ƙunshi bijiman malamai masu jawabi a yayin gudanar da taron Mauludin.

     

     

     

    Tabbas hukumomin Saudi Arabiya sun taka muhimmiyar rawa tare da namijin ƙoƙari gurin yin watsi da halatta ko rashin halattar yin murnar maulidin fiyayyen halitta saw tare da sanya shi a cikin kundin tsarin tarukan da za’a rinƙa gabatarwa duk shekara a kuma cikin watan da aka haifi fiyayyan halitta Annabi SAW.

     

    Muna murna ne kawai saboda an girmama fiyayyan halitta Annabi Muhammadu SAW a gurin daya kamata ace nan ne tushen daya kamata su ƙarfafa sha’aninsa, AlhamdulilLah sannu dai a hankali abu nata samun tagomashi fiya da tunanin mu kuma dama munsan a hankali za azo gurin, In shaa Allah.

     

    Allah ya ƙara mana ƙaunar Manzon Allah SAW tare da ahalin gidansa da masu biye musu da ƙyautatawa har ya zuwa ranar sakamako, yasa muna cikin cetonsa. Amiin

     

     

     

    Daga Imam Anas

  • Duk Cikin Idin Sallar Babu Kamar Idin Samun Manzon Allah (SAW) Inji Sheikh Dahiru Bauchi RA

    Duk Cikin Idin Sallar Babu Kamar Idin Samun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

     

    Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi RTA yace; Shehu Ibrahim Kaulaha RTA yana cewa:

     

    Duk wani Murna/idi yana zuwa ne bayan wani alkairi da aka samu Azumin watan Ramadan da muke murna ne da samun Alkur’ani, Idin Sallahr Azumi murna ne da kammala azumin lafiya, Idin Babbar Sallah (Layya) murnane na (Yan’uwan mu sun hau hajji sun sauka lafiya), Sallar Juma’a Idin sati kenan Murna ne na Allah ya bamu daman yin Sallar harna tsawon sati.

     

    Shehu Ibrahim RTA: yace ni kuma agu na babu wani Alkhairin da yakai Samun Annabi Muhammadu SAW a duniya, saboda haka Maulidin/Murna da samunsa yafi kowanne idi.

     

    Shehu yakara da cewa: Haka kuma Shehu Ibrahim RTA yake girmama Maulidin Annabi SAW ya daukeshi babu abinda ya kaishi a cikin Iduka, harma duniya tazo tai ta koyi da irin shirin Maulidin sa da ya keyi. Ko anan Nigeria da ba’asan Maulidi ba ana kiransa, A Kano Takutaha, Wani wuri Babbar Sallah, wani wuri kuma Sallahn Kaji da sauran su, to idan Muqaddamai sun je Kaulaha sun ga yadda Shehu Ibrahim keyin Maulidi in sun dawo Nigeria sai suke koyi dashi, haka nan in kowa ya gani sai yayi tambaya wai shin wannan kam meye ne ??

     

    Ace musu ai Maulidi kenan murnane da haihuwar Annabi SAW. Saisuce ah muma zamuyi, muma zamuyi inde abu na Son Annabi ne SAW baza abarmuba.

     

    Haka nan yanzu in watan ta kama to babu yaro ba babba kowa yana nuna farin cikin sa da zuwan Annabi Muhammadu SAW duk albarkar samun Shehu Ibrahim RTA, Masha’ Allah

     

    Allah ya sakawa Shehu Ibrahim Niasse RTA da Alhairi, Allah karawa Shehu lafiya Albarkar Manzon Allah SAW, Allah Kara mana soyayya A’min A’min

Back to top button