RASUWA

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un: Allah Ya Karbi Rayuwar Mahaifiyar Sheikh Sarham Sa’id MON Rasuwa.

    Inna lillahi wa Inna Ilaihir Rajiun!!!

     

    Allah SWT ya jikan Hajiya Aminah Ibrahim Maifata (Inna).

     

    Hajiya Aminah Ibrahim Inna matace ga babban malamin nan marigayi Sheikh Sarham Sa’id MON kuma Mahaifiyace ga Major General Jamil Sarham Rtd da Barrister Munir Sarham da Haj Maryam Sarham da Haj Khadija Sarham.

     

    Hakika Inna uwace gareni. Ta rikeni tsawon lokaci cikin aminci da girmamawa. A rayuwar ta.

     

    Allah SWT ya gafarta mata ya bata Jannatul Firdaus. Amiin Yaa ALLAH

     

    Daga: Imam Ghazali Umar

  • Allah Ya Yiwa Jikar Sheikh Dahiru Bauchi RA Rasuwa Sayyada Aishatu Yar Sayyadi Alhaji Ibrahim

    Hatsarin Mota Ya Rutsa Da Jikar Sheikh Dahiru Bauchi RA A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja.

     

    …..Allah ya yiwa jikan Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sayyada Aishatu yar Sayyadi Ibrahim.

     

    Allah ya karbi rayuwar daya daga cikin jikokin Maulanmu Sheikh Dahiru Bauchi RA ya ga Sayyadi Alhaji Ibrahim (Khadimul Faidah) sayyada Aishatu rasuwa sakamakon hatsarin mota daya rutsa dasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja yau asabar 18/02/2023.

     

    Muna mika sakon ta’aziyya ga Sheikh Dahiru Bauchi RA, da Khadimul Faidah Sayyadi Alhaji Ibrahim da sauran yan’uwa Musulmai masoya,

     

    Allah ya jikan ta da rahma ya gafarta mata, Allah ya karbi shahadar ta. Amiin Yaa ALLAH

     

    Daga: Babangida A Maina

    1. Tijjaniyya Media News
  • Shekara 48 Da Wafatin Sheikh Muhammadu Ngibirima Nguru RA A Dake Nguru Jihar Yobe.

    Yau Shekaru Arba’in Da Takwas (48) Da Watafin Sheikh Muhammadu Ngibirima Nguru

     

    A irin wannan rana ta 19/02/1975, Allah ya karbi rayuwar sanannen malamin Musulunci wanda ya bawa duniyar darika kariya Sheikh Muhammadu Ngibirima Nguru dake garin Guru dake jihar Yobe.

     

    Sheikh Muhammadu Ngibirima Zulma Arif shahararren malamin Musulunci ne, kuma jigo a darikar Tijjaniyya wanda ya bada gagarumar gudumawa wurin daukaka Addinin Musulunci tare da zamantakewa a yankin Africa.

     

    Shekaru Arba’in da takwas (48) kenan da rasuwan shehin malamin a lissafin miladiya. Ta 19/02/1975

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa, muna sddu’an Allah ya karbi bakwancin sa. Amiiiin Yaa Allah

     

    Babangida A. Maina

    Tijjaniyya Media News

  • An Kas@he Mana Matafiya Masu Zuwa Ziyara Khaulaq A Kasar Burkina Faso.

    WASU DAGA CIKIN FUSKOKIN TIJJANAWA DA SOJOJIN KASAR BURKINA FASO SUKA TASHE.

     

    ……Hakikanin Abunda Ya Faru Da Yan’uwa Mu Tijjanawa Matafiyan Zuwa Ziyara Khaulaq.

     

    A ranar laraba ne 1/01/2023, aka samu sanarwan mutawan yan uwan mu Tijjanawa matafiya zuwa ziyaran Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq dake kasar Senegal.

     

    A cikin tawagar wasu daga cikin matafiya sun hadu da shahada inda sojojin kasar Burkina Faso suka fito dasu daga mota suna zargin yan ta’adda ne suka Bude masu wuta har lahira.

     

    Yanda abun ya kasance shine; akwai ganganci tun farko na bin hanyar Kancare, domin hanya ce wanda tun kusan shekaru biyar aka dai na binta saboda matsalar rashin kyan hanyar da kuma yanda ƴan ta’adda su ka mai da ita wajen kafa sansanin su.

