RASUWA

  • Innalillahi Wa’inna Ilahir Raji’un: Allah Ya Yiwa Mahaifin Hafiz Abdallah Rasuwa Alh Abdallah Mai Hula

    Innalillahi Wa’inna Ilahir Raji’un.

     

    Allah Ya Yiwa Mahaifin Hafiz Abdallah Rasuwa.

     

    Cikin Jimami Muke Sanar Da Rasuwan Shehin Malamin Addinin Islama Kuma Shehin Darikar Tijjaniyya Sheikh Alhaji Abdullahi Maihula Mahaifi Ga Shahararren Mawakin Yabon Manzon Allah SAW Malam Hafiz Abdallah (Shugaban Cibiyar Ambato).

     

    Za’ayi Jana’izan Alhaji Abdallah Kamar Haka:

     

    – Rana: Juma’a 23/12/2022.

    – Lokaci: 2:00pm (Bayan Sallar Juma’a).

    – Wuri: Masallacin Juma’a Dake Sharada Kano.

     

    Allah Ya Jikan Sa Da Rahma Ya Gafarta Masa, Allah Ya Karbi Bakwanci Sa Albarkacin Manzon Allah SAW. Amiiiin

     

    Babangida Alhaji Maina

    Tijjaniyya Media News

  • Babban Malamin Hadisi Na Duniya Sheikh Abdurrahman Alkattany Ya Rasu

    Innalillahi Wa’inna Ilahir Raji’un

     

    ….Babban Malamin Hadisi Na Duniya Sheikh Abdurrahman Alkattany Ya Rasu.

     

    Sheikh Abdurrahman Alkattany babban malamin addinin Musulunci na duniya kuma babban masanin Hadisi wanda aka masa shaidar sanin Ilmin Hadisi a duniya. Kuma Sheikh Alkattany ya tattara dukkanin Uluumu na addinin Musulunci. Shehin malamin mabiya Darikar Idrisiyya ne, kuma sharifi jikan Manzon Allah SAW.

     

    Allah ya karbi rayuwar sa farkon watan December anyi sallar jana’izan kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa, ya Allah ya sadashi da Manzon Rahma SAW. Amiiiin

     

    Babangida A. Maina

    Tijjaniyya Media News

  • INNALILLAHI; Yau Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano Ya Cika Cika Shekaru Tara Da Rasuwa.

    Duniyar Musulunci Ba Zata Manta Da Rayuwar Sheikh Aliyu Harazumi Kano Ba.

     

    Al’ummar Musulmi na duniya musamman mabiya darikar Tijjaniyya na duniya na jimamin ranar zagayowar wafatin daya daga cikin manyan malaman Musulunci kuma jigo a darikar Tijjaniyya dake yammacin Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano wanda yayi wafati ranar 11/12/2013 wanda yayi dai-dai da watan safar.

     

    Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano shahararren malamin musulunci ne wanda ya bada gagarumar gudumawa wurin yada musulunci da darika a najeriya da makwabta.

     

    Marigayi ya ilmantar wanda baya tashi don bukatan sa kullum bata ilmi yake yi koda yaushe. Sheikh Aliyu Harazumi bawan Allah ne, sufi, masanin Allah, mai tawali’u.

     

    Ya karantar da dubban mutane karatun Addini da koyar dasu darikar Tijjaniyya, ya kuma bada gagarumar gudumawa eurin cigaban Musulunci A arewacin Najeriya dama yammacin Africa.

     

    Ra rasu yabar mata da yara maza da mata da kuma dubban almajirai da masoya, Sheikh Tijjani shine Khalifa bayan wafatin sa.

     

    Allah Ya Jaddada Masu Rahma Ya Gafarta Masa Allah Ya Kara Masa Kusanci Da Fiyayye Halitta Annabi Muhammadu ﷺ. Amiin

     

    Daga: Babangida A. Maina

    Founder/CEO Tijjaniyya Media News

  • Sheikh Dr, Hadi Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru Goma Sha Bakwai Da Rasuwa.

    Sheikh Dr, Hadi Sheikh Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru Goma Sha Bakwai Da Rasuwa.

     

    A rana mai kama ta yau 5/12/2022 Allah ya karbi rayuwar Sheikh Dr, Hadi Sheikh Dahiru Bauchi wanda yana daga cikin manyan Ya’yan Sheikh Dahiru Bauchi.

     

    Sheikh Dr, Hadi Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da yayi wanda Allah ya karbi rayuwar sa. Muna kara addu’an Allah jikan sa da rahma ya gafarta masa.

     

    Allah ya karawa maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi hakurin jure wannan rashi. Amiin

     

    Mustapha Abubakar Kwaro

    Tijjaniyya Media News

  • Allah Ya Karbi Rayuwar Daya Daga Cikin Matasan Tijjaniyya Ya DANLADI NDAYEBO Dake Birnin Minna

    INNA LILLAHI.. 😭😭😭

     

    .. Daya Daga Cikin Matasan Tijjaniyya Ya Rasu

     

    ALLAH Ya Jikan SYD DANLADI NDAYEBO, Ya Sa MANZON ALLAH (S.A.W) Ya Kar6i Ba’kuncinsa, Ya Rasu Yau Sakamakon Hatsarin Mota.

     

    Marigayi DANLADI NDAYEBO (‘Dan Jarida Ne, Kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Niger), Mutumin Kirki Ne Matuqa, Kuma Masoyin MAULANMU SHEHU TAHIRU(R.A),

     

    Domin a Ranar ALHAMIS ‘Din Nan Ma Da Ta Gabata ‘Kaninsa; Ibrahim Muhammad Ndayebo Ya ‘Kira Ni Yake Shaida Min Yayansu(Danladi Ndayebo) Yana So Ya Shigo Bauchi Ziyara Wajen SHEHU(R.A), In Nema Musu Wanda Zai Yi Musu Iso Zuwa Wajen SHEHU(R.A) Don Gabatar Da Wannan Ziyara.

     

    Nan Take Na ‘Kira Babban Hadimin SHEHU(R.A) a ‘Bangaren Social Media Wato Syd Abubakar Ibrahim, Na Masa Bayani, Na Nemi Izinin In Basu Lambarsa Don Su Tuntu6e Shi, Ya Amince Da Hakan, Na Tura Musu, Suka Ce Sai Sun Zo, Allahu Akbar.

     

    Kwatsam! Sai Yanzu Nake Ganin Labarin Rasuwar SYD DANLADI NDAYEBO, Allahu Akbar

     

    ALLAH Ya Kyautata Namu ‘Karshen, Ya Jaddada Rahma Ga SYD DANLADI NDAYEBO, Ameeen

     

    Daga: Othman Muhammad

Back to top button