DANGALE WANDO BA SUNNAH BANE RA’AYINEE!!! INJI IMAM JUNAID BAUCHI

Dangale Wando Ba Sunnar Manzon Allah SAW Bale, Ra’ayine. …Inji Imam Junaid Bauchi.

 

Matashin malamin addinin Musulunci a Nigeria Sheikh Imam Junaid Abubukar Bauchi kuma (Limamin Masallacin Al’irfan) ya bayyana cewa dangale wando ba Sunnah Manzon Allah SAW bale ra’ayine.

 

Imam Junaid Bauchi ya bayyana hakan ne a karatun da yake gabatar wa na littafin Shama’ilul Muhammadiyya duk sati a masallacin Al’irfan dake birnin Bauchi. Ya kawo hadisan Annabi Muhammadu SAW tare da bayyana cewa Manzon Allah SAW bai saka wando ba, kuma a lokacin rayuwar sa akwai masu saka wando.

 

 

Allah ya tabbatar mana da gaskiya ya bamu ikon binta ya amfanar damu abunda muka karanta na gaskiya. Amiiiin Yaa ALLAH.

 

Babangida Alhaji Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button