     

    Kamar yanda mu ka samu bayani daga ɗaya, daga cikin matafiyan ya shaida mana cewa tun a kan iyaka ta tsakanin ƙasar Burkina faso, da Nijar, sojojin kan iyaka su ka shaida musu cewa akwai ma’aikata yan uwansu sojoji da su ke tahowa daga wani waje kuma sojoji ne masu haɗarin gaske.

     

    Amman lamarin Ubangiji bai saka sun tsaya ba, suka ɗora da tafiya. Ya shaida mana cewa suna cikin tafiya suka haɗu da wata gagarumar rundunar sojoji wanda ya kimta yawan su sun kai kusan mutum ɗari biyar. Yace suna haduwa da su suka tare ɗaukacin motacin su kuma babu tsayawa a nan take suka hau bincike, suna sauke waɗanda suke da siffar kabilar Fulani, da kuma wanda suka ya tara gashi mai yawa, a kansu suna fito da su suna harbe su, ya cigaba da cewa a iya mota ɗaya sun harbe mutane kusan guda takwas a wata mutum biyu jimilar lissafi shi ne an harbe mutane goma sha tara.

     

    Muna kira na musamman zuwa ga Mista Marc Bassey Egbe, jakadan ƙasar Najeriya, a ƙasar Burkina Faso, da ka gaggauta sanar da hukumar ƙasar abin da ya faru a kan kisan gillar da sojojin ƙasar suka yi wa ƴan asalin ƙasar Najeriya.

     

    Sannan kuma muna kira da babbar murya zuwa ga ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje da lallai su binciki wannan al’amari mai cike da rashin imani da rashin tausayi da waɗannan sojoji suka aikata a kan waɗannan ƴan uwa namu. Idan sun kammala bincike da su nemi a hukunta waɗanda suka aikata abin kuma a biya Iyalan waɗanda suka rasu Diya…

     

    A ƙarshe muna roƙon Allah ya karbi shahadar su albarkar shugaba Sallallahu alaihi Wa sallama. Amiin

     

    Daga: Mujaheed M Muhammad

  • Wasu Sojojin Najeriya Sunyi Sanadiyar Mutuwan Dan Agaji Fityanul Islam Of Nigeria Dake Jihar Kaduna.

    INNALILLAHI WA’INNA’ILAIHI RAJI’UN.

     

    ….Allah ya yiwa Dan Agaji Fityanul Islam Ibrahim Admin rasuwa dake Jihar Kaduna.

     

    Bayan Lokacin Da Ake Gudanar da Bikin Yayanshi da Kanwarsa Wani Soja Yazo Wucewa Kuma ta Inda Ake Taron Biki, Al-hali Kuma Babu Hanyar Dashi Sojan Zai wuce Mai makon Yadanyi Hakuri Abude masa Hanyar Sai Ya nuna Bachin Rai. Bayan Ya samu Hanya Yawuce, Bayan Wani dan Lokaci Sai Sojoji Suka zo Suka Kama Bin Mutanen da Wannan Biki Yashafa Suka Raunata Wasu.

     

    Bayan Haka Sai Suka Bibiyi Ibrahim (Admin) Wato Dan Uwan Ango, Har gida Suka Masa Dukan Kawo Wuka Kamar Yadda Kuka.

     

    Ibrahim Admin Dan Agajin FITYANUL ISLAM Ne Reshen Jihar Kaduna Karamar Hukumar Rafin Guza Ibrahim Admin Babu Wani Laifi Da Ya’aikatawa Wanda ya Cancanci abunda aka aikatamasa

     

    Wanda Suka Samu Rauni Da Wanda suka rasa ransu acikin wanna aika aika, “Ubangijin Allah” Kabi musu kadi Idan Gomnatin Kasa nan Bata Bi musu Kadi ba Akan Wannan Zalinci, Ameen Ya Allah.

     

    Bayan Haka Muna Kira Ga Gomnatin Kasannan Da Tabi Kadin Wannan Zalinci da Aka aikatawa Ibrahim (Admin) Wanda yake karamar Hukumar Rafin Guza.

     

    “Ubangijin Allah Ya jikan (Ibrahim Admin) da Rahama, “Ubangijin Allah” Ya tona Asirin Wanda Suka aikata Wannan Mummunan Aikin Da Allah Bayaso, “Ubangijin Allah” Yasa Aljanna ce Makomarsa, Allah Yasa Mu cika Da kyau Da Imani Alfarmar Sayyidil Wujudi Annabi Muhammadu (Saw). Amiin

Back to top button