DA DUMI DUMIN SA: Yau An Gabatar Da Mauludi Cikin Hudubar Juma’a A Makka
TAKAITACCEN BAYANI, CIKIN KHUDBAR DA AKA TABA GABATARWA A MASALLACIN MANZON ALLAH (S.A.W) DAKE DA ALAKA DA TA YAU.
An gabatar da wannan Khudbah ranar 23 Muharram 1442.
1. Mutum zai kasance tare da wanda yake so. Son Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) sharadi ne ga imani. Mafi girman hanyar son Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ita ce koyi da rayuwarsa, da darajojinsa, da halayensa.
2. An zabe shi daga mafi girman mutane. Yana da tsatso da salsala mai cike da daraja da ɗaukaka. Kakanninsa sun cika da nagarta da daukaka. Mafificinsu shi ne Muhammad bn Abdullahi bn Abdul Muddalib, Qurashi, Hashimi Arab. Mahaifiyarsa ita ce Aminah bint Wahb Al-Qurashiyyah. Allah Ya zaba masa wuri mafi kyau. An haife shi a Makkah, Ummu Alqura, kuma a can ne ALLAH yayi masa wahayi.
3. Lokacin da ya cika shekara arba’in, sai Allah ya sanya shi ya zamo Annabi. Ya aiko masa da wahayi, ya sanya shi karshen Annabawa da Manzanni. Ya fara saqonsa da kiran mutane zuwa ga bauta wa Allah Shi kaɗai, daga barin shirka, da kwaɗaitar dasu kyawawan halaye, da umarni da kyakkyawa, da hani da mummuna da zalunci da fasadi. Ya yi haka ne a Makka tsawon shekara goma sha uku, yana kiran mutanensa dare da rana, a boye da bayyane.
4. Allah ya umarci Annabinsa yin hijira zuwa mafi tsarkin kasa, wato Madina Zama cikinsa yana da kyau. Shi ne birnin imani, kuma zuwa gare shi, muminai sukai gaggãwa. A cikinta akwai sojojin Allah, Ansar.
5. A cikin shekaru goma na Madina Allah ya kammala addininsa. Jama’a sun karbi addinin Allah da manyan igiyoyin riko. Musulunci ya yadu a cikin kasashen Larabawa kamar yadda mutanensa suka mika wuya [ga Allah], suna karbar Musulunci.
6. A watan Rabi Al-Awwal, a shekara ta goma sha daya bayan hijira, bayan hajjin bankwana ta riski Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da radadin ciwo, nayi fansar mahaifana da shi.! Allah ya ba shi zabi, kuma ya zabi haduwa da Ubangijinsa, ya ce: “Ya Allah Al’ummata, Ya Allah Al’ummata, Ya Allah Al’ummata. Lokacin tafiya ya gabato. Don haka ya yi nasiha (Sahabbansa) da bankwana. Duniya ta yi duhu a tafiyarsa, Musulmi suka wargaje..!
A KARSHE DAI DUK WANDA YA GUJI MAULUDI A GIDA NIGERIA, TO ZAI RISKESHI A MADINAR MANZON ALLAH (S.A.W).
Muhammad Usman Gashua