Takaitaccen Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Takwas (8).

CIKAMAKIN WALIYAI (8)

 

KOMARWA SA AINI MADHI DAGA FAS

 

A cikin mu’amalar sa da waliyai, ya haɗu da babban waliyyin Malamatiyya, Sidi Ahmad (RTA) wanda ya ba Shehu Tijjani Ismul A’azam yace masa ya kamata ya shiga halwa har sai ya samu Fat-hul Akbar domin yana da babban muƙami nan gaba, Shehu Tijjani bai amince da haka ba sai shehin yace bakomai, muddin dai zai cigaba da karanta Ismul A’azam din da ya bashi, burin sa zai cika.

 

Shehu Tijjani ya samu mukamai daga Halarar Ubangiji sosai saboda kokarin sa wurin riko da hanyoyin sufayen nan, kuma kullum ƙishirwan sa bai gushe ba saboda har yanzu bai riski burin shi ba.

 

Shehu Tijjani ya hadu da wani waliyyi kashifi a Fas wanda ya bashi karfin gwiwar komawa gida (Aini Madhi) domin yana cewa “burin ka zai cika ne a yankin sahara”. Shehu Tijjani ya karɓi shawarar sa ya kama hanyar tafiya, a hanya ya tsaya a zawiyoyi daban-daban domin ziyartar waliyai har ya isa Aini Madhi.

 

Daga Aini Madhi sai ya tafi “Albayad”, Tafiyar kilomita 100 da wani abu daga Aini Madhi, Ana yiwa garin lakabi da “Sidi Shekh” saboda a garin aka binne babban waliyyin nan jikan Sayyidina Abubakar Siddiƙ mai suna Abdulƙadir ɗan Muhammad (Allah ya kara musu yarda).

 

A nan Shehu Tijjani ya zauna Shekara biyar yana koyarwa kuma yana ayyukan sa na sufanci sannan yana zuwa Aini Madhi lokaci-lokaci.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button